ADDU’AR MUSIBA.

Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo. Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Ummu Salama tace; naji Manzon Allah mai Tsira da aminci yana cewa: “Babu wani bawa da wata Musifa zata same shi sai yace, Innaa Lillahi Wa Innaa ilaihi Raaji’un ya Ubangiji ka bani lada cikin musifata, ka Canja min da abin da yafi alheri. Tace, Lokacin da Abu Salama ya rasu (Wato Mijinta) sai na fadi kamar yadda Manzon Allah mai tsira da aminci ya umurce ni, sai kuwa Allah ya chanja mini da wanda ya fishi alheri. Wato Manzon Allah mai tsira da aminci (Ya aure ta)”
(HADITH MUSLIM)

Mai karatu abin da wannan Hadisi yake karantar damu shine, a duk sanda Allah ya jarrabeka da wata Musifa abin da ake so ya fara fita a wannan lokaci daga gareka shi Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, bakin da baya karya yana maka bushara da cewa zaka samu abin da ka rasa da wanda ya fishi alheri, Allah yasa mu dace.

4 COMMENTS

LEAVE A REPLY