LABARAI A TAKAICE

Hukumar Alhazan Naijeriya (NAHCON) ta dawo da Adadin Alhazai dubu 27,093, cikin sawun jirage 56 zuwa gida Naijeriya bayan kammala Aikin Hajjin Bana.

Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya a shiyyar Benin ta ce ta kama wata mata mai damfara ta yanar gizo da kan hada kai da abokan ta’annatin ta da ke Amurka.

Matar dai wacce EFCC ta kama da ke jerin mutanen da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ke nema, ta yi amfani da hanyar musayar kudi ta yanar gizo da ba ruwan sa da babban banki da a ke kira “BITCOIN” inda a ke gano darajar BITCOIN 185 ga matar da hakan ya kai zunzurutun kudi Naira miliyan 656,371,490.

Shugaban EFCC shiyyar Benin Mukhtar Bello ke cewa an kama matar da bai ambaci sunan ta ba ta hanyar musayar kudin BITCOIN inda ta kan tara bayanai jagororin kamfanoni ko kasuwanci masu hulda da ketare ta turawa ‘yan uwan hadin bakin ta na Amurka da kan aiwatar ta damfarar.

Bayan kammala bincike kan kashe rayuka ba bisa doka ba a Najeriya, majalisar dinkin duniya ta gabatar da rahoton ta kan wannan kalubale mai muni. Binciken dai ya gudana karkashin jagorancin jami’ar bincike Agnes Callamard tun ranar 16 ga watan jiya.

An sha zargin jami’an tsaron Najeriya da wuce gona da iri wajen ladabtar da wadanda su ke tuhuma da hakan kan hada har da illar da kan kai rasa rai. Gwamnatin Najeriya ta sha musanta irin wannan zargi da ya shafi jami’an tsaron wadanda kan yi alfahari da cewa su na saida ran su don sauran jama’a su samu salama.

Fasa dutse don aikin tagwayen hanyar Akwanga zuwa Lafiya har Makurdi a jihar Binuwai ya sanya rufe hanyar daga Akwanga zuwa Nassarawa Eggon na wani lokaci. Dama hanyar na da duwatsu da kwane-kwane da indai an samu fadada hanyar zai taimaka wajen rage hatsari. Yawancin hanyoyin gwamnatin taraiya da kan hada garuruwa sun lalace da ramuka da kuma ‘yan fashi da makami musamman da dare.

Saudiyya ta sauya Khalid Alfalih daga mukamin shugaban kamfanin ta na man fetur ARAMCO inda ta nada Yasir Al-Rumayyan ya maye gurbin sa.

Khalid Alfalih ya rike mukamin na babban kamfanin fetur na duniya tun shekarar 2015. Kafin sabon mukamin, Al-Rumayyan ne shugaban hukumar kula da hannun jarin gwamnatin Saudiyya. Har yanzu dai Al-Falih ne ministan fetur na Saudiyya kuma wakilin ta a kungiyar kasashe masu arzikin fetur na duniya OPEC.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
04-Muharram-1441
04-September-2019

1 COMMENT

Leave a Reply to Usman sa'adu Cancel reply