Allah ya yiwa Sakataren IZALA na jihar Borno Rasuwa

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN

Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, a madadin kungiyar na mika ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwa, da kungiyar IZALA ta jihar Borno, bisa rasuwar Sakataren Kungiyar Izala Reshen Jihar Borno Barista Baba Gana Modu.

Babagana Wanda ya rasu a yammacin lahadin nan, Za Ayi Jana’izarsa a Litinin dinnan da misalin karfe goma na safe (10:00Am), a Masallacin Juma’a na Federal Low-cost dake birnin Maiduguri a jihar Borno insha Allah.

Allah yaji kansa da Rahama, ya kyautata makwanci. Ameen

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY