KUNGIYAR IZALA A JIYA DA YAU!!!

Yan’uwa masu Sunnah! Wajibi ne a kanmu a matsayinmu na wadanda suka bayyana wa duniya cewa za mu gina aqiidarmu, da ibadarmu, da mu’amalarmu a kan Alkur’ani da sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah, muka kuma bayyana wa duniya cewa mu membobi ne na Kungiyar”Jama’tu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah”wajibi ne a kanmu mu yi wa kungiyar adalci kada mu karya rubutattun ka’idodinta saboda neman mulkar mabiyanta, ko saboda yi wa wadanda Allah ya ba wa jagorancinta hassada.

Yan’uwa masu Sunnah! Lalle ne ku san cewa ita dai Kungiyar Izalah ta kafu ne a kan cewa Chairman dinta shi ne shugaban majalisarta ta zartaswa, babu inda aka ce shugaban majalisar masu wa’azinta shi ne shugaban majalisar zartaswanta, wannan shi ya sa ma tun lokacin kafuwar kungiyar a 1978 har zuwa lokacin da wasu ke kira lokacin rabuwarta a 1990-1991 dukkan tarurrukan da majalisarta ta zartaswa ke yi Chairman dinta na kasa Malam Musa Muhammad Maigandu ne yake jagorantar su, duk kuwa da cewa Malam Isma’ila Idris wanda yake shi ne shugaban majalisar masu wa’azinta shi ma yana halartan taruurukan, amma yana zuwa ne a matsayin memba na majalisar zartaswa ba wai a matsayin shugaban majalisar zartaswa ba.

Haka ma bayan faruwar abin da ake kira”Rabuwar kungiya gida biyu”a 1990-1991 inda aka zabi Malam Yusufu Sambo Rigacukun a matsayin shugaban majalisar masu wa’azi ita dai wannan ka’idar da kuma wannan hakikar ba su canja ba, saboda shi shugaba Malam Musa Muhammad Maigandu ne dai yake shugabantar dukkan wani taro na majalisar zartaswa matukar dai yana wurin, shi kuwa Malam Yusufu Sambo a karkashinsa yake zama a matsayinsa na shugaban majalisar masu wa’azi, kuma memba a cikin majalisar zartaswa.

Yan’uwa masu Sunnah! Haka fai aka ci gaba da tafiya har na tsawon shekaru 21 watau har zuwa 6/12/2011 a lokacin da Allah Ya yi wa Shugaba Maigandu rasuwa -Allah Ya yi masa rahama da gafara shi da sauran jama’ar Musulmi da suka rigaye mu gidan gaskiya-

Yan’uwa masu Sunnah! Wannan shi yake rubuce a cikin kundin tsarin mulkin kungiyar izalah, kuma da shi ne aka yi aiki a lokacin da Malam Musa Muhammad Maigandu suka yi aiki tare da Malam Isma’ila Idris na tsawon shekaru 12 sannan da shi ne aka yi aiki a lokacin da Malam Musa Muhammad Maigandu suka aiki tare da Malam Yusufu Sambo na tsawon shekaru 21.

Sannan wani abin sha’awa shi ne shi fa kundin tsarin mulkin nan na kungiyar izalah wasu mutane goma sha hudu ne (14) amintattu, kuma yardaddu daga cikin membobin ita kungiyar a wancan lokacin, su ne aka zaba suka zauna suka rubuta shi wannan constitution din wadannan mutane kuwa su ne kamar haka:-
1-Malam Isma’ila Idris.
2-Malam Hudu Chikaji Zaria.
3-Malam Sidi Attahir Sokoto.
4-Malam Alhasan Sa’idu Jos.
5-Malam Sa’idu Hasan Jingir.
6-Malam Rabi’u Daura.
7-Malam Yakubu Musa.
8-Alhaji Ahmadu Gyalleso.
9-Alhaji Yaro Bichi.
10-Alhaji Bashir Makama.
11-Alhaji Ali Ibrahim Hikima.
12-Alhaji Bala Japan.
13-Alhaji Mamman Malumfashi.
14-Alhaji Isa Waziri Gombe.

Su wadannan mutane 14 su ne suka hadu suka rubuta wannan constitution na kungiyar Izalah, tare da shimfida kome da gina shi a kan ko dai a kan nassin Alkur’ani da Sahihan Hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah, ko kuwa a kan Ma’aquulin da bai saba wa Alkur’ani da Sahihin Hadithi ba.

Yan’uwa Musulmi! Lalle idan haka wannan lamari yake kamar yadda muka bayyana muku shi a yanzu, toh kuwa tabbas: Biye wa taguwar hassada ne, kuma cin amanar da’awah ne, sannan neman tarbiyyantar da Al’ummah masu tasowa ne a kan ruguza ka’ida, da yaudara, da shaidan zur, a ce wani zai zo bayan an zabi Shugaba ash-Sheikh Abdullahi Bala Lau a matsayin sabon Shugaban Kungiyar Izalah na kasa baki daya, ya tsaya a gaban jama’a a kan mimbarin wa’azi, ko a cikin wani masallaci, ko a cikin wata makaranta, ko a cikin tattaunawarsa da wasu abokan hirarsa ya ce: Haramun ne a ce: shugaban kungiyar izalah shi zai shugabanci shugaban majalisar masu wa’azi na kungiyar izalah! Sannan kuma ya ce: duk mutumin da ya yarda da abin da yake rubuce a cikin kundin tsarin mulkin kungiyar izalah na cewa: dukkan shugabannin majalisun da suke cikin kungiya -daga cikinsu kuwa har da shugaban majalisar masu wa’azi- suna karkashin shugaban kungiya na kasa ne, ko kuma ya ce: shi yana karban umurni ne daga shugaban kungiya ba wai daga shugaban majalisar masu wa’azi ba ya yi ta cewa: duk mai wannan kuduri da manufa a zuciyarsa mai raba kan Al’ummah ne, mai raba kan jama’ah ne, mai kin hadin kan yan kungiyar izalah ne, munafuki ne, dan tawaye ne!!

Yan’uwa masu Sunnah! Hakika dukkan mai aqiidar cewa shugaban majalisar masu wa’azi na kungiyar izalah ba zai taba zama a karkashin shugaban kungiyar izalah ba, toh lalle wannan ya saba wa tsarin mulkin kungiyar izalah, lalle wannan ya dauki hanyar raya wani reshe ne amma kuma ta hanyar kashe tushen shi wannan reshen, ma’ana ta hanyar kashe ita kungiyar izalar, duk kuwa wanda yake son raya wani reshe cikin wani abin kirki amma kuma ta hayar kashe tushen wannan abin kirkin toh kuwa wannan aiki nasa aiki ne mai munin gaske, wannan aiki nasa aiki ne na banza da wofi, saboda ya zo a rubuce cikin littafin Almuwaafaqaat 4/24 da Attahriiru Wat Tanwiir4/19’da Nash’rul Abiir shafi na 57’da Mujallatu Majma’il Fiqhii Islaamii 2-8779 cewa: Qaa’idar Usuulul Fiqh tana cewa:-
{اذا عاد الفرع على الاصل بالابطال كان الفرع باطلا}.
Ma’ana: ((Idan reshe zai kai ga kashe tushe, toh reshen ya zama banza)).
Saboda masu cewar shugaban majalisar masu wa’azi na kungiyar izalah ba zai zauna a karkashin shugaban kungiyar izala ba, lalle wadannan mutane, mutane ne masu bukatar rusa kungiyar izalah daga tushenta, lalle wadannan mutane, mutane ne da hassada ta aure su, lalle wadannan mutane, mutane ne maha’inta masu cusa wa matasanmu mugunyar tarbiyyah. Lalle wadannan mutane, mutane ne masu aqiidah irin ta yan shi’ah masu cewa shugaban majalisar malamai a kasarsu shi yake sama -a mulki da iko- da shugaban kasarsu. Allah ya tsare mu daga sharrin Hawaa da Bid’ah, ya kuma kare mana wannan kungiya tamu mai albarka”Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah”daga sharrin karkatattu yan duniya masu neman saba wa constitution dinta saboda mulkar jama’a ko ta halin kaka. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *