WA’AZIN IZALA A BIRNIN MAKKAH.

Zuwa yanzu Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta kasa ta tashi Haikan tana Gudanar da Wa’azuzzuka a Unguwannin Share’i Mansur da Share’i Sittin, Kungiyar tayi irin wadannan Wa’azozi a Muna da Filin Arfa wanda ansamu Nasarori ba dan kadan ba, hakanan gashi yanzu an kammala aiki kuma ana ta zagawa cikin unguwannin Hausawa ana karantar dasu Hakikanin Addini wanda Yayi karanci a Wannan Unguwanni.

Wanda Ya Jagoranci wannan tafiya shine Shugaban Kungiyar ta Kasa Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, tare da Rakiyar Magatakardan Kungiyar ta Kasa Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina (Daraktan Wa’azi na kasa), Sheikh Alhassan Sa’eed Adam Jos (Daraktan Makarantu na kasa), Sheikh Abubakar Giro Argungu (Daraktan Ayyuka na kasa) Eng. Mustapha Imam Sitti (Daraktan Majalisar Agaji ta Kasa), Sheikh Sani Ashir Kano, Sheikh Muhammad D. Adam Bajoga, Sheikh Mahmud Shira, Mallam Isah Aliyu Jen, Alaramma Abubakar Adam Katsina, Alaramma Ahmad Suleiman Kano, Alaramma Isma’el Maiduguri, Alaramma Anas Salisu Kura, Alaramma Attahiru Marnona, Alaramma Adam Mubi da dai sauran yan uwa yan Agaji da Sauran mutane.

Allah ya saka da alkhairi.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY