CETO YARA 9-JIBWIS TA JINJINAWA RUNDUNAR ‘YAN SANDAN NAJERIYA DA KIRA GA DAMKE MASU SAYAN YARAN

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Kungiyar JIBWIS ta samu labarin ceto yaran nan 9 na Kano cikin farin ciki daga azzalumai da su ka sace su, kazalika ta na jinjinawa rundunar ‘yan sanda don cimma wannan gagarumar nasara kan lamarin da ya zama cikin dubu tsawon shekaru.

A takardar manema labaru daga kungiyar ta AHLUSSUNAH ,shugaban kungiyar Imam Abdullahi Bala Lau ya nuna matukar takaici yadda wasu miyagun iri za su hada baki su sace yaran musulmi don sayar da su ga wasu wai marar sa ‘ya’ya don rainon su a matsayin ‘ya’yan su; inda lamari mafi tada hankali shi ne sauyawa yaran addini daga musulunci zuwa kiristanci. In an duba wannan laifi a ma’aunin hankali ya kasu kashi uku da ya hada da sace yaran,sayar da su tamkar bayi da kuma sauya mu su addini zuwa kirista.

Sheikh Abdullahi Bala ya yi kira ga gudanar da binciken kwakwaf don gurfanarwa gaban shari’a, ba madugun masu satar Paul Onwe da matar sa da sauran gungun jama’ar sa kadai ba; a gano duk wadanda su ka sayi yaran da duk masu hannu kai tsaye ko ta bayan fage ga wannan mugun aiki don hukunta su.

“da yardar Allah za mu cigaba da bin diddigin wannan lamari har karshe don tabbatar da yin adalci ga yaran” Inji shi.

Mu na amfani da wannan sako wajen yabawa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Ahmed Iliyasu don tsayin dakar sa kan kare rayuka da ‘yancin al’umma daga miyagun iri da kan yi fako don danne hakkin yara ko kuma sace yaran musulmi da juya mu su addini zuwa na mabiya kirista.

JIBWIS na da ra’ayin zurfafa bincike kan wannan lamari zai taimaka wajen gano wasu yaran ma na musulmi da barayin su ka sace, su ka bautar da su.

A karshe mu na kira ga iyaye su sanya ido kan zirga-zirgar ‘ya’yan su dare da rana da kuma tuntubar halin da yaran ke ciki a makarantun da su ke karatu na addini da na boko.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY