Dangantakar Kungiya da Sauran Kungiyoyi

SASHI NA BIYAR (5)

DANGANTAKAR KUNGIYA DA SAURAN KUNGIYOYI

  1. Wannan kungiya tana tare da kowace kungiya, matukar ta dace da dokokin musulunci (Qur’ani da Hadisi da Ijima’in Malamai).
  2. Wannan kungiya na mai farin cikin taga cewa kungiyoyin musulunci suna zaman lafiya da juna, aiki tare don cimma buri daya da kuma tsayawa gaba daya bias Al-Qur’ani mai girma da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) don cigaban addinin mu. ‘Allah’ Madaukakin Sarki a cikin Qur’ani Yace, “Muminai Maza da Muminai Mata, Sashinsu na Taimakon Sashi, Suna Umurni da Kyawa’wan aiyuka Kuma suna Hani da Munanan aiyuka Kuma Suna tsaida Sallah.  Suna bada Zakka, kuma suna yin Da’a ga ‘Allah’ da Manzonsa. A garesu ne Allah Zai saukar da Rahamarsa.”

SASHI NA SHIDA (6)

BANGARE NA DAYA SHUGABANCIN KUNGIYA

  1. Tafiyar da wannan kungiya na wuyan dattawan shugabanni wadanda kugiya tazaba. Shugabanni na karkashin Tilon Shugaba da aka zaba, saboda Annabi Muhammad (SAW) Yace, “Idan musulmi Uku (3) suka hadu, Su zabi daya ya Shugabancesu.”

Akwai majalisu wanda aikinsu ne su shirya taro don cimma matsaya guda biasa cigaban wannan kungiya.