KUNGIYAR JAMA’ATU IZALATIL BIDI’AH WA IQAMATIS SUNNAH TA KASA TAYI KIRA GA YAN MAJALISUN TARAYYA DA SUYI BINCIKE KAN KISAN DA AKAYI NA YAN UWA MUSULMI A APO DAKE BIRNIN ABUJA.

A ranar litinin 23/09/2013 Shugaban Kungiyar ta Kasa Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau yaje Asibitin Asokoro dake Birnin tarayya Abuja dan ziyartan wadanda aka harba a yankin Apo dake Abuja, bayan dubiya da ya musu yayi addu’an Allah ya basu lafiya, wadanda suka rasu kuwa Allah ya jikansu da rahama, Har ila yau Shugaban yayi kira ga ‘yan Majalisun tarayya da suyi bincike da gaggawa dan gano hakikanin abin da ya faru, yayi juyayi kwarai da gaske ya kuma tausayawa wadanda abin ya faru dasu, ya kuma bada gudun mawa na kudi dan tallafa wa majinyatan, ya karkare da addu’an Allah ya kawo mana karshen wannan tashin tashina da muke fama da shi a wannan kasa tamu mai albarka.

In baku Manta ba An samu bayanai masu karo da juna dangane da gaskiyar abin da ya faru a wani gida da ke unguwar Apo a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja inda aka yi harbe-harbe da tsakar daren juma’a.

Hukumar ‘yansandan ciki wato SSS ta kasar dai ta ce sojoji sun yi musayar wuta da mayakan kungiyar Boko Haram ne lokacin da suka kai sumame a gidan garin neman makamai; abin da yayi sanadiyar raunata wasu.

Sai dai mazauna gidan sun ce babu wanda ke da makami a cikinsu illa jami’an tsaron ne suka bude musu wuta suna barci har suka kashe mutane akalla takwas.

” Mun kwanta duk muna barci da yake an yi ruwa; sai kawai muka ji karar harbi. Mutane ne a gidan sun haura mutum dari, amma sai kowa ya shiga neman wurin buya” Inji Muhammadu Ulama’u wani wanda ya tsira da ransa daga harin.

Cikin tawagar Shugaban sun hada da Manyan Malaman Kungiyar irin Sheikh Dr. Alhassan Sa’eed Adam Jos, , Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, Engineer Mustapha Imam Sitti, (Nat. Director FAG of Jibwis) Malam Jamilu Albani Samaru (Nat. Cor’ordinator Of Youth, Jibwis Nigeria) da Malam Abdussalam Abubakar Baban Gwale, Da Wasu Daga Cikin , Shuwagabanni, Malamai da ‘yan agaji na Kasa dana Birnin Tarayya Abuja.

Muna Addu’an Allah ya jikan Wadanda Suka Rasu, ya kuma baiwa wadanda basu da lafiya lafiya, mu kuma Allah ya tsare mu yasa mu cika da Imani. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *