ANA NEMAN JEFA JIHAR TARABA CIKIN RIKICIN ADDINI SABODA SIYASA-SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU.

Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatussunnah (JIBWIS) ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki kan harkokin mulki a jihar Taraba, da su bi ka’idojin da suka dace don warware rudanin siyasar da ya kunno kai a jihar, ba tare da nuna banbancin addini ko na kabilanci ba.

Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi wannan kira ne a ofishinsa dake abuja yayin da wata tawaga ta mutanen Taraba ta kai masa ziyara a ofishin na sa. Sannan ya yi fatan samun lafiya ga Gwamna Danfulani Danbaba Suntai, wanda Allah Ya jarrabe shi da wannan rashin lafiya sakamakon hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a bara.

Shugaban ya bayyana cewa, a matsayinsa na dan asalin jihar Taraba kuma mai kishin jihar, “Ina fatan a dauki mataki don kada a jefa jihar cikin rudani da kiyayya, bayan su na zaune lafiya duk da bambancin addini da suke da shi.” In ji shugaban.

“Sannan muna kira ga shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya yi amfani da kujerarsa ta shugaba wajen daidaita al’amarin shugabanci a jihar Taraba kamar yadda dokar Nijeriya ta tanadar. Dukkan musulmi da kirista na jihar suna da hakki cikin gwamnati, saboda ba abu ne na bangare daya ba.”

Shugaban ya ce, tsawon lokaci da jihar Taraba ta yi, ana shugabanci ne tsakanin musulmi da kirista, kafin wannan larura da gwamnan ya samu, mataimakinsa na farko musulmi ne, sannan bayan majalisar dokoki ta jihar ta cire shi, a sake zabo musulmi a matsayin mataimakinsa, wato wanda ya ke rikon jihar a halin yanzu. Haka nan tsohon gwamna Jolly Nyame shi ma kirista ne, amma mataimakansa har hudu da ya yi dukkansu musulmi ne. A bisa wannan tsari jihar Taraba ta ke tafiya, don haka ka da a bari wasu mutane kalilan su saka siyasa don cimma wasu manufofinsu na neman kawo farraka a jihar Taraba.

“Sannan muna kira ga Janar TY Danjuma, a matsayinsa na dattijo kuma jagora da ya sanya baki cikin wannan al’amari tun kafin ya lalace, saboda mun ga irin rawar da ya taka don tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya ma baki daya ba Taraba kadai ba.

A qarshe shugaban ya yi kira ga ‘yan majalisar jihar da su ji tsoron Allah su yi abinda ya dace kamar yadda dokar kasa ta tanada a matsayinsu na masu yin doka a jihar, don wanzar da zaman lafiya tsakanin musulmi da kirista a jihar Taraba.
www.jibwisnigeria.org

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *