MANUFAR KUNGIYAR JAMA’ATU IZALATIL BIDI’AH WA IQAMATIS SUNNAH (JIBWIS).

Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhai Musa Gandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.

Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan manufofi da take so ta cimma domin kai wa ga gaci.

Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:

– Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu.

– Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW),

– Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.

– Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.

– Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).

– Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.

– Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.

– Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.”

– Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).

Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hada da:

Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Wasu daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da:

– Kwamitin Da’awah.

– Kwamitin Tarurrukan Wa’azi.

– Kwamitin Kula da Marayu

– Kwamitin Ilimi.

– Kwamitin Mutane Goma.

– Kwamitin Taimakon Gaggawa.

-Kwamitin Ayyuka.

-Kwamitin Sulhu da Fatawa.

-Kwamitin Masallatai.

-Kwamitin Karawa Juna Sani.

KWAMITIN ZARTASWA

Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Sheikh Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin shugabancin wannan kungiya tun bayan kafa kungiyar, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne bayan rasuwarsa.

– Marafan Tambuwal Shine: Mataimakin Shugaban Kungiya Na Kasa.

– Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiya

– Sheik Sani Yaya Jingir: Shugaban Majalisar Malamai na kasa

– Sheik Dr. Ibrahim Jalo Jalingo: Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Kasa

– Alh. Isa Waziri: Shugaban Yan Agaji na Kasa

– Engr Mustapha Imam Sitti: Mataimakin Shugaban Rundunar Yan Aagaji na kasa

kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Nijar da Mali da Sinigal da Togo da Kamaru da Cadi da Burkina da Gini, Saudi Arabia da sauransu.

Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hada da:

– Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.

– Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.

– Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni biyu ko uku ko hudu don tunatar da mutane abin da suka manta ko kuma lokutan da suka dace.

– Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.

– Kai ziyarori gidajen marayu da gidajen yari da asibitoci, domin tallafar musulmai marasa galihu.

– Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa.

Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo , dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma’ila Idris Bin Zakariyya suka bada ba, da irinsu Marigayi Sheikh Ibrahim Bawa Maishinkafa, Sheikh Hudu Chikaji Zariya, Sheikh Adam Maishafi, Sheikh Abubakar Imam Ikara da Sheikh Alhaji Musa Maigandu Muhammad, Koda ba manufarmu zayyana sunan kowa ba, amma muna addu’a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira.

Haka Suma Dattawan Izala na Farko Irin su Sheikh Dr. Alhassan Sa’eed Adam jos wanda shine Alaramma na farko a tarihin kafuwar kungiyar, da Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir, Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Sani Yahaya, Sheikh Rabi’u Aliyu Daura, Sheikh Habibu Yahaya Kaura, Alaramma Abubakar Adam Katsina, Alaramma Yahuza Bauchi da Sauran Shuwagabanni da yan agaji, muna addu’an Allah ya saka ma kowa da alkhairi ya hada mu a gidan aljanna fir’dausi.

Wannan kadan ne daga cikin irin manufofin da kungiyar Izala ta kafu a kayi tun asali, kuma a haka za’a tafi da ikon Allah.

Muna Addu’an Allah ya karkato Mana Da Hankulan Jagororin mu a koma Karantarwan Kungiyar ta Asali, Wato Kira kan Kitabu Wassunnah.

Daga Karshe Muna Addu’an Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata.

www.jibwisnigeria.org

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *