GYARUWAR SHUGABANNI SHINE GYARUWAR AL’UMMAH.

ZAGIN SHUGABANNI!

Baya daga cikin TARBIYYAH da LADABI na Musulunci da aka samo daga magabata nakwarai tun daga kan SAHABBAN ANNABI S.A.W da kuma wanda suka biyo bayansu da kyautatawa.

Hakika la,antar shuwagabanni koda kuwa ba nagari bane yana tasiri matuka wajen kara lalata sha,aninsu da rashin dai daituwarsu, atarbiyya ta musulunci ko dabba ko abin hawa babur ko mota ba,a bada damar ala,ance su ba domin la,antar zata iya tasiri agaresu.

Hadisi ya tabbata wata rana wani mutum daga cikin sahabbai suna tafiya tareda Manzon Allah s.a.w sai abin hawansa wato rakumin wannan mutumin yake masa gardama da mutumin nan yaga haka sai yace: “ALLAH YA LA,ANCI WANNAN ABIN HAWA NAWA” nan take manzon Allah s.a.w yace asaurara, sai yace da mutumin tunda ka tsinema abin hawanka to sai ka sakeshi ya shiga jeji mu kam bazamu tafi da LA,ANANNE ba, haka dole mutumin nan ya rabuda rakuminsa sabilida ya tsine masa.

To dan uwa wannan fa dabba ce haka ta faru, to ina ga MUTUM? Kuma mutum dinma JAGORA SHUGABA wanda maslaharka mai yawa take hannunsa.

Hakika mu munsan shuwagabanninmu sunyi nesa da adalci sun rungumi zalunci amma kuwa wannan ba dalili bane na zaginsu da la,antarsu! A,a dalili ne na yi musu ADDU,AH akan Allah ya shiryesu ya sanyasu zama masu adalci, ko kuma mu roki Allah ya musanya mana da mafi alkhairinsu.

Wani babban malamin musulunci daga cikin magabata yake cewa: ” idan da inada tabbacin wata addu,ah guda daya tak da za,a amsa min idan na roka, to da akan shuwagabanni zanyi wannan addu,ah domin idan shuwagabanni sun gyaru to al,ummah ta gyaru.”

Haka nan kada mu manta da cewa in har munason ingantattun shuwagabanni nagari to dole mu mabiya talakawa sai mun inganta kanmu mun zama nagari, hakika alkwarin Allah tabbatacce ne, idan muka gyara to tabbas Allah zai gyara mana, idan kuma muka lalace muka manta da adalci akawunanmu to dole mu samu shuwagabanni kwatankwacinmu, wannan haka Ayoyin Alqur,ani da Hadisan Manzo s.a.w suka tabbatar.

Hakika munyi nesa da adalci akan kanmu, to ta ina kuwa zamu samu shuwagabanni masu adalci? Kowa fa so yake ya samu dama ya dama! Anya kuwa da gaske muketa wannan kururuwa ta rashin adalcin shuwagabanninmu?

Hakika mu gyara sai a gyara mana. Allah ya shiryardamu ya bamu shuwagabanni nagari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *