KHUDUBAR RANAR ARFA 9-12-1434, ASH-SHEIKH ALI-SHEIKH.

Bayan yabo da kirari ga Allah, da salati, da sallama, ga Annabi saw, Malam ya bude da ayar da tayi magana akan Amana da Dan Adam ya dauka, bayan Allah ya bijirar da ita ga sammai da kassai da duwatsu, sunki dauka saboda wahalarta.

1- Magana akan kadaita Allah da bauta.

2- Dacewa da gamaiwar Addinin musulunci ga duk duniya.

3- sakon manzan Allah saw ya shafi kowa duk duniya.

4- Addinin musulunci, yayi kira zuwa ga dukkan wani hali na kwarai, da mu’amala mai kyau

5- Addinin musulunci, yana da sauki wajan aiki, kuma yana kunshe da rahma,

6- Addinin musulunci, yayi kira zuwa ga bawa dukkan mai hakki, hakkinsa.

7- Addinin Allah amana ne a wuyan ko wanne musulmi, ya kare shi, ya yada shi, da duk damar da Allah ya bashi, ko wacce iri ce.

8- duk matsalolin da musulmi suka fada dalilinsa shine, nisa da koyarwar addinin su.

9- Shariar musulunci itace ta dace da ko wanne lokaci da zamani da guri, da yanayi.

10- kira ga musulmi su hada kansu, akan Littafin Allah da sunnar manzon Allah saw.

11- Matsalolin da musulmi suka shiga na kaskanci da wulakanci da cin kashi daga makiya musulunci, duka ya faru ne, saboda rauni da riko da koyarwar musulunci,

12- Malam yayi kira ga masu mulki da malamai da yan boko, da yan jarida da duk wani mai dama a hannu da yayi amfani da ita wajan yada addini da kareshi,

12- Malamin yayi magana gamai da rikici tsakanin musulmi, da makiya addini suke rura wuta ya kamata ayi taka tsan tsan.

13- Malam yayi kira ga masu kudi da suyi amfani da kudin su, wajan nema da kashewa ta hanyar da ta dace,

14- Malam yayi kira ga Alhazai da suyiwa Allah godiya bisa niima da Allah yayi musu ta zuwa wannan waje.

15- Malam yayi magna akan girman wannan rana da falalar ta.

16- malam yayi magana akan wajabcin koyan aikin hajji da yinsa da ilmi akan koyarwar Annabi saw.

17- Malam yayi magana cewa mu tuna da ranar alkiyamah da abubuwan da zai faru a wannan rana na tsanance- tsanance, da wuta da
aljannah ga wanda suka cancan ta,

18- a karshe malam ya cika khudubarsa da Addua da musulmin duniya da samun izza da daukaka da kuma mummmuna r addua ga makiya addini Allah ya trwatsa su, da kuma addua ga Allah ya bamu kyakyawa a duniya da lahira.

19- ya cika da salati da sallma ga Annabisaw da iyalan gidansa da sahabban sa, da tabiai, da dukkuan mutane na kwarai bayn addua ga shuwagabanni da Allah ya taimkesu wajan jn ragamr al’umma kuma ya basu mashawarta na kwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *