An Karrama Engr. Salisu Gombe

Shuagban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala lau, ya mikawa Sakataren Ayyuka na Majalisar Agaji ta kasa, Engr Salisu Muhammad Gombe Lambar yabo da wata Hukuma ta karramashi a Abuja.

Da yake jawabi Shugaban kungiyar na kasa yace lallai Engr Salisu Gombe ya cancanci wannan girmamawa, bisa jajircewa da yake wajen hidimtawa Al’umma dama cigaban wannan addini ta bangarori da dama.

Babban Daraktan Agaji ta tarayyan Nigeria Engr. Mustapha Imam Sitti tare da Sakataren Agaji na kasa Abba Yahaya katsina, da wasu daga cikin shuwagabannin kungiyar Suna cikin wadanda aka karrama a wajen taron.

Daga karshe Sheikh Bala Lau, yayi musu Addu’ar fatan alkhairi da Majalisar agajin gaba daya .

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY