RANAR LAHADI 04/November/2013. MAIZUWA ZAAYI (KUSUFIN RANA) INJI MASU HASASHEN YANAYI !!!

HASASHEN MASANA YANAYI: Sunce Za’ayi Kusufi A Kasar Nan Ranar Lahadi Kamar yadda Darakta-Janar na hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasa (NSRDA), Dr. Saidu Muhammad, ya shaidawa manema labarai a ABuja, ranar Lahadi 3 ga watan Nuwamba, za a samu kusufewar a kasar nan da wasu kasashen dake gefenta. A wannan karon hasashen ya nuna cewa ranar za ta yi cikakken kusufi, wanda hakan ke nuni da cewa ranar zata buya ne baki daya, wanda a turance ake kira “Total eclipse”. Hasashen ya nuna cewa bangaren ranar zai fara kusufin ne da misalin 10:04:39 UTC/GMT daidai da agogon Nijeriya 11:04:39 na safe. Sannan abin zai yi tsanani inda dukkanin ranar zata dulmiye da misalin 12:46:28 UTC daidai da 1:46:28 na rana. Haka za a kasance daga nan har kuma abin ya rinka yin kasa – kasa ranar tana fitowa daga kusufin har zuwa 15:28:21 UTC daidai da 4:28:21 na yamma agogon Nijeriya.

Akwai yiwuwar kusufin ranan zai baibaye nahiyoyin Afirka da Turai da Amurka, musamman ganin cewa wata ya tare wani sashe na gurbin tafiyar rana.

Fasalin kwai da duniya ke da shi, shi ya bayyana dalilin da ya sanya daukacin fadin Afirka ta Yamma za taga kusufin rana, a yayin da Amurka da Turai za su ga wani sashe na kusufin.

Masana sun bayyana cewa, mutane su guji kallon rana kai tsaye, a lokacin kusufin, sai dai in suna da gilashin ’yan walda, wanda ke da siririyar mahangar ‘pinhole.’

ABIN LURA:
Hakan ba zai zama tabbas sai an yi shi ba, in Allah ya so sai ya canja tsarinsa.

In kuma Allah ya nufa hakan ta faru, to ana yin Sallar kusufewar rana a irin wannan rana, ba kamar yadda wasu kasashen turawa ke daukar ranar a matsayin ranar biki da sharholiya ba.

in har hakan ya tabbata kuma ga abunda yakamata kowa yayi kamar yadda yazo a hadisin manzan ALLAH (s.a.w).

Yana Cewa “Hakika Rana da wata ayoyine guda 2 daga ayoyin ubangiji.
basayin kusufi saboda mutuwar Dayanku ko dan rayuwar waninku, saidai kurun ALLAH yana Tsoratar da bayinsane dasu (dan sukara ganin girmansa )
dan haka idan kunga sunyi to ga abunda zakuyi, kudukafa da adduoi (kada allah yasa yazama azaba agareku ) kuyitayin kabbara (Allahu akabar )
ko kuyita yin hailalala. (lailaha ilallah)
Har Sai kunga ALLAH yayeyemuku.( wannan kusufi gari yadawo daidai )

Bukhari (1004 da 2783 da 992).
Muslim (1505 da 1506 da 1510)
Abu Dawud (1008′ da 997)
Ibnu Majah (1253).

Allah ya kubutar da mu daga dukkanin sharrin abinda yake kunshe cikin kusufin. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *