MUHIMMANCIN TAIMAKON FARKO GA AL’UMMA.

ALHAJI SALISU MUHAMMAD GOMBE, Shi ne Sakataren shirye-shirye na rundunar Agaji ta kasa, sannan shugaban kungiyar Izala ta jihar Gombe. Umar Mohammed Gombe wakilin jaridar Hausa Ledersship ya kebe shi waje guda, jim kadan bayan kammala babban taron hadin kan Ahlussunnah na Afirka ta Yamma, a birnin Legas. Inda Sakataren ya warware zare da abawa game da ayyukan rundunar Agaji ta kungiyar Izala. Ga yadda hirar ta kasance dalla-dalla kamar haka:

Ranka ya dade a matsayinka na Sakataren shirye-shirye na Rundunar Agaji na kasa, shin mene ne Agaji kuma yaushe aka fara Agajin?

Alhamdulillahi wassalatu wassalamu ala rasulullah. Assalamu Alaikum warahmatullahi. To an fara Agaji a wannan kungiya yau fiye da shekaru 30 da suka gabata. Sannan abin da ake nufi da Agaji shi ne taimako, idan an ce Agaji, to wani mutum ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin ya taimakawa dukkan wanda ke bukatar taimako.

Sannan dole ya zama mai iya Agajin ba wanda za a Agaza masa ba. Dan Agaji ya na taimakawa wanda hadari ya rutsa da shi wajen ba shi taimakon farko wanda muke cewa (First Aid) wannan hadari na jirgi ne ko mota ko babur ko keke da sauransu, sai kuma abin da ya shafi gobara, annoba, ambaliyar ruwa da makamantansu.

To a irin wannan lokaci ne za mu bada taimakon farko kafin akai majinyaci asibiti ta hanyar tsaida jinin dake zuba daga raunin, mu tsaftace wajen sannan mu daure da kyalle mai kyau don hana shigar wata cutar daban.

Baya ga haka kuma idan za a yi wa’azi ko wani taro na addini, mu ne ke fara zuwa wajen don gudanar da shirye-shirye wajen saukaka cunkoso ga jama’ar da za su zo a yayin taron, mu samar da yanayin tsaro tare da daidaita kayayyakin wa’azi, samar da haske, kayan sauti da sauransu.

Ire-iren wadannan bukatu kungiyar Izala ta ga dacewar kirkiro rundunar Agaji da za ta yi aiki tukuru tun fiye da shekaru 30 da suka gabata. Tun lokacin wannan runduna ta fara gudanar da ayyukanta, sannan kuma ta ke kokarin inganta tsare-tsarenta a kullum don dacewa da kunkiyoyin duniya daban-daban kamar yadda ake gani a yau.

Baya ga shirya taruka da kuma wa’azi akwai kuma wani aikin da rundunar take gudanarwa don tallafawa al’umma?

Sosai ma kuma, ita wannan runduna ayyukanta a tsare suke kamar yadda na bayyana cewa idan hatsari ya rutsa da mutum ko wane iri ne mu kan jajirce mu taimaka, sannan a lokacin aikin Hajji zaka ga jama’armu a sansanonin alhazai su na taimakawa a yayin tafiya kasa mai tsarki da kuma dawowa.

Don haka zaka ga al’umma ne daban-daban suke taruwa a filayen tashi da saukar jiragen sama, wasu daga kauyuka suka fito ba su san ko ina ba, don haka ‘yan Agaji za su taimaka musu wajen nuna musu yadda za su yi har a cimma nasara. Sannan shi ma wayayye akwai fannonin da za a taimaka masa a sansanin kafin ya tashi zuwa kasa Mai Tsarki.

Sannan rundunarmu ta na taimakawa a lokacin shirya tarukan gasar karatun Alkur’ani Mai Tsarki, don daidaita cunkoson jama’a. Sannan kuma kar ka manta muna da wata doka, dokar ita ce, wajibi ne idan ana gudanar da wani taro wanda yake halastacce na addini dan Agaji ya je ya taimaka. Kuma dukkan wani taro da addini bai yarda da shi ba ko da an danganta shi da addini to a wajen dan Agajin Izala haramun ne ya halarci taron.

Kamar yadda ka bayyana tsare-tsaren Agaji wajen daidaita al’amura a taruka, wani zai yi mamakin yadda kuke yin wannan aiki har ku kai ga nasara ba tare da makami ba, shi me ye sirrin?

Ai rundunar Agaji ba ta yaki ba ce, don haka akwai wasu halayya da ake bukatar dan Agaji ya dabi’antu da su. Na farko ya zama mutum ne mai tsoron Allah da akida, idan ka na da kyakkawar akida zaka iya yin mu’amala da kowane irin mutum, sannan dan Agaji ya zama mai hakuri da juriya ya zama maras tsoro.

Idan dan Agaji ya siffantu da wadannan siffofi, to duk yadda mutum yake za ka iya tunkararsa da irin halinsa, wani ya na da kaushi, wani ya na da sauki, to duka zaka yi ta kokari har akai ga samun nasara ba tare da an yi amfani da makami ba.

Misali a farkon lokacin da muka fara zuwa taimakon Alhazai a sansanoninsu mun fuskanci matsaloli da daman gaske kafin su fahimce mu, wani zai zage ka, wani ya hana ka taba kayansa, wani ma har miyau zai tofa maka, amma babu makami babu komai muka yi ta hakuri, Alhamdulillahi har Allah Ya kawo wannan lokaci da mutane suka fahimcemu, su na kaunarmu, wanda a yanzu zan iya cewa kusan dukkan wani abu ya koma hannun ‘yan Agaji a sansanonin Alhazai, mu ne amintattu da ake son hulda da mu a yau.

Wani lokaci akan ga ‘yan Agaji suna aiki kafada da kafada da jami’an ‘yan sanda a lokacin taruka, shin ku ne ke neman karin taimako daga gwamnati don cimma nasarar aikin ne ko kuwa?

To da farko idan taro ne da kungiyar Izala ta shirya, to ita kungiya ce da take bin dokokin Allah (SWT) sannan ta na bin ka’idojin kasa wadanda ba su saba wa Allah Madaukaki ba. Saboda haka duk inda Izala za ta yi wani taro a bayyane take yin sa, babu wani asiri a ciki, don haka muke rubutawa hukuma cewa za mu yi taro akan kaza, kuma a guri kaza, ita kuma gwamnati sai ta turo jami’an tsaro mu yi aiki tare da su, su su na da bindiga mu kuma mu na tare da jama’a, idan mun roki jama’a muka nuna mu su Girman Allah sai ka ga sun biyu yadda ake so, kasancewar mu na da alaka tsakaninmu da jami’an tsaro sai ka ga an yi taro lafiya an tashi lafiya.

Sannan mu na mutunta su su ma suna mutunta mu, yadda muke sara wa na gaba da mu, su ma haka muke sara wa babba a cikinsu.

Ko zaka sanar da mu adadin ‘yan Agajin da kuke da su a Nijeriya, musamman idan aka kwatantaku da jami’an ‘yan sanda ma su adadi dubu 360?

To wannan adadi na ‘yan sanda dubu 360 da Nijeriya take da su ai ko kusa da adadinmu ba su kai ba, domin ‘yan Agajin Izala mun fi milyan biyu (2,000,000) a tarayyar Nijeriya yanzu haka. Sannan duk wani taro da ka gani komai girmansa, wani dan adadi ne kadan suke turawa, ko a wannan taro wadanda ba su zo ba sun ninninka wadanda kuke gani anan nesa ba kusa ba.

Idan mutum ya na son zama dan Agaji, wadanne ka’idoji ya kamata ya bi don zama dan agajin Izala?

To Alhamdulillahi, wannan kungiya mai albarka ta na da tsari da kuma ka’idoji a kowane fanni na ta. Da farko idan mutum ya na son ya zama dan Agaji a wannan kungiya, to dole ya zama ya na da kyakkyawar akida wacce ba a gurbata ta da komai ba. Sannan na biyu dole sai ka samu tazkiya daga mai unguwarku wacce za ta tabbatar mana cewa kai mutumin kirki ne ka na da rikon amana da sauransu.

Sannan na uku dole ya zama ka na da sana’a ba zaune kake ba, ma’aikacin gwamnati ne ko dan kasuwa ko manomi ko mai sana’ar hannu. Idan kuma yaro ne karami to ya zama ya na makaranta. Sannan na hudu dole ya zama ka na aji ko makaranta da kake karatu, saboda ba ma daukar wanda bai san addini ba. Sannan na biyar ya zama wanda zai iya karbar horaswa ta yadda zai san ka’idojin aikin yadda ya kamata.

Sannan na shida za a yi ma sa jarabawa kan abin da aka koya ma sa idan ya ci shike nan ya zama dan Agaji. Sai na bakwai, dan Agaji shi da kan sa zai dinka kayan Agaji da duk wasu kayayyaki na aikin. Sannan na karshe zai amince cewa idan Allah Ya masa rasuwa kayansa na Agaji ba na magada ba ne, za a dawo da su a baiwa wani ya ci gaba da amfani da su, shi kuma Allah Ya ba shi ladar a makwancinsa.

Haka nan Allah Ya sawwaka idan ya aikata wani laifi da za a kore shi nan ma zai dawo da kayan Agajinsa a baiwa wani yaci gaba da amfani da su. To wadannan su ne ka’idojin zama dan Agaji a takaice.

Sannan har ila yau akwai dattijo dan shekaru 60 ko 70, sannan kuma sai aga yaro dan shekaru shida ko bakwai, shin ya tsarin daukar aikin yake a matakin shekarun yaro, ko kuma na yin ritaya ga wanda ya tsufa?

To aikin Agaji dai ana son mutum Baligi mai hankali, wanda za a iya sanya shi ko wane irin aiki, sannan zai iya wakiltar kungiyar a kowane lokaci. Amma a kasa kamar yadda ka fadi cewa akwai yara kanana, e, haka ne, mu na da wani mataki na daukar yara kanana saboda koyar da tarbiyya, mu yi mu su tirenin mu ba su tarbiyya su taso a haka. mu na daukarsu saboda dalilai kamar haka; Na farko za su samu tarbiyyar da za su amfani iyayensu, saboda ba su da kasala, don haka za su je aika, diban ruwa, kai nika da sauransu.

Domin idan yaro ya saba da aikin Agaji, to babban abin ba ya so shi ne ace za a kwace inifom dinsa, don haka duk wanda aka kawo rahoton ya ki yin aika a gidansu idan aka yi ma sa barazar kwace inifom din sa sai ya yi ta kuka sannan ya yi alkawarin zai gyara halayensa.

Na biyu mu kan yi amfani da yaran don burge jama’a a wajen taruka, wajen sanya su yin dirama ko fareti mai ban sha’awa. Sannan na uku za su ta so da tsoron Allah da rikon amana.

Sai kuma maganar ritaya, gaskiya mu ba mu da wani matakin yin ritaya a wannan aikin saboda shekarun mutum, sai dai ba ma daukar mutum a karon farko idan shekarunsa suka kai 50 ko 60, saboda a lokacin ya fara rauni.

Amma idan ya fara aikin tun ya na matashi, to ba za mu yi ma sa ritaya saboda tsufansa ba, sai dai za a sanya shi aiki irin wanda ya dace da shi, tunda aiki ne na addini ba ka hana mutum samun alherin dake cikinsa, sai ya yi ta yi har Allah Ya dauke shi.

Ko zaka bayyana mana yadda tsarin karin girma yake a wannan aiki na Agaji?

To wannan runduna a karkashin kungiyar Izala mun kasa mukamai ne zuwa kashi shida. Akwai abin da muke kira ‘unit’ ko wane unit akwai adadin ‘yan Agajin da suke wurin, idan suka wuce wannan adadin sai su zama ‘Detachment’ daga nan kuma sai ‘Dibision’ sai karamar hukuma, sai jiha, sannan matakin kasa gaba daya.

Don haka daga kan ‘Unit’ din nan akwai shugaba akwai mataimakin shugaba, akwai sakatare, akwai sakataren tsare-tsare da sauransu. Haka nan dukkan wadanna matakai akwai shugabanninsu har zuwa kan Daraktan jiha zuwa Babban Darakta na kasa. Sannan mutum ya na samun karin girma ne bisa cancanta, ilmi da kuma kwazonsa wajen aiki.

A sau da dama Malamanku na Izala sukan yi suka ga ‘yan siyasa, musamman a lokacin zabe, inda wadansu ‘yan siyasar ke yin hayar matasa da za su rika kawo cikas ko su sace akwatin zabe da sauransu, shin ku na da wani tunani wajen sanya jami’anku na Agaji su rika bayar da tsaro a lakacin zabe ko kuwa?

A’a la! Wannan kungiya ce ta addini ba ta siyasa ba. Don haka ba mu da wani tunani na aika ‘yan agajinmu wajen tsaron akwati a lokacin zabe. Amma kamar yadda ka ce, wannan kungiya ta na fada da irin wannan dabi’a na rashin adalci, sannan gazawar gwamnati wajen samar da tsaro shi yake kawo haka, domin duk mutum kuri’a guda yake da ita, amma idan gwamnati ta tsare wannan amana dake kanta, babu yadda za a yi irin haka ya ci gaba da faruwa a kasa irin Nijeriya.

Sai dai kamar yadda wasu ‘yan siyasar suka dauki matakin cewa, a kasa a tsare a raka, to wannan ba aikin dan Agaji ba ne, na dukkan al’umma ne, kar ka manta dan Agaji ya na da yancin da zai je ya jefa kuri’a kuma ya sa ido wajen ganin an yi ma sa adalci ga wanda ya zaba, amma ba da sunan Agaji ba, zai je ne kamar kowa cikin kayan gida ya jefa kuri’arsa ga wanda yake so.

A karshe wane karin haske za ka yi game da wannan taro wanda ya hada dukkan Afirka ta Yamma baki daya, game irin rawar da rundunarku ta Agaji ta taka har aka kai ga wannan nasara da za a iya cewa shi ne irinsa na farko a Nijeriya?

To da farko dai sai mu ce ‘Alhamdulillahillazi Bini’imatihi ta timmussalihat’ wannan nasara ce da Allah Ya ba mu. Sannan mu na godiya ga shugabannin wannan kungiya wajen kyakkyawar jagoraci ba ga wannan taro kawai ba, a dukkan tarukan da ake shiryawa. Musamman shugaban kungiyar na kasa baki daya, Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, bisa dimbin gudumowa da goyon baya da yake ba mu.

Sannan mu na godiya ga Babban Daraktan Agaji na kasa, Injiniya Mustapha Imam Sitti, wanda ya sanar da mu cewa shugaba ya ba shi umarnin cewa mu kasance a birnin Legas tun kwanaki uku kafin taron, don daidaita al’amura yadda ya dace. Kuma Legas ba kamar sauran garuruwa ba ne, sannan ana da baki daga sassan kasashe daban-daban na Nahiyar Afirka.

Kuma cikin ikon Allah mun shirya komai yadda ya kamata, domin ta kowace kusurwa ka shigo Legas har zuwa inda ake gudanar da taron a babban filin taro na Tafawa Balewa Skure dake Ikoyi, za ka rika ganin yaranmu ko ina su na gwada wa baki inda za su bi. Don haka Babban Darakta ya jagoranci wannan aiki har aka kai ga samun nasara kamar yadda kuke gani.

Don haka Alhamdulillahi bisa wannan Agaji da Allah Ya yi mana, musamman kasancewar taron shi ne irinsa na farko da aka taba yi a Nijeriya Alhamdullahi.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY