Izala ta gabatar da Murna gami da Nasiha ga Dr. Ali Pantami

Kungiyar Wa’azin Musulunci ta JIBWIS reshen jihar Bauchi ta mika takardan taya murna, da shawarwari, da kuma addu’oi na fatan alkhairi ga sabon ministan sadarwa ta Naijeriya Sheikh Dr. Isah Ali Pantami, da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu da karamar ministan Sana’o’i da hannun jari Amb. Maryam Katagum wanda shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada su a matsayin ministoci cikin watan da ya gabata.

Shugaban Kungiyar ta Jihar Bauchi Imam Muhammad Inuwa Dan’asabe shi ya jagoranci tawagar har zuwa birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis din da ta gabata, domin basu rubutacciyar takardan da kuma gabatar musu nasiha akan irin nauyin da yake kansu.

Yayin dayake jawabi, Shugaban yaja hankalinsu dasuji tsoron Allah a lokacin da suke gabatar da ayyuakansu, kana su zamanto jagorori nagari wanda sauran za suyi koyi dasu.

A nasa bangaren, Babban limamin Masallacin Juma’a na Gwallaga Sheikh Imam Ibrahim Idris yaja hankalisu, dasu sanya tsoron Allah su kuma zama jakadu nagari, kana ya shawarci ministan sadarwa Dr. Isah Ali pantami, kan cewa kada ya tsaya da ayyukan da’awa kawai domin ya zamo minista, domin ayyukan da’awa agareshi a daidai wannan lokaci babban hidimane wa musulunci.

Cikin jawabinsa, shugaban komitin marayu na Kungiyar a Jihar Bauchi Hon. Isah Musa Matori yaja hankalin ministotin ne akan su dage wajen kawo ababen more rayuwa a yankunansu saboda zamansu a wannan kujeru suna wakiltar alummar jihohinsu ne, ya kuma yaba wa ministan sadarwa game da kokarin da yake na rufe layukan waya marasa rijista wanda yawansu yakai miliyan Tara. Daga karshe ya kara da cewa su cigaba da bada shawarwari nagari ga maigirma Shugaban kasa Muhammad Buhari domin ciyar da Najeriya gaba.

Yayin da yake gabatar da jawabin godiya, Sheikh Isah Ali Pantami ya karbi tawagar da kansa, sannan ya nuna jin dadinsa kwarai da gaske bisa yadda aka nuna masa kauna da kuma addu’o’in da akayi tayi tun daga lokacin da aka ayyana sunansa a jerin wanda za’a basu wannan mukamin, sannan kuma ya bukaci da’a cigaba da sanya shi cikin addu’oi na musamman domin samun nasarar wannan aiki nashi.

Sauran ministoti guda biyu Malam Adamu Adamu da Amb. Maryam Katagum wanda Masu tallafa musu na musamman suka karbi tawagar a madadinsu sun nuna farin cikinsu da jin dadinsu kuma sun tabbatar da wannan sako kamar a kunnensu aka fada zasu isar musu kamar yadda aka basu.

Daga Karshe an gabatar da addu’a ta musamman wanda Alaramma Adam Adam Muhammad ya jagoranta.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY