AHLUSSUNNAH SUKE CI GABA A DUNIYAR MUSULMAI.

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta Kasa Tana Nuna Farin Cikinta a Fili Ganin Yadda Allah Ya Sanya Daya Daga Cikin ‘ya’yanta Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo yake Karantar da Sunnah a Cikin Masallacin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Wannan babbar Nasara ce a Tafiyar Sunnah, In baku Manta ba a Bara ne Hukumar Saudiyya ta baiwa Malaman Sunnah na Nigeria Karkashin Kungiyar Izala Shaidar Cewa Su Shiga Ko Wane Lungu a Birnin Makkah dan yin Wa’azin Musulunci.

Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo Mutumin Kano ne, Kuma Yana Daya Daga Cikin Masu Tsare Tsaren Seminar ta Kungiyar Jibwis a Nigeria, a Bara Yana Daya Daga Cikin Wadanda Suka Tara Dalibai da Suke Karatu a Jami’oi na Duniya Kusan Dubu Daya Wanda akayi a Sokoto.

Da Muka Tambayi Shugaban Kungiyar ta Kasa Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau game da Wannan Nasara da aka Samu na Karantar da Sunnah da Harshen Hausa a Masallacin Annabi Tsira da Aminci a gare shi, Sai Shugaban Yace, Wannan abin farin ciki ne, kuma daya ne daga cikin nasarorin da Kungiyar Izala take Samu a Kasar Saidiyya, yace Malaman Sunnah ta Saudi ta gamsu da karantarwan Izala, ta kuma gano izala abokiyar aiki ne, yace kuma nan gaba kadan akwai wasu nasarorin da za’a samu, wanda in an samu kowa zai gani kuma zaiyi farin ciki, Shugaban yace Kungiyar ta Izala ta shirya wa’azozi da za’a gabatar bana a nan garin Makkah, Wanda a bara an gabatar da irin sa, wanda har Ambassador na Nigeria dake kasar Saudi Arabia ya yaba da wannan kokari kuma ya nemi na bana yafi na bara, Shugaban Yace akwai Shirin da akeyi wanda za’a hada karfi da karfe da ‘ya’yan Kungiyar ta Izala dake Jami’ar Madina dan zuwa Gidajen Mahajjata da suke Madina ayi musu Wa’azi, a karantar dasu Hakikanin Aikin Hajji yadda yake a Sunnah.

Daga Karshe Shugaban ya yabawa Dalibai Yan Makarantar ta Madina kuma Wakilan Izala anan birin Madina da Daliban mu na Al’Azhar dake Egypt, da daliban mu na Malaysia da Sudan da Sauran Jami’oin mu na kasashen Duniya, Musamman yadda Suka bada Hadin kai wurin Tasowa takanas ta Kano dan gabatar da tafsirin azumin daya gabata, da kuma irin kokarin da suke badawa wurin karfafa tashar Sunna TV, Allah ya saka ma kowa da alkhairi.

Muna addu’an Allah ya taimaki duk mai taimakon Addininsa, ya hada Zukatan Musulmi akan Kitabu Wassunnah, ya kori Sheidan a tsakanin mu, ya bamu nasara duniya da Lahira, Amin.

ASH-SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU (NATIONAL CHAIRMAN JIBWIS NIGERIA).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *