Shugabancin Kungiya

SHUGABANCIN KUNGIYA

Shugabanin wannan kungiya. Babu tilas su kasance. Mutanen kirki kuma amintattu, wato wadanda zasu kaucewa aiyukan ash’sha da kuma na zubar da mutunci.

Dole shugabanni su zama yan kungiya. Babu tilastawa kan shugabanci. Mutum zai iya sauka dag agama yin zabe ko kuma ya bada notis na kwana Goma (10) ko wani shugaban yana da mataimaki mai taimaka masa wajen tafiyar da aiyukan kauna ga dukkan wani shugaban in dai har hakan zai kawo zabe kamar canja da kuma zabe kamar jam’iyar siyasa. Tarihin musulunci ya nuna cewa Manzon ‘Allah’ (SAW) Yana canja shugabannin rundunonin yaki akai akai saboda kowa ya samu dama ya nuna jaruntakarsa.

Duk wanda kungiya ta zaba ya zama shugaban dole ne duk wani dan kungiya yabi duk wani umurni da shugaban ya zartas in dai har wannan umurni bai sabawa dokokin ‘Allah’ dana kasa ba in wannan umurni da aka zartas bai yima wani dan kungiya dadiba, yana iya rubuta kukansa ga kungiya danta binciki wannan umurni da aka zartas. Za’a kafa kwamitin don wannan aiki hukuncin wannan kwamitin dole ne mai kuka da shigaba su karbeshi.

JAGORANCIN WANNAN KUNGIYA

SUNE KAMAR HAKA:-

 • Shugaba
 • Mataimakin Shugaba Na daya (I)
 • Mataimakin Shugaba Na biyu (II)
 • Sakatare
 • Mataimakin Sakatare Na daya (I)
 • Mataimakin Sakatare Na biyu (II)
 • Mai Binciken Kudi
 • Mataimakin Mai Biciken Kudi
 • Ma’aji
 • Sakataren Kudi
 • Mataimakin Sakataren Kudi
 • Sakataren Watsa Labarai
 • Mataimakin Sakataren Watsa Labarai
 • Sakataren Aiyuka
 • Mataimakin Sakataren Aiyuka
 • Shugaban Masu Wa’azi
 • Mataimakin Shugaban Masu Wa’azi

KUNGIYAR YAN’AGAJI

Wannan kungiya nada yan’agaji. Suna da kayan aiki mai rowan kasa da baje mai takubba biyu dabino a tsakiya. Suna da shudin hula da farin takalmi. Wannan kungiyar Yan’agaji nada hedkwata a Bukuru. Suna da shugabansu na kasa, yankin jiha, bagare da kuma na rassa. Duk da cewa suna da dokokin su, amma suna karkashin shugaban kungiya. Wannan kungiyar Yan’agaji bata sabawa sauran kungiyoyin Agaji na duniya ba wurin da ake aikatawa ash’sha ba ‘Allah’ Yace cikin Al-Qur’ani Mai Girma kada ku taimaka akan sabo da gaba.

KARFIN KUNGIYAR YAN’AGAJI

Yan’agaji nada dammar zaben shugaban sune kawai shugaban da sakataren sune zasu zabi ma’aji shugaban yana karkashin uwar kungiya ne domin lura da ladabtarwa.

JAWABIN RUFEWA

Wannan kungiya na kira ga musulmi baki daya dasu hada kai kamar yadda ‘Allah’ (SWT) Ya fadi a cikin Al-Qur’ani Mai Girma cewa musulmi karsu rasa addininsu (riki koyarwar Al-Qur’ani da kuma Hadisan Annabi).

Muna kira ga kungiyar suyi kokari su tsayar da dokokin ‘Allah’ maimakon shirya dokokin wadanda ke jan zuwa rikici da rashin hadin kai. ‘Allah’ ya taimakemu Amin.

Muna tabatarwa ga musulumi dake duniya cewa wannan kungiya an kafatane domin wayar da kan mutane ta hanyar yin wa’azi da gina matarantu. Ita ba kungiyar siyasa bace kuma bata asiri bace kuma ita ba wata darika bace. Ita dai cikakkiyar kungiya musulunci ce kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) Ya kawo.

Babu tilas tawa ga zama dan kungiya kamar yadda aka riga aka bayyana.

Wannan kungiya bata yan kama-karya bace. Bata kutsa kai cikin harkokin tafiya da gwamnati ko kuma wata matsala cikin wacce akwai yan wannan kungiya (wannan na nufin cewa wannan kungiya bata da dammar hana hukuma yin kasarta wanda yake kuma dan wannan kungiya ne kuma an same shida laifin aikata wani laifi).

Duk wani ke bin Al-Qur’ani sauda-kafa kuma ya’yarda dashi, Hadisan Annabi Muhammad (SAW) da kuma fassarar Malaman Kwarai to ba wata tantama dan wannan kungiya ne. Mutum kuma mai sauraren wa’azi wannan kungiya shima ya taimaka kungiya bata da wani kati ko wani rubutu da zai tilasta mutum yin rijista. Dan kungiya nada dammar ya bada shawarwarin ga ko wani mutum da za’a bama shawarwari yake (rika dashi) in har shawarar data dace da musulunci.

‘Allah’ ya taimaki dukkan Musulmi a duk inda suke.

‘Allah’ yahada kansu gaba daya Amin summa Amin.