An Umurci Malamai da limamai su dukufa wajen addu’oin zaman lafiya a kasa

Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau

An Umurci Malamai da limamai su dukufa wajen addu’oin zaman lafiya a kasa. Kiran ya fito ne daga Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, a wata tattaunawa da yayi da jami’in yada labaru ta kafar yanar gizo Alh. Ibrahim Baba Suleiman ta wayar tangaraho.

Sheikh Bala Lau ya umurci Limamai da Malaman kungiyar a fadin Naijeriya, cikin birane da kauyuka da Su dukufa da addu’oi musamman a masallatan juma’a da na kamsus-salawat, da sauran majalisin karatuttuka wajen ganin Allah ya kawo zaman Lafiya mai dorewa a kasar Naijeriya.

Haka zalika Sheikh yace a sanya jihar Katsina da hanyar Abuja zuwa kaduna a addu’oi na musamman domin Allah ya kawo karshen wadannan kashe-kashe da garkuwa da mutane da ya addabi wadannan yankuna.

A karshe yayi kira ga yan uwa musulmi da a yawaita “ISTIGFARI” sannan kowa ya tuba daga ayyukan da yasan laifi ne ga Allah, sannan a jira taimako daga Allah.

Allah ya bamu zaman lafiya mai dorewa ga kasar mu ta Naijeriya mai tarun albarka. Amin.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY