Musifa da Bala’i a Najeriya: Mene ne Mafita? – Sheikh Bala Lau

WANNAN ITACE FASSARAR KHUDUBAR DA SHUGABAN KUNGIYAR JIBWIS TA KASA ASH-SHEIKH IMAM ABDULLAHI BALA LAU YA BADA UMURNIN A KARANTA TA A MASALLATAN JUMA’A A DUK FADIN KASAR NIGERIA NAN.

Da Sunan Allah mai rahama mai Jin kai.
Bayan haka, Yan’uwa Musulmi! Hakika muna cikin wani irin jarabawa mai tsananin gaske cikin wannan Kasa tamu Nigeria; muna cikin jarabawar rashin mulkin adalci daga wasu shugabanni, muna cikin jarabawar fadace-fadace irin na kabilanci da addini, muna cikin jarabawar yan fashi da makami, da masu garkuwa da mutane, muna cikin jarabawwar masu daukan makamai domin yakar hukuma. Hakika, wadannan bala’o’i da muka ambata sun yi sanadiyyar tabarbarewar al’amura, sun yi sanadiyyar yaduwar talauci da rashin aikin yi tskanin yan kasa, sannan uwa-uba sun yi sanadiyyar kashe rayukan jama’a da yawa wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Fa inna lillahi wa inna ilaihi raaji’un!

‘Yan’uwa Musulmi! Lalle duk da wannan hali da muke ciki na tabarbarewar lamura ba za mu fidda tsammanin kyautatuwar wadannan lamuran ba, ba za mu fidda tsammanin samun rahamar Allah da tausayinsa gare mu ba. Saboda Allah Madaukakin Sarki ya ce cikin suratul Hijri aya ta 56: ((Babu mai yanke tsammanin samun rahamar UbangijinSa sai batattu)). Ya kuma ce cikin suratu Yusuf aya ta 87: ((Lalle yadda lamarin yake, babu mai yanke tsammanin samun rahamar Allah sai mutane kafurai)). Ya kuma ce cikin suratul A’araafi aya ta 156: ((Rahamata ta yalwaci dukkan kome, da sannu zan rubuta ta ga wadannan da suke tsare dokokin Allah suke ba da zakka, watau wadannan da suke imani da ayoyinmu)).

Yan’uwa Musulmi! Da ma ita rayuwar mutum haka take, wata rana cikin dadi, wata ranar kuwa cikin wahala, to amma su al’ummar Musulmi wadanda suka yi imani da Allah a matsayin Ubangijinsu, suka yi imani da Musulunci a matsayin addininsu, suka yi imani da Muhammad a matsayin annabinsu kuma Manzo zuwa gare su, lalle wadannan ba sa gushewa cikin alheri bayan alheri matukar dai zukatansu na rataye da Ubangijinsu, suna kuma kaskantar da kai gare Shi suna kuma nuna naciya cikin rokon Shi dare da rana.

‘Yan’uwa Musulmi! Lalle abu mafi alheri da al’ummar Musulmin Nigeria za su aikata domin samun kubuta daga bala’o’in da suke cikinsu yanzu, shi ne mura’ja’ar kai, da kyautata ayyuka, da kuma fiskantar Allah Madaukakin Sarki cikin kaskantar da kai, da kuma yawaita addu’a dare da rana; saboda ita addu’a wani babban makami ne ga salihan bayi, a gaskiya ma addu’a ita ce ginshikin ibada. Abu Dawud cikin hadisi na 1479, da Tirmizi cikin hadisi na 2969, da Ibnu Majah cikin hadisi na 3828 sun ruwaito da isnadi sahihi daga Nu’uman Dan Bashir cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Addu’a ita ce Ibadah)) daga nan sai ya karanta fadar Allah cikin suratu Gafir aya ta 60: {Ubangijinku Ya ce ku roke ni zan amsa muku, lalle wadanda suke nuna girman kai ga bauta mini da sannu za su shiga Jahannama suna kaskantattu}.

Ya ku al’ummar Musulmi! Hakika ita addu’a tana da wasu ladubba, wanda duk ya kiyaye su to in sha Allahu Ta’ala za a amsa masa addu’arsa. Ga mafi muhimmanci daga wadannan ladubba:-

Na daya: yin addu’o’in cikin lokuta masu daraja, kamar ranar Arafa, kamar cikin watan Ramadan, kamar ranar Juma’a, kamar sulusin karshe na dare, kamar tsakanin kiran salla da ikama, da makamantansu. Abu Dawuda ya ruwaito hadisi na 521’ da Tirmizi hadisi na 212, da Ahmad hadisi na 22,174 da isnadi sahihi daga Anas Dan Malik ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Ba a kin karbar addu’a tsakanin kiran salla da ikama)). Bukhari ya ruwaito hadisi na 935, da Muslim hadisi na 852 daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Lalle akwai wata sa’a a ranar juma’a musulmi ba zai roki Allah wani alheri a cikinta ba face sai ya biya masa bukatarsa, wata sa’a ce mara yawa)). Har yanzu Bukhari ya ruwaito hadisi na 6321, da Muslim hadisi na 758 daga Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Ubangijinmu Tabaraka wa Ta’ala yana saukowa cikin ko wane dare a sulusin karshe na dare yana cewa: Wa ke kira na in amsa masa, wa ke roko na in ba shi, wa ke neman gafarata in gafarta masa)).

Na biyu: Yin addu’ar cikin wani hali na daraja da ake ciki, kamar lokacin saukan ruwan sama, da lokacin da mai azumi yake yin buda baki, da lokacin sujuda cikin salla, da lokacin da bawa ke cikin halin tafiya. Muslim ya ruwaito hadisi na 482 daga Abu Huraira ya ce: Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Lokacin da bawa ke fin kusanci da Ubangijinsa shi ne lokacin da yake sujuda, saboda haka ku yawaita addu’a)). Abu Dawuda ya ruwaito hadisi na 1536, da Tirmizi hadisi na 1905, da Ibnu Majah hadisi na 3862, da Ahmad hadisi na 8375 da isnadi mai kyau daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:((Addu’o’i uku karbabbu ne ko shakka babu: addu’ar mahaifi, addu’ar matafiyi, addu’ar wanda aka zalunta)).

Na uku: Lokacin da mai addu’a zai yi addu’a ya fiskanci Al-Kiblah, ya daga hannayensa, ya sassauta muryarsa, ya kuma nisanci Saja’i. Allah na cewa cikin Bakara aya ta 186: {Idan bayina suka tambaye ka labarina ka ce: Lalle ni kusa nake, ina kuma amsa kiran mai kira idan ya kira ni, saboda haka su amsa mini, su kuma yi imani da ni, tsammanin za su shiriyu}. ya kuma ce cikin Israa’i aya ta 110: {Kada ka bayyanar da addu’arka, kada kuma ka boye ta, ka rika yin ta tsakatsaka}. A hadisi na 1737 cikin Buhari Abdullahi Dan Abbas ya ce: Ka dubi duk abin da yake na saja’i ne cikin addu’a ka guje masa, saboda ni na lura da cewa wannan shi ne abin da manzon Allah da sahabbansa suke yi)).

Na hudu: Sa ikhlaasi da nuna tsoron Allah cikin addu’ar, da kuma nuna sakankancewar cewa lalle Allah Mai karban addu’ar bayinsa ne. Tirmizi ya ruwaito hadisi na 3479, da Ahmad hadisi na 6617 da Hakim hadisi na 1817 da isnadi mai kyau daga Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah mai tsira da mincin Allah ya ce: ((Ku roki Allah kuna masu sakankancewar samun ijaba, ku sani lalle Allah ba ya amsa addu’a daga zuciyar gafalalle rabkananne)). Bukhari ya ruwaito hadisi na 6338 daga Anas Dan Malik ya ce Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Idan dayanku zai yi addu’a to ya yi ta da karfin guiwa kada ya ce: Ya Allah in Ka so Ka ba ni; saboda babu mai iya tilasta Shi)).

Na biyar: Ya nuna naciya cikin addu’arsa, sannan kada ya nuna cewa me ya sa har yanzu ba a biya masa bukatarsa ba? Bukhari ya ruwaito hadisi na 6340, da Muslim hadisi na 2735 daga Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah mai tsira da mincin Allah ya ce: ((Za a amsa wa dayanku addu’a matukar dai bai nuna gaggawa ba, a inda zai rika cewa: Na yi addu’a amma ba a amsa mini ba)).

Na shida: Ya bude addu’arsa ya kuma rufe ta da ambaton Allah, da kuma yi wa Annabi salati, daga nan sai ya gabatar da addu’arsa. Bukhari ya ruwaito hadisi na 1130, da Muslim hadisi na 769 daga Abdullahi Dan Abbas ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance in ya tashi sallar dare yana cewa: Ya Allah godiya ta tabbata gare Ka, Kai ne hasken Sammai da Kasa, godiya ta tabbata gare Ka Kai ne madogarar Sammai da Kasa, godiya ta tabbata gare Ka Kai ne Ubangijin Sammai da Kasa da abin da yake cikinsu, Kai ne gaskiya, alkawarinKa gaskiya ne, zancenKa gaskiya ne, gamuwa da Kai gaskiya ne, Aljannah gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Sa’ah gaskiya ce. Ya Allah gare Ka na mika wuya, da Kai na yi imani da tawakkali, zuwa gare Ka na koma, saboda Kai nake husuma, wurinKa nake kai kara. Ka gafarta mini abin da na gabatar da abin da na jinkirta, da abin da na boye da abin da na bayyana. Kai ne Abin bautana, babu Abin bauta bisa cancanta sai Kai)). Tirmizi ya ruwaito hadisi na 486 da isnadi mai kyau cewa Umar Dan Khattab ya ce: ((Lalle addu’a a dakace take tsakanin Sama da Kasa babu abin da ke kaiwa sama daga cikinta har sai ka yi salati ga annabinka tukun)).

Na bakwai: Tuba daga ayyukan zunubi, da kuma maida dukkan wani kayan zalunci da ke hannunka, da kuma takaituwa da cin halal. Muslim ya ruwaito hadisi na1015 daga Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Alkah ya ambaci labarin wani mutum da yake tsawaita tafiya gashi a cike da kura yana mika hannayensa zuwa sama yana cewa: Ya Ubangiji, Ya Ubangiji! Alhali abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufarsa haramun ce, kuma da haramun aka ciyar da shi, ta kaka za a amsa wa wannan)).

Ya Allah! Muna rokon Ka, Ka amsa mana addu’o’inmu, Ka dawo mana da zaman lafiya cikin kasarmu, Ka kyautata mana shugabanninmu, Ka sa albarkarKa ta game dukkan al’ummarmu.
عباد الله! ان الله يامر بالعدل والاحسان وايتاء ذي القربى وينهى عن الفحشاء والمنكر والبغي يعظكم لعلكم تذكرون. اقول قولي هذا واستغفر الله لي ولكم.

SHARE
Previous articleDUTSEN UHUD!
Next articleKUKAN KURCIYA:

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY