Ba’a cire Sheikh Kabiru Gombe daga Sakataren Izala ba…

A yammacin Larabar da ta gabata ne aka samu bullar labarin cewa Shugaban Izala Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya tsige sakatarensa na kasa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe.

Wannan labarin ya fito ne daga wata jarida ta bogi mai shafi a Kafar sadarwa ta Facebook, wato jaridar HAUSA 7, wadda ba’a san masu ita ba, kuma ba’a san masu gudanar da ita ba.

Jin wannan labarin ne yasa muka tuntubi Babban daraktan Kwamitin yanar gizo na kungiyar Izala ta kasa, Ustaz Ibrahim Baba Sulaiman, don muji menene gaskiyar wannan lamarin. Inda ya labarta mana cewa wannan labari zance kawai ne, labari ne mara tushe balle makama. A cewarsa.

“Sheikh Kabiru Gombe da Sheikh Bala Lau aminan juna ne, kuma suna da’awarsu da ayyukan kungiya tare, babu wata matsala tsakaninsu da har zata kawo irin wannan mummunan labari. Ko a wannan makon sunyi tafiya tare zuwa birnin Lome dake kasar Togo domin gudanar da ayyukansu na da’awa” Inji Baba Sulaiman.

Ita dai jaridar bogi ta Hausa 7, sun bayyana labarin, har da karin cewa ‘zuwa yanzu Sheikh Bala Lau bai ambata sunan Sabon sakatarensa ba.

Yawaitar Jaridun bogi a kafofin sadarwa, yana daga abinda yake janyo yawaitar labaran Karya.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY