JIBWIS NIGERIA HAJJ 2013.

AIKIN HAJJI A SHARI’ANCE.

MAS’ALA TA {1} SHIGA IHRAMI A JIDDA:
SHIMFIDA:

Ko shakka babu, mas’alar Jidda Mikati ce ko kuwa ba Mikati ba? mas’ala ce babba cikin addini wacce kusan ta shafi dukkan Musulmi mai yin aikin Hajji ko Umra, kuma an yi ta fatawowi dabam-dabam cikinta, wasu sun ce cikin fatawowinsu kai tsaye: Jidda Mikati ne, wasu kuwa suka ce kai tsaye: Jidda ba Mikati ba ne, wasu kuwa suka bi hanyar rarrabewa cikin mas’alar. Kuma an sami Malamai dabam-dabam da suka yi tali’fi cikin mas’alar, daga cikinsu akwai wadanda suka yi rubutu mai fadi da kayatarwa, kamar: Sheik Adnan Al-Al’uur cikin littafinsa mai suna: (أَدِلَّةُ إِثْبَاتِ أَنَّ جُدَّةَ مِيقَاتٌ) Watau: “Hujjojin tabbatar da cewa Jidda Mikati ne”. Da kuma Dr. Abdullah As-Sakakir cikin littafinsa mai suna: (نَوَازِلُ الْحَجِّ) Watau Sababbin lamura da suka taso cikin aikin Hajji”, Allah Madaukakin Sarki Ya saka musu da alherinSa. Amen.

MIKATAN DA SUKA TABBATA CIKIN NASSI:

Akwai mikatai biyar da suka tabbata cikin nassi, wadannan Mikatai kuwa su ne: Zulhulaifa, da Juhfa, da Karna Manazil, da Yalamlam, da Zatu Irkin, kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhari hadisi na 1524 da Sahihu Muslim hadisi na 1181 daga Abdullahi Dan Abbas cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya sa wa ((Mutanen Madina mikatin Zulhulaifa, mutanen Sham kuwa mikatin Jhufa, Mutanen Najad kuwa mikatin Karnu Manazil, Mutanen Yaman kuwa mikatin Yalamlam, wadannan Mikatai na Mutanen wuraren da aka ambata ne, da kuma dukkan mutanen da suka biyo ta kansu daga cikin wadanda suka yi nufin aikin Hajji, ko Umra, mutanen da kuma suke ta cikin mikatan nan, to ko wannensu zai dauki harami ne daga inda yake zaune har ma mutanen Makka za su dauki harami ne daga cikin garin Makka)). A wata riwaya ta Imam Muslim hadisi na 1183 daga Jabir Dan Abdullahi An ce: ((Wurin daukan harami na Mutanen Irak shi ne Zatu Irkin)).

MIKATI NA RESHE

Akwai abin da za mu iya kiran shi: “MIKATI NA RESHE”, ko “MIKATIN MUHA’ZAH” watau wurin da yake seti da mikati mafi kusa da shi, kuma nisan shi zuwa Makka daidai yake da nisan wannan Mikati zuwa Makka, a nan ana nufin mutuminda ya nufi Makka saboda Umra, ko Hajji, amma hanyarsa ba ta biyowa ta kan daya daga cikin mikatan nan guda biyar da muka ambata dazu ba, to shi wannan mutum in ya iso inda yake hannun riga da mikatai biyu, sai ya duba ya gani da wani mikati ne cikinsu ya fi kusa da shi, idan ya gane Mikati mafi kusan, to, sai ya duba ya ga nisan nawa ne tsakanin shi wannan Mikatin da Garin Makka? In ya san nisan, to, sai ya auna daga inda yake zuwa Makka nisan shi ya kai nisan wannan Mikati zuwa Makkan? In ya kai to sai ya dauki harami daga wannan wuri nasa. Saboda wannan wurin a yanzu sunan shi ya zama “MIKATI NA RESHE” Misali: mutumin da ya taso daga Nigeria zuwa Makka saboda Hajji, ko Umra, in ya iso Jidda –masalan- sai ya auna ya gani daga Jidda zuwa Jhufa, da kuma daga Jidda zuwa Yalamlam, wanne ne ya fi kusa? In ya fahimci cewa Jidda ta fi kusa da Yalamlam a kan Jhufa, to sai ya auna ya gani daga Yalamlam zuwa Makka kilo mita nawa ne? Idan ya ga cewa kilo mita settin ne –masalan- to sai ya auna daga Jidda kuma zuwa Makka, in ya tarar kilo mita settin ne, to sai ya dauki haraminsa daga Jidda, saboda Jidda a nan ta zamanto masa “MIKATI NA RESHE”.

HUKUNCIN DAUKAN HARAMI KAFIN A KAI MIKATI:

Mas’alar daukan harami kafin a kai Mikati, watau mutum mai niyyar aikin Hajji ko Umra tun daga cikin gidansa, cikin garinsa, ko cikin filin jirgin sama na kasarsa, ya yi niyyar yin Hajjinsa ko Umra, ya yi talbiyya, ya sanya tufafin harami, ya haramta wa kansa dukkan abin da ihrami ya haramta masa, har sai ya gama dawafin umrarsa, ko jifan jamararsa da yankan hadayarsa. Wannan mas’ala muhimmiya ce ainon, saboda in an fahimce ta da kyau, to, za a iya fita daga mushkilar Jidda mikati ne, ko kuwa ba mikati ba ne. Saboda dukkan maluman Musulunci sun yi ijma’I a kan cewa duk wanda ya dauki ihrami na yin Hajji ko Umra kafin ya kai bigiren Mikati, to ihraminsa ya inganta, babu kuma wani jini a kansa, to amma mafi yawan malamai: Malikiyya, da shafi’iyya, da Hambaliyya, na kyamar hakan ba tare da haramtawa ba, su kuwa Maluman Hanafiyya suna ganin yin hakan shi mustahabbi. (Dubi Almugni na Ibn Qudama5/65-66). Hanafiyya sun ce hakan mustahabbi ne saboda dogara da hadisi na 1741 da Abu Dawud ya ruwaito daga Ummu Salama cewa Annabi mai tsira da amincin Allah y ace: ((Wanda ya hurta yin hajji, ko umra, daga Masallacin Aqsa zuwa Masallacin Haram, an gafarta masa abin da ya gabata da abin da ya yi jinkiri na zunubansa)). Imamul Albani ya raunana wannan hadisi kamar yadda ya zo cikin Dha’ifu Sunani Abi Dawud shafi na 175.

HUKUNCIN RIKON JIDDA A MATSAYIN MIKATI

Ya ku ‘Yan’uwa Musulmi! Idan mun fahimci wadanne ne Mikatan nan guda biyar da suka tabbata cikin nassi, sannan kuma muka fahimci abin nan da ake kira “Mikati na reshe” da kuma “Hukuncin daukan harami kafin a kai Mikati”? To, ya dace bayanammu yanzu su dawo kan jauharin mas’alarmu, wacce ita ce: Mas’alar hukuncin rikon garin Jidda a matsayin mikati, ko rashin rikon shi a matsayin mikati. Wannan mas’ala a fahimtarmu tana da bangarori biyu:-
Bangare na farko shi ne: Dukkan malaman Musulunci sun yi ittifaki kan cewa garin Jidda mikati ne ga mutanen da suka rike shi mazauni, kuma mikati ne ga mutanen da suke ba mazaunan shi ba ne na din-din amma sun zo ne domin su zauna cikinsa na wani dan lokaci, matukar dai a nan Jiddan ne suka daura niyyar yin aikin Hajji, ko Umra. Wannan bigire ijma’I ne tsakanin Maluman Musulunci.
Bangare na biyu shi ne: Ko wannan gari na Jidda yana iya zama mikati ga sauran jama’a banda wadanda aka ambata a baya? A nan Malamai sun yi sabani, sun yi maganganu daidai har hudu:-
Magana ta farko ita ce: Jidda ba mikatin kowa ba ne, sai wanda kawai yake mazaunin garin ne. Wannan ita ce maganar mafi yawa daga cikin malamai, hujjarta ita ce Jidda ba ta daga cikin Mikatan nan guda biyar da aka ambata a cikin nassi, kuma ba ta setin daya daga cikin Mikatan nan guda biyar, ko kuma mu ce guda biyau, Yalamlam da Juhfa.

Magana ta biyu ita ce: Jidda mikati ne ga dukkan wanda ya shigo garin, ko ta hanyar tudu, ko ta hanyar teku, ko ta hanyar sama. Hujjar wannan Magana ita ce: Jidda reshe ne na Mikati, saboda yana setin Mikatin Yalamlam. Wannan shi ne kaulin da Dr. Abdullahis sakakir ya zaba, kamar yadda ya zo cikin littafinsa mai suna Nawazilul Hajji 1/11.

Magana ta uku ita ce: Jidda mikati ne kawai ga wadanda suka zo garin ta hanyar teku, ko ta hanyar sama. Hujjar wannan Magana ita ce: lalle, Jidda ba ta setin daya daga cikin Mikatan nan da ake da su guda biyar, to, amma saboda lura da aka yi na cewa akwai tsanani wahala idan har aka dora wa alhazai daukan harami cikin jiragen sama, ko cikin jiragen ruwa, duk kuwa abin da zai jawo tsanani da wahala ga Al’ummar Musulmi, to shari’ar Musulunci tana kauda shi daga gare su, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratul Bakara aya ta 185: ((..Allah Yana nufin sauki gare ku, ba Ya nufin tsanani gare ku..)). Kuma Ya ce cikin suratul Ma’ida aya ta 6 ((..Allah ba Ya nufin sanya wani kunci a kanku, amma yana nufin Ya cika ni’imarSa a kanku tsammanin za ku gode)). Kuma Ya ce cikin Suratul Hajji aya ta 87 ((..Shi ne Ya zabe ku alhalin bai sanya wani kunci a kanku ba cikin addini..)).

Magana ta hudu ita ce: Jidda mikati ne kawai ga mutumin da ya zo garin ta bangarensa na yamma, watau kamar mutanen da suka zo daga kudancin Masar, ko arewacin Sudan, ko daga Nigeria da makwabtanta, sawa’un sun zo ne ta jirgin ruwa, ko kuwa sun zo ne ta jirgin sama. Hujjar wannan Magana ita ce: su wadannan da suka zo ta wannan nahiya ba su bi ta wani Mikati ba kafin su iso Jidda, ballantana a kama su da laifin ketare Mikati kafin daukan harami. Wannan Magana ta hudu ita ta fi damun mu, mu mutanen Nigeria. An sami Maluma da dama da suka tafi kan wannan mazhaba, daga cikinsu akwai Babban Malamin nan na Kasar Saudiyya, watau Sheik Abdullah Bin Abdurrahman Al-Jibreen, ga ma abin da yake cewa cikin littafin Sharhu Umdatil Ahkam 9/35: ((Zai yiwu Jidda ta zamanto Mikati ga wadanda ke zuwa daga Sudan, ko daga inda yake seti da Jidda ta bangaren yamma. Mutanen Kasar Sudan da abin da yake seti da ita ba sa bin kan wani abu daga cikin Mikatan nan da ake da su, saboda haka idan suka zo ta jirgin sama, ko suka zo ta jirgin ruwa bisa ga misali, sai mu ce da su: Mikatinku shi ne Jidda, amma wadanda ke zuwa daga Masar, da Siriya, ko masu kama da su, su wadannan suna bi ta Mikati kafin su iso Jidda, suna bi ta kan Juhfa, ko ta kan Mikatin mutanen Madina watau Zul-Hulaifa, wadannan ba ya halatta gare su su ketare mikatinsu ba tare da sun dauki harami ba. Saboda wannan Musulmi sai ya maida hankali sosai ta yadda ba zai fada cikin ketare iyaka ba, ta inda ba da jini zai zama wajibi a kansa)).

Daga cikinsu wadannan Malamai akwai Sheik Abubakar Mahmud Gumi daga Nigeria, da Sheik Mustafa Ahamaduz Zarqaa daga Jordan, kamar yadda yake rubuce cikin littafin “Mujallatul Buhuthil Islamiyya 32/333. Da kuma littafin Fatawa Islamiyya 2/436. Da Sheik Abdul Karim Al-Khudhayyir cikin littafin Sharhu Umdatil ahkam1/23.

FAHIMTAR MAI RUBUTU:

Na amince da Fatawar su: Sheik Abdullah Bin Abdurrahman Al-Jibreen, da Sheik Abubakar Mahmud Gumi, da Sheik Mustafa Ahamaduz Zarqaa, na cewa: Jidda mikati ne kawai ga mutumin da ya zo garin ta bangarensa na yamma: kamar mutanen kudancin Masar, da arewacin Sudan, da Nigeria da makwabtanta. To amma na fi son Alhazammu da aka san cewa za su wuce ne kai tsaye zuwa Makka daga saukarsu Jidda su dauki haraminsu daga nan gida Nigeria. Allah Shi ne Ya fi sani, kuma Shi ne Mai ba da taufiki.

MAS’ALA TA {2} HUKUNCIN KWANAN MINA CIKIN FILIN MUZDALIFA:

Dukkan mai kyakkyawan nazari cikin littattafan Musulunci zai fahimci cewa wuraren da aka yi tattalinsu saboda yin aikin ibada, to, idan bukatar fadada su ta kama, kamar kuncinsu saboda yawaitar masu ibada cikinsu, ana iya fadada su. Saboda abu ne da ya tabbata cikin littattafan Musulunci cewa Salafus Salih sun kara fadada Masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah a lokacin da bukatar haka ta taso. Khalifa Umar Dan Khattab Allah Ya kara masa yarda ya fadada Masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah a shekarar Hijira ta 17 a inda tsawonsa ya kai zira’I 130 fadinsa kuma zira’I 120, sannan Khalifa na uku Uthman Dan Affan ya fadada shi a shekarar Hijira ta 29 a inda tsawonsa ya kai zira’I 160, fadinsa kuwa zira’I 130, sannan a shekarar Hijira ta 88 Khalifa Amawiy Alwaleed Dan Abdul Malik ya fadada shi a inda tsawonsa ya kai zira’I 200, fadinsa ma zira’I 200, sannan a shekarar Hijira ta 160 Khalifa Abbasiy Al-Mahdiy ya fadada shi ta inda ya kara fadinsa ta bangaren arewa har na tsawon zira’I 65, sannan a shekarar Hijra ta 1370, miladiyya ta 1951, Sarki Abdul Aziz Alu Su’ud ya fadada shi a inda ya kai murabba’in mita dubu shida, sannan a shekarar miladiyya ta 1986 Sarki Fahad Dan Abdul Aziz ya fadada shi fadadawa mai yawan gaske ta inda girmansa ta dukkan bangarorinsa ya kai murabba’in mita dubu dari hudu. [Dubi Sahihu Ibni Khuzaimah 2/282, da Tarikhul Masajidish Shahira 1/42-46].
Kuma Maluman Musulunci sun bayyana cewa: Hukuncin yin salla a inda aka kara na Masallacin Haram da ke Makka, da kuma Masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah da ke Madina, shi ne hukuncin yin salla a asalin Masallatan biyu. Watau karin na daukan hukuncin abin da aka karan. Ya zo cikin Littafin Fatawal Lajnatid Da’imati Lil Buhuthil ilmiyyati Wal Ifta’I 6/228-229 cewa:-
Tambaya: Shin salla a inda aka fadada na Masallacin Annabi karkashin laimomin da aka kafa, kamar yin salla ne a cikin Masallacin Annabi?
Amsa: Wuraren da ke shiga cikin Masallatai bayan an fadada su ana ba su hukuncin asalin Masallatan ne, a bisa wannan ana daukar karin da aka yi a Masallacin Annabi a ka shigar da shi cikin Masallacin Annabi hukunce-hukuncen Masallacin Annabi na asali na gudana kansa na irin rubanya lada da wanin haka, koda yake dai samun lada na bambanta da juna saboda bambancin da ake samu cikin ba da sallar, watau cikin yinta a sahun farko ko a sahu na biyu, da abin da ya yi kama da wannan)).

Saboda wannan, a yanzu idan filin Mina ya yi kunci da matsi ga mahajjata ta yadda in har ba a fadada shi ba za su cutu, ke nan ya zama wajibi a shari’ance a dauki matakan fadada shi, da yalwata shi, saboda yin aiki da ka’idodin Ilmin Qawa’idul Fikhi, kamar ka’idar nan da take cewa: (الْمَشَقَّةُ تَجْلِبُ التَّيْسِيرَ) watau “Tsanani na jawo saukakarwa” da kuma wacce take cewa: (الضَّرَرُ يُزَالُ) watau: “Ita cutarwa ana gusar da ita ne” [Dubi littafin Alwajeez na Dr. Muhammad Sudqiy shafi na 157,201, da littafin Alqawa’idul Fiqhiyyah na Ali An-Nadwiy shafi na 252,265].

Ya zo cikin littafin “Fatawal Lajnatid Da’imati Lil Buhuthil Ilmiyyati Wal Ifta’I 11/266 kamar haka: ((Bigire da kuma zamanin da ake gabatar da aikin Hajji abubuwa ne da shari’a ta bayyana iyakokinsu, babu fagen ijtihadi cikinsu, kuma Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi aikin hajji: Hajjin ban kwana ya ce -a lokacin wannan Hajjin: “Ku koyi ayyukan hajjinku daga gare ni, watakila ba zan sake gamuwa da ku ba bayan wannan shekara tawa” a wannan Hajjin ya bayyana iyakokin wuri, da kuma zamani na aikin Hajji. Iyakokin Mina suna farawa ne daga kwarin Muhassir har zuwa Jamratul Aqabah, saboda haka wajibi ne a kan wanda ya tafi aikin hajji ya nemi bigire cikin iyakokin Mina ya zauna, idan hakan ya gagare shi, to, sai ya sauka a wani wuri wanda yake kusa da filin Mina, in ya yi hakan babu kome a kansa)).

FAHIMTAR MAI RUBUTU:

Na amince da abin da Hukumar Su’udiyya ta yi na fadada tantunan Mina har zuwa wani bangare na filin Muzdalifa, saboda tabbatar da maslahar Alhazai da tunkude musu cuta da kunci, amma kuma ina ba da shawarar cewa abin da ya kamata Hukumar Su’udiyya ta yi shi ne: Ta gina benaye a filin Mina maimakon kakkafa tantuna, a nan sai ka ga cewa an yi maganin dukkan cinkoson da ake gani a Mina yanzu, kuma za ku ga cewa ko wane alhaji ya sami damar kwana a asalin filin Mina, ba wai a filin kari da aka yi saboda maslaha ba, domin in aka gina benaye za ku ga cewa filin da aka yi tattalinsa a da saboda mutanen Nigeria, to, a lokacinda aka gina benayen wannan filin sai ya ishi mutanen Kasashen Pakistan da Bangaladash da Indiya gaba daya. Allah Shi ne Mafi sani, kuma Shi ne Mai ba da taufiki.

MAS’ALA TA {3} HUKUNCIN JIFAN JAMARAT NA KWANUKAN TASHRIKI:
SHIMFIDA:
Saboda irin yadda mas’alar: Ko ya halatta a yi jifar jamarat a cikin kwanukan tashrik kafin zawalin rana, ko kuwa bai halatta a yi jifar ba sai bayan zawali? Saboda muhimmancinta a wannan zamani namu, zamanin da mahajjata suka yawaita ainon, suka kai miliyoyi, ga kuma irin rashin yelwar filin da ake yin jifar cikinsa, wanda wannan shi ya sa ake ta samun hatsura dabam-dabam lokacin jifar, wasu lokutan ma abin ya kan kai zuwa rasa rayukan jama’a da dama, wannan dalili ya sa an samu da yawa daga cikin Maluman Musulunci sun yi ta rubutu kan wannan mas’ala, saboda samo hanyar da ya kamata a bi domin kubutar da Mahajjata daga wannan mushkila. Daga cikin Maluman da suka yi rubutu akwai:-
Sheik Abdullah Alhawaliy Ash-Shamraniy. Inda ya wallafi littafi mai suna: (جِسْرُ الْجَمَرَاتِ) watau Gadar Jamarat.
Da Dr. Sharaf Bin Ali Ash-Shareef. Inda ya wallafi littafi mai suna: (رَمْيُ الْجَمَرَاتِ وَمَا يَتعَلَّقُ بِهِ مِنْ أَحْكَامٍ) watau Jifar Jamarat da abin da yake rataye das hi na hukunce-hukunce.
Da Sheik Abdul Muhsiniz Zaamil, shi ma ya yi rubutu mai kyau kan mas’alar, da sauransu. Allah kadai ke ba da taufiki, She ne kuma gatan Musulmi.

SABANIN MALAMAI GAME DA JIFAR JAMARAT KAFIN ZAWALI A KWANUKAN TASHRIK:

Malaman Musulunci sun yi sabani kan ingancin yin jifar Jamarat kafin zawalin rana a cikin kwanaki ukun nan na tashriki, zuwa maganganu da dama:-
1. Malikiyya, da Shafi’iyya, da Hanabila, sun tafi kan cewa: Jifar Jamarat cikin kwanukan tashriki ba ya inganta sai in an yi shi bayan zawali. Hujjarsu a nan ita ce hadisi na 2635 da Imamu Ahmad ya ruwaito cikin Musnad4/386 daga Abdullahi Dan Abbas cewa: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi jifar Jamarat (a ranakun tashriki) lokacinda rana ta yi zawali)). Sheik Shu’aibul Arna’ut ya hassana wannan hadisi cikin talikinsa a kan Musnadu Ahamad 4/386. Sannan Imamu Muslim ya ruwaito hadisi na 602 cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((ku koyi ayyukan hajjinku daga gare ni)). Suka ce abin da za mu koya a nan shi ne: yin jifar Jamarat bayan zawali, cikin ranakun tashriki, domin shi ne Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi.

2. Imam Abu Hanifa ya tafi kan cewa: yana inganta bayan fitowar alfijir a yi jifar Jamarat a rana ta uku kawai na kwanukan tashrik amma tare da kyamar yin hakan. Hujjar Abu Hanifa a kan wannan shi ne: Tunda dai shari’a ta yaddar wa mahajjata su bar yin jifar ma gaba daya a ranar tashriki ta uku, saboda saukake musu wahala, ke nan ya halatta a saukake musu in har za su yi jifar a ce: Su yi ta kafin zawali bayan fitowar alfijir.

3. Tabi’I Tawus Dan Kaisan, da Tabi’I Ata’u Dan Abi Rabah sun tafi kan cewa yana halatta a yi jifar Jamarat a dukkan kwanuka uku na tashriki. Kuma wannan shi ne kaulin wasu daga cikin Maluman Hanabila, kuma akwai riwayar haka daga Imamu Abi Hanifa. Hujjarsu a nan ita ce: Abin da dama aka shar’anta cikin wadannan kwanaki uku na tashriki shi ne: Yin jifar Jamrorin nan guda uku, wanda kuma wannan ba karamin aiki ba ne, saboda haka abin da ya fi dacewa da wannan shi ne: Sai a yalwata lokacin wannan jifar, ba wai a kuntata shi ba. Kuma har yanzu muna iya kiyasta jifar wadannan kwanaki uku na tashriki a kan jifar ranar Babbar Salla, mu ce: Ya halatta a yi jifar Jamarat kafin zawali a cikin kwanaki uku na tashriki, kamar yadda ya halatta a yi jifar Jamratul Aqabah a ranar Babbar Salla kafin zawali, saboda ko wanne daga cikinsu jifar Jamarat ne a filin Mina. Aikin da kuwa Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi na yin jifar Jamarat a ranaku uku na tashriki bayan zawali, wannan ya yi shi ne saboda zaben abin da ya fi yawan lada ba wai saboda yin sa ya zama dole ba.

FAHIMTAR MAI RUBUTU:
A bisa ga abin da ya gabata na maganganun Malamai da hujjojinsu, lalle ya bayyana mana a fili cewa yin jifar Jamarat a ranakun tashriki bayan zawali shi ne asali, shi ne kuma ya fi karfin dalili, shi ne kuma mafi yawan malamai suka yi riko da shi, wannan shi ya sa ma wanda duk ya yi haka, an yi ittifaki kan cewa jifarsa ta inganta, amma wanda ya yi sabanin hakan wasu malamai sun ce jifarsa bata inganta ba, wasu kuwa sun ce jifarsa ta inganta. To amma duk da wannan, idan har majibincin lamarin Musulmi, watau sarkin kasa, ko shugaban kasa ya yi nazari mai zurfi game da wannan mas’ala har ya kai ga fahimtar cewa: Umurtar alhazai su yi jifar Jamarat cikin kwanakin tashriki kafin zawalin rana shi ne zai sama musu maslaha: maslahar tsare lafiyarsu, ko tsare dukiyarsu, ko tsare rayukansu, to a wannan lokaci wajibi ne al’ummar musulmi masu aikin hajji su yi masa da’a, musamman ma idan aka fahimci cewa: Shi wannan aikin Hajjin fa dama an gina shi ne a kan saukake wa mutane, da rashin kuntata musu. Kamar dai yadda Imamul Bukhari ya ruwaito hadisi na 83, da Imamu Muslim hadisi na 1306 daga Sahabi Amru Dan Ass cewa ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a Hajjinsa na bankwana, ya tsaya saboda mutane su tambaye shi a filin Mina a ranar Babbar Salla, sai wani mutum ya zo masa ya ce: Ban fadaku ba har na yi aski kafin in yanka hadayata? Sai ya ce da shi: Ka yi yankar babu kome, sai wani mutum ya zo masa ya ce: Ban fadaku ba har na yanka hadaya kafin na yi jifar jamrah? Sai ya ce da shi: Ka yi jifar babu kome. Watau babu hukuncin wani abu da aka tamabaye shi wanda ya kamata a jinkirta, amma kuma aka gabatar, ko wanda ya kamata a gabatar, amma kuma aka jinkirta a wannan ranar face sai ya ce: Ka yi kawai babu kome)). Wannan hadisi yana gwada mana cewa fidda alhazai daga cikin kunci, da masi, abu ne wanda yake babban ginshiki cikin aikin Hajjin da Allah Ya shar’anta wa Al’ummar Musulmi. Allah Shi ne Mafi sanin al’amura, kuma Shi ne Mai yi wa bayinSa taufiki.

MAS’ALA TA {4} HUKUNCIN LAZIMTAR YIN MAKO GUDA A MADINA
SHARI’A BATA WAJABTA WA ALHAJI YIN MAKO GUDA A MADINA BA
A gaskiya babu inda shari’a ta wajabta wa alhazai yin mako guda a garin Madina saboda samun salloli arba’in cikin jam’I a Masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah, babu wajibcin haka cikin Alkur’ani mai girma, ko Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah, ko Ijma’in Maluman Musulunci, saboda wannan, duk wanda ya wajabta hakan to ya yi mummunar bidi’a, Allah Ya tsare!

HUJJAR DA WASU KE AMBATAWA NA YIN HAKAN

A kwai wasu mutane daga cikin masu wajabta hakan da ke kafa hujja da hadisi na 12,583 cikin Musnad na Imam Ahmad 20/40 daga Anas Dan Malik cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((مَنْ صَلَّى فِي مَسْجِدِي أَرْبَعِينَ صَلَاةً لَا يَفُوتُهُ صَلَاةٌ كُتِبَتْ لَهُ بَرَاءَةٌ مِنْ النَّارِ وَنَجَاةٌ مِنَ الْعَذَابِ وَبَرِئَ مِنَ النِّفَاقِ)) Watau: ((Wanda ya yi salloli arba’in a masallacin nan nawa ba tare da wata salla ta kubuce masa ba, to, an rubuta masa kubuta daga Wuta, da kuma tsira daga azaba, kuma ya kubuta daga munafirci)).

AMSAR WANNAN SAI A CE:

Na farko dai: Wannan Hadisi dha’ifi ne, ba a iya tsaida hujja da irinsa, saboda cikin isnadinsa akwai wani mutum majhuli watau wanda ba a sani ba, shi ne Nubait Dan Umar. Masanin hadisin nan Sheik Shu’aibul Arna’ut ya raunana shi saboda jahalar shi Nubait Dan Umar, kamar yadda ya zo cikin hashiyar Musnadu Ahmad 20/40, haka ma Imamul Albani a cikin littafinsa na Manasikul Hajj 1/63, da littafinsa Hajjatun Nabiy1/142. Sannan shi Imamul Albaniy ya ce cikin Manasikul Hajji wal Umra1/63: ((Lazimtar zama mako guda da masu ziyarar garin Madina ke yi, domin su sami damar yin salloli arba’in cikin masallacin Annabi, saboda a rubuta musu kubuta daga Wuta da kuma munafirci (ba daidai ba ne) saboda hadisin da ke Magana kan hakan dha’ifi ne ba a kafa hujja da shi, na bayyana illarsa cikin Silsilatul Ahadisid Dha’ifa 364, ba ya halatta a yi aiki da shi, domin yin hakan shar’anta hukunci ne, kuma hakan yana iya matsawa wasu alhazan, kamar yadda na san hakan da kaina, saboda tsammanin da suke yi na cewa hadisin mai inganci ne, sannan kuma (wani alhajin) na iya rasa yin wasu sallolin farillan (cikin Masallacin Annabin) ka ga a lokacin sai ya shiga cikin kunci ainon, kuncin da tuni Allah ya raba shi da shi)).

Na biyu: Koda wannan Hadisn ya inganta zahirinsa ba ya wajabta wa alhazai yin mako guda a garin Madina, domin gayarsa a wannan lokaci shi ne ya nuna falalar da ke cikin yin wadannan sallolin ne kawai, ba tare da cewa wanda ya kasa yin hakan ya yi wani laifi ba a shari’a.

Na uku: Hadisi ingantacce da ya zo cikin wannan babi shi ne hadisi na 241 wanda Imamut Tirmizi ya ruwaito daga Anas Dan Malik cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((مَنْ صَلَّى لِلَّهِ أَرْبَعِينَ يَوْماً فِي جَمَاعَةٍ يُدْرِكُ التَّكْبِيرَ الأُولَى كُتِبَ بَرَاءَتَانِ، بَرَاءَةٌ مِنَ النَّارِ وَبَرَاءَةٌ مِنَ النِّفَاقِ)) Watau: ((Duk wanda ya yi salla cikin jam’I saboda Allah na tsawon kwana arba’in yana kuma riskar kabbarar farko, to za a rubuta masa kubuta biyu: kubuta daga Wuta, da kuma kubuta daga munafirci)).
Wannan hadisin Imamul Albani ya inganta shi cikin littafinsa Silsilatul Ahadisis Sahiha4/629, da kuma littafinsa Sahihul Jami’is Sagir2/1089. Kun ga a nan wannan hadisi sahihi bai kebance Masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah da wannan falalar ba, a’a koma a wani masallaci ne musulmi ya yi wannan aiki na ibada, to, zai sami wannan falala ta Allah Madaukakin sarki.

FAHIMTAR MAI RUBUTU:

Da wadannan bayanan da suka gabata ne za mu iya cewa: in har alhaji ya sami dama yana iya yin ko kwana nawa ne a garin Madina, wannan babu laifi cikinsa, in ya samu dama yana iya yin wata guda, ko mako guda, ko kwana guda, ko yini guda, gwargwadon dai abin da ya saukaka gare shi ba tare da lazimtar wani adadi ayyananne ba, saboda haka a duk lokacinda shugabannin alhazai suka ce kwana daya za a yi, to dayan ne za a yi, in kuma sun ce biyu, ko uku, ko hudu, ko biyar, ko shida, ko bakwai, ko fiye da haka, ko kasa da haka za a yi to hakan ne za a yi, wannan shi ne Musulunci, shi ne kuma tabbatar da maslaha ga mahajjata. Allah Ya taimake mu, Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon kin ta.

NADEWA:

Mun yi Magana kan ko Jidda mikati ne, ko kuwa ba mikati ba ne? A nan mun yarada da fatawar cewa: Mikati ne kawai ga mutumin da ya zo garin ta bangarensa na yamma: kamar mutanen Nigeria, amma kuma mun fi son Alhazammu da aka san cewa za su wuce ne kai tsaye zuwa Makka daga saukarsu Jidda su dauki haraminsu daga nan gida Nigeria. Mun kuma amince da abin da Hukumar Su’udiyya ta yi na fadada tantunan Mina har zuwa wani bangare na Muzdalifa, amma kuma muna ba da shawarar a gina benaye a Mina maimakon kakkafa tantuna da za su kai har wajen Mina. Mun kuma amince da cewa idan har shugaban Musulmi, sarki ko shugaban kasa ya nazarci mas’alar jifar Jamarat kafin zawali sannan ya umurci alhazai da yin haka saboda tsare maslaharsu, to ya zama wajibi ga mahajjata su yi masa da’a. Mun kuma amince da cewa: In har alhaji ya samu dama yana iya yin ko kwana nawa ne a garin Madina: yana iya yin mako guda, ko kasa da haka ko sama da haka, amma babu inda shari’a ta wajabta wa alhaji yin mako guda a garin Madina saboda samun salloli arba’in cikin jam’I a Masallacin Annabi mai tsira da amincin Allah, babu wajibcin haka cikin Alkur’ani, ko Sunnar Annabi, ko Ijma’in Maluman Musulunci.

Allah ya Bamu Ikon Yin Aikin Hajji Karbabbe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *