ABUBAKAR SIDDEEQ (RA) ZABI NE NA ALLAH DA MANZON SA !

Jagoran Ahlul Bait Aliyu Ibn Abi Talib (RA), yace : Mun shiga wurin Manzon Allah (SAW), sai muka ce: Ya Manzon Allah Ka sanya mana Khalifah, sai yace : Idan Allah Yasan akwai Alkhairi acikin ku, to zai shugabantar da mafi Alkhairin ku akan ku. Sai Aliyu (RA) yace : Sai Allah Ya tabbatar da Alkhairi acikin mu, sai Ya Shugabantar da mafi Alkhairin mu Abubakar (RA), akanmu. To wannan Hujjah ce mai Karfin Gaske ga dukkan wanda yake Da’awar son Aliyu Ibn Abi Talib, da ya yarda da abunda ya fada, idan shi ba zindeeqi bane.

An Sami Hadisi daga Jubaiyr Ibn Mud’em yace : Wata mata ta zo wurin Annabi (SAW), akan wata Bukatar ta, sai Manzon Allah ya umurce ta, da taje ta dawo, sai tace : Idan na dawo ban same ka ba fa ? Kamar tana nufin Mutuwa ne. Sai Manzon Allah yace : Idan baki same ni ba, to ki sami Abubakar (RA). Imamu Bukhari da Muslim suka Ruwaito Hadisin.

Ibnu Umar (RA), yace : Naji Manzon Allah yana cewa : Khalifofi Goma sha biyu za’ayi a bayana, Abubakar (RA) ba zai dade ba a Khalifanci ba. To wannan Hujjah ce mai karfi, domin acikin Khalifofin shine farkon wanda Manzon Allah ya fara Ambata.
Hadisin Huzaifa (RA) yace Manzon Allah (SAW) Yace : Kuyi koyi da wadannan Mutane biyu a bayana : Abubakar da Umar (RA). Imamu Ahmad da Tirmiziy da Imamu Hakim, suka Ruwaito shi.

A wani Hadisin na Huzaifa (RA), yace Manzon Allah (SAW) yace : Ni ban san Gwargwadon abunda ya rage na zamana acikin ku ba, saboda haka kuyi koyi da wadannan Mutane guda biyu a bayana, Abubakar da Umar (RA), Kuyi riko da Shiriyar Ammar, duk abunda Ibnu Mas’uud ya gaya muku to ku gaskata shi. Imamu Ahmad ne ya Ruwaito shi. Duk wannan gudar Hujjah ce dake nuna Manzon Allah yana yin Ishara zuwa ga Khalifancin Sayyidina Abubakar.

Huzaifa yace : Banuu Musdalaq sun aike ni wurin Manzon Allah in tambaye shi, wa zasu ba zakkar Dukiyoyin su, bayan yayi wafati ? Sai Manzon Allah yace Abubakar (RA). Imamu Hakim ya Ruwaito shi kuma ya Inganta shi. Wannan ma Dalili ne mai karfin Gaske.

Ummul Muminina A’isha (RA) Tace : Manzon Allah (SAW) a Rashin lafiyar sa ta Ajali, yace dani ki kira mun Babanki da Dan Uwan ki, har na rubuta musu Takarda, domin ni Ina jin tsoron kada wani Mai burinta yayi Burinta ( Khalifanci ), wani mai Magana yace nine na cancanta da ita, to Allah da Muminai sunki, sai dai Abubakar ne ya Cancanta da ita. Imamu Muslim da Imamu Ahmad su suka Ruwaito Hadisin.
Ba shakka wadannan Hadisan suna Fitar da dukkan wanda bai yarda da Khalifancin Abubakar ba, daga Da’irar Imani. Allah Ya Shiryar damu.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY