JIBWIS ta kammala wa’azin bana a Makkah

Kungiyar wa’azin Musulunci ta JIBWIS yau asabar ta kammala wa’azin da take gabatarwa na wannan Shekara 1440/2019 a Unguwanin Hausawa dake Birnin Makkah ta kasar Saudiyya.

Shugaban Kwamitin Ayyuka na JIBWIS Nigeria Shekh Abubakar Giro Argungu shine Wanda ya jagoranci rufe Wa’azi a Masallacin Hara Gobirawa dake Birnin Makkah, Bayan takaitaccen wa,azin da ya gabatar tare da Alaramma Mustapha Bindawi Daga kasar Nijar.

Sheikh Giro ya gabatar da wa’azin ne akan Muhimmancin yin Nasiha ko wa’azi a tsakanin Al’umma da gaskiya da rikon Amana, Sannan da illar yin shirla, Daga Bisani ya yabawa shugaban Kungiyar JIBWIS Shekh Dr. Abdullahi Bala Lau akan kyakkyawan jagoranci ga Kungiyar, da kuma rungumar wannan aiki na wa’azi a birnin makkah shekara da shekaru.

Shima kakakin kungiyar a mumbarin wa’azi na JIBWIS Nigeria Shekh Abdulbasir Isa Unguwar Maikawo, yace an gudanar da wa’azozi har sau 10 Daga lokacin da aka fara wa’azin a Bana har zuwa yau DA aka kammala. Ya rufe da addu’ar Allah ya saka ladan wannan aiki a mizani.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY