Majalisar Agaji ta kasa, ta kai ziyarar ta’aziyya a a garin Bauchi

Hoto Engr. Salisu Muhammad Gombe da Muhammad Sabitu Yusuf

A safiyar lahadin nan Sakataren tsare tsare a majalisar agaji ta kasa, Engr. Salisu Muhammad Gombe ya jagoranci tawaga ta ‘yan agaji wakilan kasa zuwa garin Bauchi domin cika umurnin babban Daraktan Agaji na Kasa Engr. Mustapha Imam Sitti, na gabatar da ta’aziyyar rasuwar Dan Gidan MAL. MUHAMMAD SABITU YUSUF (Asst. Nat. operation Officer) na majalisar agaji ta kasa.

Marigayin mai suna SUHEL SABITU YUSUF ya rasu ranar asabar 21/9/2019 a garin BAUCHI.

Muna addu’ar Allah ya gafarta masa.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY