DUTSEN UHUD!

Manzon Allah saw yace: “Hakika dutsen Uhud yana son mu, muma muna son sa, Bukhari.

wata rana Manzon Allah saw yana kan Dutsen Uhud, sai Dutsen yayi girgiza, sai Manzon Allah saw yace: Ka tabbata ya Uhud, akanka akwai Annabi saw, Da Siddiqu (Abubakar), da shahidai guda biyu, (Umar da Usman)
Wannan dutse yana Arewa da Madina, Kusan Tsawon Kilometer hudu daga Masallacin Annabi saw, tsawonsa yakai kilo bakwai, fadinsa kilo hudu,
duk sanda nazo jikin wannan dutsen abu hudu nake tunawa,

1- Manyan sahabbai 70 da sukayi shahada wajan kare addinin Allah a wannan waje.

2- gumurzun da akayi a wannan waje tsakanin karya da gaskiya, mutum dari bakwai suka tunkari dubu uku.

3- wannan waje aka jiwa Annabi saw rauni, har jini ya zuba, saw.

4- wannan guri , tarihin ne na mazan jiya, daya kamata muyi koyi dasu wajan taimakon addini da rayukan mu, da kudin mu, da lokacin mu, Allah ka bamu ikon yada addini da kareshi, da duk damar da muka samu.

Duk Wanda bai samu zuwa wannan wuri va Allah ya kawo shi, mu da mukazo Allah ya dawo damu, Amin.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY