Dalilan Kafa Kungiya

SASHI NA BIYU (2)

MANUFA DA DALILAN KAFA WANNAN KUNGIYA

A.  Hada kan musulmi kamar yadda Allah ya fadi a cikin Al-qur’ani “Kuma kuyi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba”. Kuma Annabi Muhammad (SAW) yace “Musulmai daya ne, kuma basu rabuwa (Sashi na Karfafa Sashi)”

B.  Wayar da kan mutane kan ayyukan wasu dake kiran kansu musulmi, wadanda basa tafarkin Manzon Allah.
C.   A sanar da dukkan musulmi don suyi hankali da littafai da wasu miyagun malamai suka rubuta don kaworudani a cikin musulunci.
D.    A nuna wa musulmi cewa: Annabi Muhammad (SAW) Kafin rasuwarsa ya kammala Isar da sakon da Allah ya bashi.
E.  A sanar da musulmi cewa duk wanda yayi Da’awar Annabta ko Annabi Muhammad (SAW) Yana ziyartarshi a daukeshi a matsayin makaryaci.

Wannan na nuna cewa Annabi naraye kenan alhali Allah ya fadi cikin Al-Qur’ani cewa “Hakika kai zaka mutu, (wata rana) haka nan suma zasu mutu (wata rana)” Kuma Annabin ya tabbatar cewa zai mutu kuma yamutu.

Khalifa Abubakar bayan rauswar Annabi yafito yace “Duk wanda ya kasance yana bautawa Muhammadu, To, Muhammadu Yamutu, amma wanda ya kasance yana bautawa Allah ne, To Allah rayayyene baya mutuwa.”

SASHI NA UKU (3)

DALILAN KAFA KUNGIYA

Dukkan dalilan kafa wannan kungiya an samo sune daga cikin Al-Qur’ani Mai Girma da kuma Hadisan Annabi Muhammad (SAW) don Karin bayani, hujjoji an tsakuro sune daga cikin Qur’ani da Hadisi.
Don yada musulunci, Allah ya fadi a cikin Al-Qur’ani: “Kuma wata Jama’a daga cikinku, su kasance suna kira ga Alkhairi kuma suna Umarni da aikhairi kuma suna Hani daga abinda ake ki kuma wayannan sune masu cin nasara.”
A cikin hadisin Annabi Muhammad (SAW) akwai wurare da dama daya Umarci Sahabbansa su “Isar da wannan sakoga wa’yanda zasu zo bayansa.”
A cikin wani Hadisi Annabi Muhammad (SAW) Yace “Duk wanda yaga wani abinki daga cikinku, ya can zashi da Hannunsa, in bazai iya ba, da Harshensa, in bazai iya ba, To yakishi a zuciyarsa, wannan shine mafi raunin Imani.
Allah Madaukakin Sarki Yace “Lallai ne wadanda ke boyewar abinda Allah ya saukar daga hujjoji bayyananu, da shiriya, bayan munbayyana shiga mutane a cikin littafi (Al-Qur’ani) wadannan Allah yana La’antarsu kuma masu La’ana suna la’antarsu.”

SASHI NA HUDU (4)

Wajibi nega dukkan dan kungiya ya kare mutuncin kungiya da kuma yancin kasa a duk inda yake a kuma dukkan halin dayake, Indai har yin hakan bai sabawa tafarkin Allah da Manzonsaba. Hakanan duk wani dan kungiya ya zama mai bin doka koda an kulubalanceshi don karya doka, ko tada hankali, ya lura da cewa hakuri shine abu mafi muhimmanci. ‘Allah’ a cikin Qur’ani Yace, “Kuma bayin mai Rahama sune wadanda ke yin tafiya a kan kasa da sauki, kuma idan jahilai sunyi musu Magana, sai suce “Salama” (a zauna lafiya).”
Kafin, ko bayan zama dan kungiya, mutum zai iya bada sadaka ko kyauta ga kungiya don tafiyar da ayyukanta. Dalilin haka shine ‘Allah’ yafadi cikin Al-Qur’ani “Ku fita da yaki kuna masu saukakan kaya da masu nauyi, kuma kuyi Jihadi da Dukiyoyinku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alheri agareku. Idan kun kasance kuna sani.”