LABARAI A TAKAICE

Hukumar Alhazan Naijeriya ta dawo da Mahajjata adadin dubu 20,181 Cikin sawun jirage 42 Zuwa gida Naijeriya bayan kammala aikin Hajjin Bana

Kungiyar wa’azin Musulunci, mai fatattakar bidi’a tsaida Sunnah (JIBWIS) ta kammala wa’azin da take gudanarwa na wannan Shekara 1440/2019 a Unguwanin Hausawa dake Birnin Makkah ta kasar Saudiyya.

An rufe wa’azin ne karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Ayyuka na JIBWIS Shekh Abubakar Giro Argungu, An rufe Wa’azin a Masallacin Hara Gobirawa dake Birnin Makkah, Bayan takaitaccen wa’azi da ya gabatar tare da Alaramma Mustapha Bindawi Daga kasar Nijar.

Rundunar ‘yan sanda a Lagos ta sake ‘yan ci rani daga yankin arewa su 123 da tun farko ta kama bayan samun bayanin cewa su ka iya zama miyagun iri ne. Mutanen da yawanci daga jihar Jigawa su ka fito, na tare da baburan su na achaba 48.

Rundunar ta ce ta samu labarin shigowar su ne ta hanyar yiwa babbar motar da ta ke dauke da su belbela kuma wai sun haura 300. Bayanin ya nuna tamkar mutanen sun kai wa Lagos hari ne ko ma ‘yan ta’adda ne daga yadda su ka shiga Lagos a cunkushe.

Da a ka gudanar da bincike ba a samu wani abun laifi tare da mutanen ba, in ka debe baburan su da za su yi aikin achaba da su. Kazalika yawancin su ma sun tafi hutun babbar sallah ne don haka sun dawo Lagos din ne don cigaba da gudanar da sana’ar su.

Bayan hasashen yiwuwar rasa tikiti, yanzu dai gwamnan Kogi Yahaya Bello ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar karkashin inuwar APC. ‘Yan takara da dama su ka shiga zaben da ya gudana karkashin jagorancin gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru.

Baya ga samun sabani da mataimakin sa, gwamna Yahaya Bello ya samu suka da cewa bai tabuka abun kirki ba a wa’adin mulkin sa na farko. Duk da haka akwai wadanda su ka yi zargin ba a gudanar da zaben ta hanyar da ta dace ba.

Za a gudanar da zaben gwamnan Kogi ranar 16 ga watan Nuwamba. Kwamishinan zabe a hukumar zaben Najeriya Muhammad Haruna ya ce hukumar ta tura sakamakon zabe na na’ura mai kwakwalwa amma gwaji ne kawai ta yi.

Haruna ya ce tukun lamarin bai zama doka ba don haka gwada aiki da wannan hanyar a ka yi don yiwuwar fara aiki da ita a nan gaba. Da dai shugaba Buhari ya sa hannu kan sabuwar dokar zabe da matakin ya zama doka.

Duk da aiyana tsagaita bude wuta a yankin Idlib da ya sanya mutane boris da mota, hakan bai hana Amurka kai hari da makami mai linzami yankin ba da hakan ya haddasa muuwar akalla mutum 40.

Hukumar tsaron Amurka PENTAGON ta ce ta kai harin ne don hallaka wasu ‘yan kungiyar Alqa’ida. Gwamnatin Damaskas ta amince da tsagaita wuta da Rasha ta jagoranta bayan tsawon wata 4 a na ruwan boma-bomai a yankin.

Ibrahim Baba Suleiman*
Jibwis Media & Publicity
01-Muharram-1440
01-September-2019

SHARE
Previous article
Next articleHotuna

1 COMMENT

Leave a Reply to Tajuddeen Haruna Gurun Cancel reply