Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da cin Mutunci da yan kwankwasiyya suka yiwa Dr. Ali Pantami

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Kungiyar wa’azin musulunci ta Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah a Naijeriya, Tayi Allah wadai da cin Mutuncin da ‘yan kungiyar kwankwasiyya sukayi wa ministan sadarwan Naijeriya Sheikh Dr. Isa Ali Pantami a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake Birnin kano.

Shugaban IZALA Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau, shi yayi wannan kira ta wayar tarho daga Birnin Maiduguri jihar Borno a tarayyar Naijeriya, inda yake halartar wani taro a Birnin na Shehu.

Sheikh Bala Lau yace, wannan al’amari akwai damuwa kwarai cikinsa, Malami mahaddacin Al’qur’ani, masanin tafsiri, Wanda ya kare rayuwarsa wajen aiki da fadakarwa akan addinin Musulunci, shine wasu ‘yan Siyasa zasu masa irin wannan cin Mutunci tabbas an aikata laifi Babba.

Shehin Malamin yayi kira da babbar murya cewa jagoran kwankwasiyya Dr. Rabi’u Musa kwankwaso ya fito ya baiwa yan uwa musulmi da shi kansa Dr. Isa Ali Pantami Hakuri, sannan yaja kunnen yaransa, domin duk Wanda zai taba Malami ya saurari fushin Allah, Domin Annabi SAW Yace Malamai Magada Annabawa ne.

Sannan Annabi yace girmama malamai mahaddata alqurani na daga girmama Allah, sannan kuma hakan ya saba wa tsarin mulki kasa domin Malamin yana rike da mukami na babban dan majalisar zartaswa ta Nigeria waton (Minister) wadda haka na iya zama cin mutumci ga ita kanta gwamnati.

Dan haka Kada ku kuskura Malamai su zama abun cin mutuncin ku.

Muna jan hankalin masu irin wannan hali suji tsoron Allah su mutunta addini, zaman lafiya da kuma girmama Dokan kasa.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY