MATSAYIN RANAR ARFA A SHARI’AH!!!

Malamai sun yi Muhawara kan Asalin wannan babban fili mai albarka na Arfa da ke wajen Garin Makka, Wassu sauka ce: Lokacin da a ka saukar da Annabi Adamu da Nana Hauwwa’u a bayan kasa, an saukar da su gurare daban daban ne, Bayan tsawon lokaci suna neman Juna, sai su ka yi kicibis! a wannan Fili, Wannan shine farkon Ala’amarin Taro a wannan Katafaren Fili…Allahu a’alam.

Wannan Rana itace shugabar Ranakun Shekara, kuma Mafificiya cikin Yini, Allah yana saukowa kusa da Bayinsa yana bada Bonos din Karbar Addu’a , shi ya sa Annabi SAW yace: “Mafificiyar Addua’a, Addu’ar Ranar Arfa”

Komin Mukamin Mutum a wannan Rana sai ya shiga gajiya, wahala wato shiga cikin Rairayi, cunkoso, Gogaiyya da Talakawa, wani lokaci har Layin Bahaya ko Fitsari da sauran Gazawa da Kasawa.

Ga wadanda su ke Makkah dole su kula da Ladduba da Sharrudan Tsayuwar Arfa, In kuwa ba haka ba, sa yi tsayuwa Irin ta Baban Giwa!!
Ga Mazauna Gida kuma, Sunnah ce a Azumci wannan Rana ( wadda a bana gobe litinin 09 Dhul Hijjah 1434, 14/October/2013.

Hakika wannan Gangamin Musulmai da ke wannan ranar arfa babu irin tsawon shekara wajen musulmi na kwarai, wato babu Irinsa a Duniya, gaskiya ne! kowa ya je Makka kallo ya kare!!!

Allah ya baiwa mahajjatan mu ikon yin aikin Hajji Karbabbe, ga wadanda basu samu daman zuwa Makkah ba kuwa su azumci wannan yini na arafat a gobe litinin in Allah ya kaimu.

Allah ya amshi ibadar mu, ya karbi addu’oin mu.

Allahumma ij’alhu hajjan mubruran wa zamban magfuran wa sa’ayan mashkuran, wa tijaratan lan tabuur. Amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *