Tsarin Shugabancin Kungiya

TSARIN SHUGABANCI, MANUFOFI DA KUMA DOKOKI, NA JAMA’ATU IZALATIL BID’AH WA’IKAMATIS SUNNAH

SASHI NA FARKO (1)

SUNAN KUNGIYA

1.   Takamaiman sunan wannan kungiya JAMA’ATU IZALATIL BID’AH WA’IKAMATIS SUNNAH

 1. Ma’ana:- Kawar da Bidi’a daga addinin musulunci da kuma kafa sunnah ta Annabi Muhammad (SAW).
 2. Wannan Kungiya ta musulunci ce, wacce musulmi suka kafa kuma tana da hedkwata a Jos, Jihar Pilato, Kungiyar bata da alaka ko wace iri ce, da wata kungiyar asiri, darika ko kuma kungiyar Siyasa.
 3. Don dacewa, kungiyar na da Rassa a Jihohi da kananan Hukumomi a fadin tarayya Karkashin wadannan Sharruda.
  1. Jihohi bayan zaben Shugabanninsu su aika ma hedikwatar kasa don amincewa.
  2. Wajibi ne ga dukkanin Shugabannin Jihohi dasu halarci taron Jihohinsu ko kuma na kasa a duk lokacin da aka gayyacesu.
  3. Wajibi ne duk Shugaban Jiha ya aika wa Shugaba nakasa da bayanin ayyukanshi bayan duk Wata Uku (3).
  4. Shugaban Jiha bashi da damar hana wani mai wa’azi ko dan agaji halartar wani wa’azi da aka shirya bisa ka’ida tare da kuma yardar kungiya. Duk da haka, mai wa’azi ko dan agaji ya sanar da Shugabanni wurin da yake.
  5. Gaba daya an yarda cewa babu wata jiha da zata shirya wa’azi a dai dai lokacin Wa’azin Kasa, saboda haka, idan jiha nason yin wa’azi sai Ta sanar da Hedkwatar kasa don kar asmi karo.

Wannan kungiya tana kan tafarkin musulunci ne wanda ta dogara ga Qur’ani da hadisan Annabi Muhammad (SAW) Bisa fassarar Magabata. Babu bambanci a cikin kungiya in dai har mutum musulmine da yayi Imani da ‘Allah’ kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya karantar. Kungiya na maraba da irin wannan mutum da kuma shawarwarinsa masu amfani wadanda suka dace da musulunci.