MARIGAYI SHEIKH AUWAL ADAM ALBANIN ZARIYA

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI ILAIHI RAAJI’UN!!!

‘Yan Bindiga Sun Harbe Sheikh Albani Zaria Da Mai Dakinsa Da ‘Dansa.

Wasu ‘yan bindiga, sun harbe Sheikh Muhammad Auwalu Albani Zaria, da matarsa da dansa, a kan hanyarsu ta komawa gida daga wurin ba da karatu.

Majiyar ta shaida mana cewa, abin ya faru ne yayin da malamin da iyalin na sa suke kan hanyar komawa gida daga masallacin da yake ba wa dalibai karatu bayan sallar Isha’i. Majiyar ta kara da cewa, nan take mai dakin na sa, ta ce ga garinku nan, a wurin da ta’addancin ya faru, yayin da shi kuma da dansa Allah ya dauki ransu bayan an garzaya da su asibitI, Tuni akayi musu Jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya ta tanadar a ranar Lahadi da misalin karfe Goma na safe 10:00am Anan cikin garin Zariya dake jihar Kaduna a tarayyar Nigeria.

Zuwan yanzu da muka kammala rubuta wannan labari ba a samu tabbacin wadanda suka aikata kisan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *