Watarana Babban Sufin Nan Sheikh Ibrahim Adham(R.A) Yana Tafiya Cikin Kasuwar Birnin Basrah, Sai Mutane Suka Yi Gungu Suka Same Shi Suka Ce:-
“Ya Abu-Ishaq! ALLAH Madaukakin Sarki Ya Fada Mana a Cikin Littafinsa Mai Tsarki Cewa:’KU ROQE NI ZAN AMSA MUKU’ Amma Mun Roqe SHI Na Tsawon Lokaci Amma Bai Amsa Mana Ba???”.
Sai Ibrahim Adham(R.A) Ya Ce:-
“Yaku Mutanen Basrah! Zuciyoyinku Sunyi Tsatsa Sun Mutu Akan Abubuwa Goma:-
*1. Kun San ALLAH Amma Kunqi Ku Bashi Haqqinsa.
*2. Kullum Kuna Karanta Al’Qur’ani Amma Bakwa Aiki Da Koyarwarsa.
*3. Kuna Ikrarin Ku Masoya Manzon ALLAH(S.A.W) Ne Amma Kun Bar Koyi Da SHI(S.A.W).
*4. Kuna Ikrarin Ku Maqiyan Shaytan Ne Amma Kullum Kuna Kyautata Hanyarsa.
*5. Kun Ce Kuna Son Aljanna, Amma Bakwa Aiki Don Shiga Aljannar.
*6. Kun Ce Kuna Tsoron Wuta Amma Kullum Kuna Kusantar Da Kanku Da Wutar, Ta Hanyar Aikata Zunubai.
*7. Kunce Mutuwa Gaskiya Ce, Amma Har Yanzu Banga Kuna Shirya Mata Ba.
*8. Kun Shagaltar Da Kanku Wajen Hango Laifukan Wasu, Kun Manta Da Naku.
*9. Kullum Kuna Cikin ‘Kwankwadar Ni’imomin Da ALLAH Yayi Muku, Amma Baku Gode Masa.
*10. Kullum Kuna Binne/Suturar Mamatanku, Amma Baku Daukar Wani Darasi Daga Gare Su.
(Don Karin Bayani a Duba: Abu Nu’aym, Hilyah Al-Awliyaa’ 8:15, 16),
Comment:Jazakumullahu bikhair