TSAYAR DA TAUHIDI SHI YAKE KAFA GOMNATIN SHARI’AR MUSLUNCI

Sau da yawa wasu masu kishin kawo gyara a cikin al’ummar musulmi sukan so kafa Gomnatin Muslunci wacce za ta tsayar da Shari’ar Muslunci a tsakanin musulmi, amma abin mamaki, sai ka ga sukan yi tuya su manta da albasa! Wato sukan yi gini ba tare da kafa tushe ba. Ma’ana sukan yi kokarin kafa Shari’a, don hana zina, shan giya, sata, fashi da makami, amma kuma sun gafala sun bar mutane ba su san Tauhidi ba, suna aikata Shirka ma Allah Ta’ala.

Alal hakika ba karamin kuskure ba ne ka faro gyara daga sama, alhali ka bar kasa a rube. Wannan ya sa sau da yawa masu fafutukan kawo gyara, masu son kafa Gomnatin Shari’ar Muslunci suke ta shan wahala, saboda sun kauce ma hanya madaidaiciya ta kafa Shari’a.

Annabi (saw) Shirka ya kawar, ya kafa Tauhidi a cikin al’ummar Sahabbai kafin ya kafa Gomnati wacce ta kafu a Madina, aka tsayar da Shari’ar Muslunci. Saboda asali an aiko Annabi (saw) ne don kira zuwa ga Tauhidi, da hani a kan Shirka. Allah ya ce:
ولقد بعثنا في كل أمة رسولا أن اعبدوا الله واجتنبوا الطاغوت.

Kuma du ya ce:
وما أرسلنا من قبلك من رسول إلا نوحي إليه أنه لا إله إلا أنا فاعبدون

Saboda asali don Tauhidi Allah ya halicci bayinsa, Allah ya ce:
وما خلقت الجن والإنس إلا ليعبدون

Kuma don haka ne Allah ya saukar da littatafai, har zuwa Al- Qur’ani, Allah ya ce:
ينزل الملائكة بالروح من أَمره على من يشاء من عباده أَن أَنذروا أَنه لا إِله إِلا أَنا فاتقون

Kuma du ya ce:
آلر كتاب أحكمت آياته ثم فصلت من لدن حكيم خبير . ألا تعبدوا إلا الله

Kuma ana yaki ne, da fita don gwabzawa, har azubar da jinane, har a samu shahada don tsayar da Tauhidi da kawar da Shirka. Allah ya ce:
وقاتلوهم حتى لا تكون فتنة ويكون الدين لله

Fitina a cikin ayar ita ce: Shirka.

Annabi (saw) ya ce:
من قاتل لتكون كلمة الله هي العليا فهو في سبيل الله

Kalmar Allah kuwa, ita ce kalmar Tauhidi; “LA’ILAHA ILLALLAH”. MA’ANA; “BABU ABIN BAUTA BISA CANCANTA SAI ALLAH”.

Ya kamata mu karanci Sunna da Sirar Manzon Allah (saw) mu fahimceta kafin mu shiga gwagwarmayar kafa gomnati don kafa Shari’a.

A zamanin yau, wasu masu niyyar kafa gomnatin Shari’a a kasashen Larabawa ne ko a Afirka suna yayata wannar kalma kamar haka: “BABU HUKUMA SAI TA ALLAH”!!

Wannar Jumla an samota ne daga ‘Yan kungiyar Ikhwan wacce cibiyarta ke kasar Misra, wadanda suke fassara kalmar Shahada; “LA’ILAHA ILLALAH” da cewa: “BABU HUKUMA SAI TA ALLAH”, kamar yadda masu Ilmul Kalam suke fassara kalmar da cewa; “BABU MAHALICCI SAI ALLAH”. Duka wadannan fassara guda biyu ba dadai ba ne, saboda wannan ba shi ne hakikanin ma’anar kalmar shahada ba. Ma’anar kalmar shahada ita ce; “BABU ABIN BAUTA BISA CANCANTA SAI ALLAH”.
Kaucewa daga ma’ana ta dadai na kalmar shahada, shi ya sa masu da’awar kawo gyara suke sakaci da lamarin Tauhidi, da sakaci da lamarin kawar da Shirka, abin da yake kai ga kowane mabarnaci sai ya buya bayan irin wadancan ma’anoni na kuskure da ya fi jan hankalin jama’a don cimma burinsa.

SAI MUN KAFA TAUHIDI MUN KAWAR DA SHIRKA, MUN RIKE SUNNA, MUN NISANCI BIDI’A, KAFIN MUN IYA KAFA GOMNATIN SHARI’AR MUSLUNCI.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *