Ana Shirya Wa Musulmi Makarkashiya A Kasar Nan – Sheik Bala Lau

A ranar lahadin ne shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya tattauna da manema labarai, a yayin taron wa’azin kasa daKunigiyar Izala ta gudanar a garin Mashi da ke jihar Katsina, ciki har da wakilin RARIYA a Katsina, inda ya bayyana makasudin yin wannan wa’azi na karamar hukumar Mashi da bayyana rashin jin dadin kungiya ta kasa na irin kashe-kashe da ke faruwa a kasar nan musamman a Arewa inda ya ce kungiyar ba za ta lamunta ba, kuma asali ma ana son rage al’ummar Musulmi a kasar ne, saboda wata makarkashiya da ake shiryawa. Ga yadda hirar ta kasance tare da Sheikh Abdullahi Bala
Babu shakka sakon da muke tafe da shi a wannan wa’azi na kasa wanda za a gudanar da shi a garin Mashi ta jihar Katsina shine kira ga al’ummar Musulmi wajen kadaita Allah, domin Allah ya hallice mu don mu bauta masa kuma shine jagora kan zaman lafiya. Na biyu, bayan mun ja hankali al’umma kan kadaita Allah, hada kan al’ummar Musulmi su zama al’umma guda kamar yadda Ubangiji ya fada cikin alkurani.
Ana barna a kasa da kashe-kashe amma shugabanni babu ruwansu, Nijeriya ta samu kanta cikin mawuyacin hali, muna da bukatar tuba ga Allah. Allah ya jarrabe mu da jarraba wa iri iri tun daga shugabanni, tallakawa wadanda ake mulka, malamai da mu koma zuwa ga Allah, mu dauka wannan jarraba wa ce daga Allah, mu kuma yawaita Istigifari da tuba zuwa ga Allah, zai ba mu mafita.
Ya ci gaba da cewa “hakika kashe-kashe a kasar nan ya yi yawa, yana daga cikin hakkoki na shugabanni ya tsare rayukan al’umma da dukiyar al’ummarsa da addinin su kuma muddin aka rasa wannan an samu babbar matsala.
Don haka halin da muka tsinci kanmu akwai tabarbarewar tsaro kuma akwai nuna gazawa ga ainihin shugabanni, kafin wannan lokaci Arewa na zaune lafiya saboda da shugabanci ake gyara komai.
Rashin tsaro da ya kadaddabe kasar nan musamman Arewa, wannan kungiya JIBWIS ta damu matuka kuma yana nuna kasa wa daga gwamnatin tarayya ko ana nufi kowa ya tashi ya kare kansa saboda gwamnati ta gaza?
Lau ya kara da cewa “abin bakin ciki ne a ce ‘ya’yanmu ‘yan makaranta da aka sace a Chibok ka kaddara ‘yarka ce aka kama. Idan Amurka da Isra’ila za su yi yaki kan kama mutum guda, rayuka nawa aka kashe a cikin wata guda zuwa yanzu?
Mun fahimci cewa akwai wani makirci ko zagon kasa idan muka kalli maganar da tsohan shugaban kasa ya yi a wasikarsa, inda ya ce akwai shirye shirye na kashe-kashe da zub da jini a kasar nan da za a yi.
Kafin ya fada ba a taba kashe mutum daya a Katsina, zamfara, Adamawa ko Taraba ba, amma bayan wannan magana ta shi, an kashe mana Sheikh Albani Zaria. A Katsina kawai an kashe mutum sama da dari, yanzu an kai hari a Abuja kuma babu wani mataki da gwamnati ta dauka kuma a matsayinsa na tsohon shugaban kasa kenan. Gaskiya tunda ga abubuwan da ke faruwa, mu al’ummar Musulmi mun dauki wannan magana gaskiya ne, wannan shiri don a kashe al’ummar Musulmi.
Kiristocin Nijeriya da shugaban CAN, duk lokacin da wani abu ya faru sai sun fito sun yi magana domin nuna ana kashe mutanensu da ba su yarda ba. Amma tunda ga wancan lokacin da suka gane Musulmai ake kashewa, babu wanda ya kara magana a cikinsu.
Saboda haka wannnan ya nuna wani zagon kasa ne ake yi wa Musulman kasar nan don a rage su.
Haka kuma ana kokarin a hada kabilun Hausa da Fulani fada a Arewacin Nijeria wanda tun da Allah ya zaunar da Nijeriya lafiya. Amma bari a jefo mana fitinar da za a ce Hausawa da Fulani suna fada, wannann shiri ne na musamman domin a tabbarbara tattalin arzikin Arewa ko kuma a kashemu.
Haka Tib da Fulani abokan wasa ne, su ma ana son hada fada tsakaninsu, duk inda aka kai hari sai a ce Fulani ne suka kawo hari ana son a ce Musulmai ne suka kawo hari.
An tashi da cewa Boko Haram domin an gono cewa Boko Haram ya rikide zuwa hanya ce ta kashe wanda ake so a kashe”.
Daga karshe ya yi kira da babba murya cewa “wannan kashe-kashe ba mu yadda da da shi ba kuma ana cutar da mu, kuma muna jaje ga al’ummar Musulmi kan harin Abuja kuma lalle ne gwamnati ta dauki mataki.
A kwanakin baya an kashe Malam Albani, ana da niyyar kashe kashen Malamai da Sarakuna nan gaba. Ba ni na fada ba, tsohon shugaban kasa ya fada. Muna son gwamnatin tarayya ta nemi shi domin ya yi bayani.
Kwanakin baya an kama wadanda suka kashe Sheikh Albani Zaria, muna jira mu ga an kai su kotu, har yanzu shiru ba mu san yadda aka yi ba. Mu ba za mu yi shiru ba, muna son mu ji me ke faruwa, idan ba haka ana nuna mana mu tashi mu kare kanmu. Yanzu haka ana ci gaba da tsare ‘ya’yanmu mata ‘yan makaranta. Da ‘ya’yan Kiristoci ne, watakila da yanzu duniya ta tashi tsaye kan sai an fito da su. Lalle muna son a dau mataki kuma a yi mana adalci.
Haka kuma wannan taron kasa ba shi ya kamata a yi ba a wannan lokaci, kamata ya yi a ce ana taron gano hanyar magance matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.
Kuma ina kira ga Musulmai a ci gaba da yin addu’a duk wanda ke da hannu a cikin wannan makarkashiya da ake wa Arewa Allah ya tona asirinsa.
Haka kuma mu al’umma Musulmi a wannan taron kasa da ake yi, ba a yi mana adalci ba a wajen zakulo membobi ba, a ce Kiristoci sun fi Musulmai yawa a wannan taron duk da Musulmi sun fi Kirista yawa a Nijeriya.
Daga karshe ya yi kira ga manya ‘yan Arewa da masu rike da mukamai na wannan gwamnati da su tashi tsaye don ganin an kawo karshen wannan kashe kashe da ke faruwa a Arewa.
Shi ma a lokacin da yake na shi jawabin, shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a na jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan (Sautis Sunna) ya jawo hankulan al’ummar Musulmi kan bin tafarkin Sunnah da kuma kauce wa bidi’a komin kankantarta. Haka kuma ya jaddada kiran ga Musulmai duk inda suka samu kansu su ji tsoran Allah, kuma su tabbatar da cewa mutuwa fa za ta iya riskar su da zaran lokaci ya yi. Kuma a ci gaba da yin addu’a domin samu dawwamammen zaman lafiya a kasar nan, kuma ita ma gwamantin tarayya ta tshi tsaye don kawo karshen tashe-tashen hankula da ke faruwa a Arewa.
Yakubu Musa ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da gwamnan Shema kan mawuyacin hali da masu karbar fansho suke a matakai daban daban, saboda sabon tsarin da gwamnatin ta shigo da shi wanda har yanzu wasu ba su karba, don haka ya kamata gwamnati ta duba wannan al’amari da idon basira.
Da yake jawabi shugaban majalisar dokoki ta jihar Katsina, Yau Umar Gwajo-Gwajo wanda kuma shi ya wakilci gwamnan Katsina, ya nuna jin dadinsa da kungiyar Izala da ta kawo wannan wa’azi na kasa a jihar Katsina da kuma karamar hukumar Mashi, kuma ya yi wa kowa fatan alheri Allah maida kowa gidan sa lafiya

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY