Cibiyoyin Tafsiran Izala Za Su Tara Wa Marayu Kayan Abinci da wasu abin bukatu a Sassan kasarnan~Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau

SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU, shi ne Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah JIBWIS, ta kasa, ya yi kira ta musamman ga dukkan Musulmin Nijeriya da su ji tsoron Allah, tare da kyautata niyya don fuskantar wannan wata mai al’farma na Ramadan, wakilinmu UMAR MOHAMMED GOMBE yana daga cikin wadanda suka tattauna da shugaban, jim kadan bayan da Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa game da daukan azumin Ramadana na wannan shekara, inda ya kasance babu inda aka ga jaririn watan a Nijeriya, wannan ne dalilin da ya sanya, Sultan din ya bayar da umarnin cika watan Shawwal zuwa kwanak 30. Ga yadda hirar ta gudana kamar haka:

Akaramakallahu kamar yadda muka samu wannan sanarwa daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi game daukar azumin Ramadan na wannan shekara cewa, ba inda aka gan shi, don haka za a cika watan Shawwal zuwa 30, shin a wannan shekara me kake fata Musulmin Nijeriya su yi a wannan wata mai alfarma na Ramadan?

To Alhamdulillahi, Wasallalahu wassalama ala Sayyidina wa Nabiyina Muhammad, wa ala alihi wa sahbihi waman tabi’ahum bi ihsanin ila yaumid-din. Assalamu Alaikum wa rahamatullahi ta’ala wa barkatuhu. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya sanya wannan azumi da za mu shiga ya zama sanadi kuma dalilin warwarewar matsalar da Musulmin Nijeriya suka samu kansu a ciki.

Sannan ba su kadai ba da ma dukkanin Musulmin duniya baki daya. Domin wata ne mai albarka wanda a cikinsa ne Allah Madaukaki Ya saukar da Alkur’ani. Inda Ya ke cewa, “Shahru ramadanallazi unzila fihil Kur’ana, hudan linnasi wa bayyinatin minal huda wal furkan….” A cikin wannan wata ne aka saukar da Alkur’ani mai girma, sannan har ila yau a cikinsa akwai wani dare mai albarka, wanda darajarsa ta fi shekara dubu. shine daren ‘Lailatil Kadri’. Inda Ubangiji Ya ke cewa, “Inna anzalnahu fi lailatil-kadri.” To wannan sauka Ubangiji Ya yi shi ne a lokaci guda cikin daren lailatil-kadri zuwa wani waje da ake cewa ‘Baitul Izza’ sannan daga nan kuma aka yi ta saukar da shi kadan-kadan a tsawon shekaru 23 na rayuwar Manzon Allah.

Gafarta Mallam kuna karantar da darussa da dama, kamar su Tauhidi da Hadisai da sauransu a masallatai, amma da zaran wannan wata na Ramadan ya kama, sai mu ga an rufe ko wane littafi an koma kan Alkur’ani kadai. Shin kai tsaye ko mene ne dalili?

Sosai ma kuwa, ai idan Ramadana ya tsaya to Manzon Allah ya na ajiye dukkan komai na karantarwa ya komawa littafin Allah, Alkur’ani Mai Girma. Mala’ika Jibrilu da kansa ya kan zo wa Manzon Allah su yi tushi da darasi na Alkur’ani, su karanta su sake komawa su karanta.

Sannan har ila yau Manzon Allah ya kan taimakwa al’ummarsa, har ma an ce ya fi iskar da aka sako sauri wajen ciyar da dukiya, kuma saboda fa’ida da albarkar wannan wata, sahabbansa sun kasance suna addu’ar Allah Ya nuna musu Ramadan tun watanni shida kafinsa, sannan sukan yi watanni shida bayansa suna addu’ar Allah Ya karbi ibadarsu.

Wannan dare da ka ambata a baya na Lailatil-kadri, ya ya za ka kwatanta alkhairinsa ga wanda ya riske shi?

To kamar yadda na fada a baya cewa, baki dayan Alkur’ani an saukar da shi ne cikin wannan dare. Kuma Allah ne da kanSa ya fadi alkhairin wannan dare na Lailatil-kadri cewa, ya fi dare dubu daraja. To idan ka lissafa darare dubu kadai, za ka samu fiye da shekaru 80, to ashe ke nan wannan wani garabasa ne daga Ubangijni zuwa ga bayinsu. Saboda shekarun wannan al’umma yana tskanin 60 – 70 ne kamar yadda ya zo cikin hadisi. Amma sai aka ba mu kyautar shekaru fiye da 80 a cikin dare guda kadai, hakika wannan ya na nuna soyayyar da Allah Ya ke yi ga bayinsa. Don haka wannan dare ba na wasa ba ne, sai mu mayar da hankali don neman dacewa da shi, muna fata Allah Ta’ala Ya datar damu baki daya.

Ga al’ada idan wannan wata na Ramadan ya zo, sai wasu ‘yan kasuwa su rika kara farashin kayan masarufi, ko wane kira Mallam zai yi ga irin wadannan ‘yan kasuwa?

To wannan ba daidai ba ne, ana bukatar ‘yan kasuwa musulmai su nuna rahama da tausayawa, sannan su nuna cewa wannan watan musulunci ne, har ma wadanda ba Musulmi ba su gane cewa wannan addini rahama ne garesu su ma. Domin ga wani wata na addinin musulunci ya zo suna samun sauki, kuma ‘yan kasuwa su kula cewa a lokacin da suke fatan samun lada, kar su yi tsammanin samun riba mai yawa, don al’umma su samu sauki. Da wannan ne nake kira garesu da su sausauta farashin kayayyakinsu. Dubi wadanda ba Musulmi ba ma suna yin abu a lokacin ibadarsu da suke cewa Bonanza. To idan wanda ba Musulmi ba ya yi haka, to kai Musulmi me ake zaton gani daga gareka? Don haka su dubi Allah su sassauta don su ma Allah Ya sassauta musu.

Sannan ba ‘yan kasuwa kadai ba, su ma mawadata su taimaka wa al’umma, saboda Allah Ya kawo azumi ne don Ya dandana musu halin da talakawa ke ciki a shekara. Akwai wani mawadacin da idan ba don Ramadana ba, to ba bu ranar da zai yi azumi tsawon rayuwarsa. Amma sai Allah Ya wajabta shi akan kowa don ya gane cewa akwai wanda yake wuni bai ci komai ba, don haka Alla Ya kawo domin ka dandana don ka tallafa wa talakawa a rayuwarsu ta cikin Ramadan da bayansa.

Kuma yanzu haka mu a Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah mun fito da wata gidauniya don tallafawa gajiyayyu da marayu da masu rauni, kuma mun umarci dukkannin malanmu da za su gudanar da tafsiri da cewa, su kafa wannan gidauniya don taimakawa marayu da mabukata. Saboda marayu su ji kamar mahaifansu su na nan da rai. Duk irin hidamar da muke yi wa ‘ya’yanmu to su ma marayu mu tuna da su, don haka malanmu su yi amfani da wannan dama don kira ga mawadata da su taimaka don gudanar da irin wannan aiki. Ina tabbatar muku cewa idan muka yi haka, to da sannu Allah Zai ji kanmu sannan ya dawwamar mana da zaman lafiya a kasarmu. Ya zo a cikin nassin hadisi cewa, Manzon Allah ya ce ni da mai taimakon maraya kusa muke a gidan Aljannah, sannan duk mai taimakon maraya kamar mai yin jihadi ne fisabilllahi.

Akwai wata ibada wacce ake tarewa cikin masallaci wato I’itikafi, shin ya ya kamata Musulmi ya yi wannan ibada a lokacin Ramadan?

Wannan tambaya ce mai muhimmanci. I’itikafi wata ibada ce mai dumbin lada da Allah (SWT) Ya ke bai wa bayinsa. To amma a yau akwai kurakurai da yawa da mutane su ke yi da sunan I’itikafi a masallatai. Da farko ana son mai I’itikafi ya yi ta cikin masallacin juma’a, idan akwai ranar juma’a cikin kwanakin da ya ke son yin wannan I’itikafi a ciki. Ana son mai I’ikafi ya shiga bayan sallar Asuba, idan zai fita kuma ya fita bayan sallar Isha’i. sannan zai yanke duk wata hulda da kowa sai bayan ya fito. Sannan kar ya fita sai fita ta larura, kamar zuwa ban daki ko cin abinci. Kuma ana bukatar baki dayan zaman da zai yi a cikin masallacin ya zama daga sallah sai karatun Alkur’ani sai zikiri da saransu.

Amma a yau sai ka iske mutum ya shiga I’itikafi da wayarsa, ya na buga wa mutane ya na tura sakonnin tes da sauransu. Wani ma har intanet ya ke yi a cikin masallacin, sannan za ka iske wasu suna hira a tsakaninsu. Sannan abu mafi muni ma shi ne, irin yadda ake samun cakuduwar maza da mata a wasu wuraren I’itikafin, har a rika musayar kalaman soyayya da sauransu. To gaskiya wannn duk ba I’itikafi ba ne, bata lokaci sunansa. Don haka ina kira ga masu yin I’itikafi da su ji tsoron Allah, mutum ya san cewa wata ibada ce mai muhimmanci da zai yi zuwa ga Allah (SWT) don neman yardarsa.

To a karshe mene ne kiranka ga gwamnatin tarayya da kuma na jihohi?

Kira na gare su shi ne su ji tsoron Allah su sauke nauyin da Allah Ya dora musu na talakawansu. Domin dukkan shugaba mai kiwo ne, sannnan Allah zai tambayeshi akan kiwon da Ya ba shi. Idan ya yi yadda ya kamata ya na da sakamako kyakkyawa, idan kuma ya yi akasin haka to ya sani Allah Yana nan a madakata. Allah Ya ba mu ikon sauke nauyin da ke kanmu na shugabanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *