An Nada Sabon daraktan Agaji a Jihar Niger

A asabar din nan babban daraktan Agaji na kungiyar JIBWIS Engr. Mustapha imam sitti Ya tura wakilai zuwa jahar Niger domin tabbatar da sabon Director yan Agajin jahar Niger bayan mutuwar daraktan Agaji na jahar marigayi mallam Abdulbaseer Musa.

Wakilan daga majalisar kasa, Wanda Tirkashin Zazzau ya jagoranta, ta tabbatar da mallam Muhammad A yawa a matsayin sabon daraktan agaji na jihar Niger.

Sauran ‘yan tawaga sun hada da Mallam Muhammad sani abubakar minna, Mallam Auwal Musa gulma, Mallam Mustapa Nasiru Batsari.

Muna Addu’an Allah yataya shi riqo. Amin.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY