Bangaren Majalisu

BANGARE NA BIYU MAJALISU

SUNE:

 • Majalisar Zartaswa
 • Majalisar Magabata
 • Majalisar Iyayen kungiya
 • Majalisar Masu Wa’azi
 • Majalisar Sadarwa da Watsa Labarai
 • Kwamitin Tafiyar da Aiyuka
 • Majalisar Al’amuran Shari’a
 • Majalisar Al’amuran Ilimi
 • Majalisar Al’amuran Kudi
 • Majalisar Binciken Kudi

 1.   MAJALISAR ZARTASWA

Ta hada da shugaba wanda zai Shugabanci zaman Majalisar

Akwai sakatare na Majalisar

Akwai sakatare da mataimakansu ga dukkan kwamiti

Akwai zababbun wakilai.

Gaba dayan Majalisar ta kunshi mutum Ashirin da Biyar (25) wanda ya nuna cewa mutum Biyar (5) za a iya samun mutanen da suka cancanci zama kuma su yanke shawara a gaban shida daga cikin yan majalisar kamar yadda musulunci ya bayyana.

2.   MAJALISAR IYAYEN KUNGIYA

Zasu nemi shawarar majalisar magabata kan zaman lafiya da cigaban wannan kungiya. Zasu sanya Ido akan dukkan majalisun kwamiti. Wajibine ga dukkansu girmama aiki, da kuma su yan majalisar Iyayen kungiya in har aikinsu akan ra’ayin musulunci ne, ‘Allah’ a cikin Al-Qur’ani Mai Girma Yace, “yaku wadanda su kayi Imani, kuyi da’a ga ‘Allah’, kuyi da’a ga Manzonsa da Ulul’amri mikum. Idan kunyi Sabani cikin wani abu, ku dawo dashi ga ‘Allah’ da manzonsa.

Kuma Annabi Muhammad (SAW) Yace, “Yaku mutane, kuji tsoro ‘Allah’ ko da Bakin Bawan Habasha yake Mulkinku. Kusaurareshi kuyi masa biyayya in har Umurninsa sun dace da Littafin ‘Allah’.

3.   KWAMITIN TAFIYAR DA AYYUKA

Shugaba da sakataren wannan kwamitin zasu kasance a karkashin babban sakatare wannan kungiya zasuyi aiki, Tare da juna. Aiyukan Sune kamar Haka:

 • Suyi tanadi da shirya wa’azi a duk lokacin da majalisar zartaswa tabada Izini wannan Wa’azi.
 • Su shirya taron musulunci da kuma karawa Junasani a madadin kungiyar.
 • Su taimaki Shugaban Malamai wajen shirin zaben wanda suka cancanci sugabatar da wa’azi da kuma wadan da zasuyi wa mutane Magana a ko wane lokaci
 • Shugaban wannan kwamitin shine shugaban, kwamitin Shirye-Shirye. Kuma shine zai bada dama ga kwamitin zartaswa in akwai bukatar Wa’azi.

Mataimakin sakataren shirye-Shirye (Aiyuka). Shi zai taimaki sakatare, kuma yayi aikin shi (sakatare) Idan baya nan ko kuma bias umarnisa.

4.   MAJALISAR WA’AZI

Wannan majalisar tana karkashin shugabancin, Shugaban masu Wa’azi, Na wannan kungiya. Aikin wannan kungiya ne taga cewa dukkanin masu Wa’azi da wannan kungiyar ta shimfida. Shine wa’azi da Al-Qur’ani da kuma Hadisan Annabi Muhammad (SAW) da kuma Littattafan koyarwar Musulunci.

Aikin wannan majalisar taga cewa a duk inda za’ayi wa’azi mutanen wannan waje, sun sanar da hukuma (Ba neman Izini ba) domin akwai wannan dama acikin Tsarin mulkin Nageria na 1997, Kashi na Hudu (4) sashi na Talatin da daya (31) karamin sashi na Daya zuwa na Uku (1-3).

Kuma su sanar da duk wadanda abin yashafa don a kaucewa duk wata damuwa a lokacin wa’azi ko a bayanshi.

Majalisar masu wa’azi suneke da hakin yin rijista ga duk wani mai wa’azi da kuma bashi dama da zata nuna cancantarsa nayin wa’azi ga Jama’a.

5.   MAJALISAR SADARWA DA WATSA LABARAI

Tana karkashin shugabancin watsa labarai. Aikintane ta sadar da dangantaka tsakanin wannan kungiya da wasu, a karkashin dokokin kungiyar da aka fadi a sama. Aikintane taga cewa wannan kungiya da wasu nada fahimtar juna batare da wani rashin fahimtaba.

Babban aikin wannan majalisar shine yada aiyukan wannan kungiya ta hanyar Rediyo. Jarida da kuma Sanarwa, Aikintane kuma ta maida martini ga duk wani bayani marastaushi da aka danganta ga wannan kungiyar.

6.   MAJALISAR AL-AMURAN SHARI’A

Wannan majalisa tana karkashin Shugabancin Babban Uban kungiya.

Sakataren wannan majalisa zai zama kwararrene kan harkokin Shari’a wanda ya yarda ya tsayama kungiya ko bata shawarwari bisa kan al-amuran Shari’a.

Majalisar ce zatayi caraf ga duk wani wanda yayi kokarin bata mata suna ko zubar mata da mutuncinta Zata gabatar dashi ga hukumar data dace.

Majalisar zata kare duk wani abu daya shafi al-amuran Shari’a a halin da aka kai karan kungiya a Kotu.

Aikin tane har yau takare duk wani dan kungiya kan al’amuran Shari’a ko kuma wani abu daya shafi kungiya batareda aikatawani laifiba.

Saboda muhimmancin wannan majalisar, za’a dinga taimakamata a duk lokacin da bukatar hakan ta’taso.

7.    MAJALISAR AL-AMURAN ILIMI

Wannan majalisar zata kasance karkashin shugabancin dan kungiya wanda yake kwararrene akan addini. Sakataren wannan majalisa shine babban sakataren wannan kungiya da mataimakinsa, Aikin wannan majalisar ne suwayarwa da jama’a kai akan bukatar Ilimin addini dana zamani a kasa bakidaya.

Majalisar zata kafa wata majalisa ta musamman wanda aikinta shine lura da kulawa dasa ido akan makarantun kungiya baki dayansu. Kuma Majalisar zata tabatar cewa yara da manya sun amfana daga tsarin koyarwarta daga aikinta nakoyar da cikakken karatu mai amfani akan mizanin Shari’a.

KOYAR DA MATAN AURE

Wannan majalisar zata jawo hankalin maza kan koyar da matansu.

Masu wa’azi zasu dinga shirya kaset-kaset na musamman don Ilmantar da matan Aure akan Ilimin musulunci tahanyar makarantun matan Aure.

Dayardar ‘Allah’ Nan kusa idan akasami mata masu Ilimin addini, zasu dinga koyarda matan Aure aiyukan ibada da taimakon addinin ‘Allah’. Insha Allahu.

8.   MAJALISAR KUDI

Tana karkashin shugabancin ma’ajin kungiya. Aikin majalisar ne ta kirkiro hanyar samin kudi don tafiya da kungiyar. Ga misali tahanyar buga Littattafai, Kaset, Jaridu da kungiyar, takeyi har izuwa bude shagon sayarda littattafai indai harbai sabawa dokokin ‘Allah’ da Manzonsa ba.

Suna kuma da dama su karbi taimako bayan yarda majalisar zartaswa da kuma hukuma ta sanar, “Babu wata kungiya ko tarin jama’a da zai kadamarwa da asusun neman taimako ko kayan aiki daga mutane ta hanyar kafafen yada labarai ba tare da yardarta ba”.

Saboda haka tilas ne wannan kungiya ta hada kai da hukuma kafin kadamar da wannan asusun neman taimako.

Ba wata jama’a da zata kadamarwa da asusun neman taimako ga kungiya ba tare da yardar wanan majalisa ba in dai har wannan neman taimakon ya kai a yarda dashi ko bugashi a kafafen watsa labarai.

Ba’a yarda wani yafitar da wani abu ba, day a shafi kungiya kamar jarida bayanai, baje da sauransu, sai dai izinin wannan majalisa.

Ba’a yarda wani ya saida wani abu ba, ta cikin lasifika ko yayi tallan wani abu a wajen wa’azi ba.

Idan aka sami wani mutum ko wasu jama’a da aikata wani daga cikin abubuwan da aka lissafa a sama, za’a mika su ga majalisar Al-amuran shari’a don tambayoyi kafin daukar wani mataki akansu.

TAFIYAR DA KUDIN KUNGIYA

Da yardar ‘Allah’ wannan kungiyar zata dinga tafiya da abinda take dashi kan yada musulunci. Shugaban na kasa, ma’ajin kungiya da sakataren kudi suneke da dammar fitar da kudin kungiya.

9.   MAJALISAR BINCIKEN KUDI

Mutum biyar ne zasu shugabanta, Sune:- Babban mai binciken kudi da mataimakinsa, Sakataren watsa labarai a matsayin sakataren majalisar biyu. Aikin wannan majalisar ta binciki yadda aka kasha kudin kungiya. Ana iya kafa kwamitin na musamman idan da bukatar hakan.