SHUGABAN KUNGIYAR JIBWIS TA KASA ASH-SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU YAYI KIRA GA YAN MAJALISU DA SUYI WATSI DA DOKAR YARINYA SAI TA KAI SHEKARA SHA TWAKAS KAFIN A AURAR DA ITA.

Shugaban yayi Wannan kiran ne a wa’azin da kungiyar ta gabatar a garin Bukkuyum ta jihar Zamfara, inda yayi wa’azi mai kama hankali sannan yayi kiraye kiraye ga yan majalisun kasarnan kan dokar da ake kokarin kafawa a kasarmu nigeria na ya baza’a aurar da yarinya ba sai takai shekara goma sha takwas, Ash-Sheikh Abdullahi balalu ya cigaba dacewa Addinin mu na musulunci ya koyama na yadda zamu Aurar da yayanmu in sun balaga. Shugaba yace akwai yaran da sun balaga tun suna shekara goma, kuma Manzo Tsira da aminci a gare shi ya Auri nana A’isha tun tana shekara shida tazo gidansa tana da shekara tara.

Hakika duk dan majalisar da ya amince da wannan doka kamar ya shirya fada ne da addinin Allah, dawannan shugaba yayabawa wasu da ga cikin yan majalisu da shugaban majalisar dattabai. Alokacin da suka shure dokar Auren jinsi. Sannan yace kungiyar izala tayi Allah wadai da wannan doka.

Sannan shugaba yayi kira ga yan’uwa Alhazai masu tafiya aikin hajji da suyi Addu’a Allah ya zaunar da kasanmu lafiya.

Sannan shugaba yayi tsokaci akan wasu bayin Allah wayanda suka kuduri aniyar cewa sai sun cutar da kungiyar ko yan kungiyar ko shugabannin kungiyar mu ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah, Shugaban yacigaba dacewa lallai mu munsani babu mai karemu ban da Allah wannan aikin da muke muna yinshi ne domin Allah. Sannan shugaba yayi Addu’an Shiriya ga wayannan bayin Allah masu tunanin ganin kungiyar ta shiga matsala, Allah ya ganar da su in madu ganewa ne.

Shugaban ya cigaba dacewa mun soma fuskantar rikita rikita na siyasa sannan yayi Addu’a Allah yakawo mana shi cikin sauki yakuma bamu shuwagabanni na kwarai masu Adalci wayanda zasu Shugaban cemu akowani mataki masu jin tsoron Allah. Sannan yayikira ga malamai dacewa karwani yahauminbari na wannan kungiya yashiga dandali na Siyasa domin mimbarine na karantar da addini. Kuma zamucigaba da addu’a Allah yakawomna shuwa gabanni na gari a wannan kasa tamu.

Shugaban yace Al’ummar musulmi muna da bukatar hadin kai kasantuwar yadda akasa musulunci agaba ako ina kuma akowani mataki, sannan yayi kira ga Al’ummar musulmida kar mutum ya kasance abokin gabanshi shine dan uwansa musulmi, kasani abokin gabanka shine Shedan.

Shugaban yacigaba dacewa Manufarmu shine Hadin kai, cigaban addini, cigaban sunnah ta manzo Allah tsira da aminci a gare shi, sannan yayi kira ga dukkan yan’uwa da suke gefe, cewa mu kofar sulhu abude take bai rufeba. Duk wadda yake neman sulhu da mu yazo kofa abude take, amma ya kasance akan Al’Qur’ani da Hadisi.

Shugaban yayi kira kan muntane da sukasance masu fitar da Alkhairi aduk inda suka tsinci kansu. sannan ya zayyono wasu da gacikin cigaban kungiyar da muka samu na bada dama ga duk wani malamin izala damar yayi wa’azi akasa mai tsarki, yace Wannan ba karamar nasara bace, kuma Malaman Saudiyya sun gamsu da wa’azin Sunnah da kungiyar Izala take yi a fadin Duniyar nan.

Zamu ci gaba insha Allah…………….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *