GORON SALLAH DAGA ASH-SHEIKH IMAM ABDULLAHI BALA LAU.

Ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau (Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah) ta kasar Najeriya yana yiwa dukkan Yan Uwa Musulmi Ahlussunnah Gaisuwar Sallah (Id-El Fitr) tare da fatan alkhairi a gare ku, Shugaban Wanda a yanzu haka yana kasar Saudiyya dan gabatar da ibada na Umrah, yace yaga Sakonnin yan uwa da sukayi ta rubutawa a dandalin Facebok da email dama wadanda suka yimashi Text Massage ta GSM, yace yana Godiya Kwarai da Gaske.

Shugaban ya Kara da Cewa Dukkan abubuwan da muka koya a watan Ramalana kada mu ajiye shi mu ci gaba da yin wadannan ayyuka har iya rayuwar mu, misali Sallolin Nafilfili, tsayuwar dare, Kame Harshe, kauracewa sa’bo, kyauta tare da Sadaka

Ya Kara da Cewa yana da kyau Mu bada Kulawa Ta Musamman akan Marayu da gajiyayyu Musamman na Unguwannin mu, idan munyi wannan kuma mun kiyaye tabbas Allah zai taimake mu muna raye ko bama raye.

Shugaban yayi kira na Musamman da kowa ya zama wakili a fagen Da’awa, kana iya yin wa’azi ga Musulmi in yana yin addini ba yadda yakamata yayi ba, Shima Wanda ba Musulmi ba kana iya yi masa wa’azi ya shiga addinin Islama, Nasara daga Allah take,saboda Allah ta’ala yana cewa “Idan Nasarar Allah ta zo da budi, kuma kaga mutane suna shiga cikin addinin Allah tawaga-tawaga. To kayi Tasbihi tare da godiya ga Ubangijinka, ka nemi gafarar sa. Lalle shi ya kasance Mai Yafiya ne”. (Q298).

Shugaban yace Mai Da’awa sai ya hada da Hakuri, matukar zakace a ajiye son zuciya ayi addini irin yadda yazo daga Wajen Annabi Muhammad Tsira da Aminci a gare shi, Duka, Zagi, cin mutunci, kage dama kisa duka wannan kada ya baka tsoro ko ya saka kasala akan kira akan Gaskiya, dan ba’a kanka aka fara a kuma ba’a kanka za’a kateka. Yace kada kayi tsokana, kuma in anci maka Mutunci kada ka rama, in kayi wannan ka tsira, domin “Allah madaukakin sarki yace:
“Babu wata magana da zai furta face akwai mai tsaro (a tare da shi) halartacce”. (Kaf: 18)

Shahararren Malamin tafsirin nan, Malam Ibnu Kasir ya fada dangane da wannan aya: Babu wata kalma da ‘dan Adam zai fada face sai an sa mata wanda zai rubuta ta ya ajiye masa ita. Kamar yadda Allah madaukakin sarki yace:

“Lallai akwai masu kiyaye-duk abin da kukayi-masu daraja, marubuta, suna sanin duk abin da kuke aikatawa” (infidar: 10-12)

Daga Karshe Ya Rufe Da dukkan wanda yake da shawari ko gyara akan wannan tafiya to kofa a bude yake, kowa na iya bada nasa gudun mawar ta hanyar da yaga zata same mu cikin gaggawa, kuma yace kofa a bude take na karban gaskiya tare da fadan gaskiyar ga ko wanene, kuma dukkan wanda zaizo ya bada gudunmawar sa na Wa’azi indai zaiyi aiki da Al’Qur’ani da Hadisi kuma ya bar dukkan abin da babu shi a wadannan littafi to yazo ya bada nasa gudunmawar a Mimbarin Izala.

Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon bijere mata.

BARKA DA SALLAH!!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *