KUNGIYAR IZALA TA UMURCI A FARA AL’QUNUT A DUK FADIN KASARNAN

Shugaba Ash-Sheikh Imam Bala Lau ya Umurci dukkan masallatai da makarantu na kungiyar da su dukufa da Al’Qunut a duk fadin kasarnan dan neman agaji daga Allah bisa yanayin da musulmi da musulunci suke ciki a kasarnan.

Kungiyar Izala tayi kira ga masu Hannu da Shuni Su taimakawa Samari da ‘yan mata wurin Aurar dasu dan rage yawan matasan a layi.

Alhaji Dahiru Mangal ya amsa da wannan kira kuma yace nan bada dadewa ba za’a kafa kwamiti dan gabatar da wannan shiri na aurar da yan mata da samari a jihar ta katsina, ya kuma godewa Allah da ya sanyawa kungiyar izala tunanin aikata ayyuka na alkhairi a duk inda suke.

Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan, yayi Addu’oi na musamman kan Allah yayi maganin duk wanda yake da hanu a cikin wannan mugun aiki da ake aikatawa musulmi a kasarnan.

Malaman da suka gabatar da wa’azi a wannan dare sun hada da;
Ash-Sheik Imam Abdullahi Bala Lau.
Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina.
Sheikh Dr. Alhassan Sa’eed Adam Jos.
Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe.
Sheikh Abubakar Giro Argungu.
Sheikh Mukhtar Zinder.

Allah ya bamu ikon aiki da wa’azozin da ake mana kullum, Amin.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY