TAKAIYACCIYAR NASIHA

Annabi Muhammad Tsira da Aminci su tabbata a gare shi yace;
Dukkanin ku masu kiwo ne, kuma kowannen ku sai an tambaye shi game da kiwon da aka bashi;

Shugaba mai kiwo ne, kuma sai an tambaye shi akan Wadanda ya shugabanta, namiji makiyayi ne game da mutanen gidansa, kuma sai an tambaye shi akan abin da aka bashi kiwo, mace Makiyayiya ce a gidan mijinta da ‘ya’yan sa, sai an tambaye ta a kansu, Bawa Makiyayi ne akan dukiyar uban gidan sa, kuma sai an tambaye shi a kansu, Ku Saurara! Dukkanin ku masu kiwo ne, kuma sai an tambaye ku game da kiwon da aka baku.”

HADITH BUKHARI.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *