TASHAR SUNNA TV:

A shekarar da ta wuce ne kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah wa Iqamatis Sunnah ta kasa karkashin jagorancin Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya samu nasarar Samun tashar Sunna TV, Tashar wacce a yanzu miliyoyin jama’a daga sassan duniya suke kallonta, ta samu karbuwa irin wacce baza ta misaltu ba, a yayin da ake gabatar da wa’azozi, darussa, debe kewa, da tallace tallace, kuma ya kara bude wata tasha ta Sunna TV 2 dan sauran yarukan da suke kasashen africa suma su amfana da wannan garabasar da muke samu a gidajen mu na wa’azozi.

Deputae Isah Sale, wanda sanata ne a kasar Benin shine bawan Allah da ya bude wannan tasha shi kadai, kuma ya danka amanarta a hannun kungiyan JIBWIS TA kasa, A Office din Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau dake Abuja, ya kuma bada gudun mawa dari bisa dari ga dukkan tsarin da zai kawo ci gaban tashar dan samun karbuwan ta a Duniya, Allah ta’ala yana cewa: “Wadanda sukayi kokari cikin al’amarin mu, wallahi zamu shiryar dasu tafarkin mu, kuma Allah yana tare da masu kyautatawa”. Al’ankabutu:69.
Allah ta’ala yace: “Wanda ya aikata kwatankwacin kwayar zarra na alkhairi zaiga sakamakon sa. Azzalzala:7.
Allah ta’ala yace: “Abin da kuka gabatar ga kawunanku na alkhairi zaku same shi a wajen Allah, shine mafi alkhairi kuma mafi girman lada.” Al-Muzzammil: 20.
Annabi mai tsira da aminci yace kuyi gaggawan ayyukan alkhairi kafin zuwan fitinu kamar yankin dare mai tsananin duhu, mutum yana wayar gari da imani, ya yammata kafiri, ya kan yammata mumini ya wayi gari kafiri, yana sayar da addininsa da dan abin duniya. (Muslim).

To kunga in mun duba wadannan ayoyi da hadisai duka suna magana ne akan ka tabuka ayyuka na alkhairi da dukiyan da Allah ta’ala ya baka, kamar yadda wannan bawan Allah Deputae Isah Saleh ya gina wannan tasha ta Sunna tv ake kallo a dukkan sassa na duniya, muyi kokarin taimakawa addinin Allah da dukiyar da ya bamu, zamu samu sakamako mai kyau daga Allah (SWT)

A kokarin kungiyar JIBWIS ta kasa karkashin jagora tsayayyen namiji Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau tana kokarin gina gina Studio ga jihohi na zamani tare da kayan aiki irin na zamani saboda samun saukin gabatar da shirye shiryen tashar, zuwa yanzu an samu kammala studio na Sokoto da Kano, saura Katsina, Adamawa, Taraba da Gombe suna kan aikin basu kammala ba, bayan da kungiya ta gina nata Studio a garin Bauchi, wanda shine studio na farko da ya fara aiki kuma mallakar kungiya na kasa.

Kungiyar ta Jibwis tana baiwa masu sauraro hakuri tare da musu albishir cewa zata kara inganta harkan Wannan tasha yadda zamu hada kafada da kafada da sauran tashoshin Television na duniya, ga dukkan masu son bada shawara kan wannan tasha mai albarka suna iya turo sako kai tsaye ta dukkan hanya mafi sauki da zata samu shiga ga Shugaban kungiyar ta kasa.

Allah ya taimakemu kan niyyar mu ta alkhairi ya bamu ladan abin da muke aikatawa, ya mana tsari da Shaidan da Shaidanu dan ganin aikin addini bai tasaya ba, ya karfafa imanin mu akan bin Allah (SWT).

9 COMMENTS

LEAVE A REPLY