SHAWARWARI GUDA 10 DAGA BAKIN SHAHEED HASSAN AL-BANI.

Ka karanta ka yi tunanin dabbaqawa.

1. Tashi ka garzaya zuwa ga sallah, duk lokacin da kaji kiran sallah a duk halin da ka ke.

2. Ka rika karanta Alkur’ani tare da kokarin fahimtar sa, ko sauraron tilawarsa, ko ambatin Allah tare da tsarkake sunan sa. Kar ka yarda ka bata lokacinka ba tare da yin wani abu mai amfani ba.

3. Yi kokarin koyo dayin Magana da mafi kyawun larabci, don hakan yana daga alamun musulunci.

4. Ka nisanci yawan musu akan dukkan al’amura, domin yawan musu bas hi da wata fa’ida.

5. Ka daina yawan dariya, domin zukatan bayain Allah kullum cike suke da nitsuwa.

6. Ka nisanci yawan RAHA, al’umma mai manufa da gaske take al’amuranta.

7. Kar ka rinka yin ihu, domin yana cutar da wasu.

8. Ka guji cin naman mutane da cin fuska, kar ka amabci aibin kowa.

9. Ka gabatar da kanka ga ‘yan uwanka musulmai a karon farko, domin manufar wannan sakon na mu shine kyakkyawar fahimtar juna.

10. Ga abubuwan yi da yawa, kuma lokacin yinsu takaitacce ne, don haka taimakawa ‘yan uwan ka wajen amfani da lokacin su.

Wadannan shawarwari da Imam Hasan Al-Banna, ya bawa al’ummar Musulmai.

Allah ya bamu ikon aiki da su.

Fassarawa:

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY