ISRAI DA MIRAJ

MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCI ALLAH YA TABBATA A GARE SHI.

An karbo daga Anas yace [RA] annabi [saw] yace mala’iku 3 sunzo sun same ni [alokacin ina kwance da dare] sai 1nsu yayi magana wa 1′ nan take saiya ya kamani ya tsaga qirjina ya ciro zuciya ta saiya dauko wani kasko sai ya wanke zuciyar tawa, sai ya mayar, nan take sai mala’ika jibrilu ya gabato mini da wata abun hawa [guraqa] batakai alfadari ba amma tafi jaki, nan take na hau.

sai muka tafi zuwa sama ta 1, sai jibrilu ya qwanqwasa akace wanene, yace jibrilu ne , aka ce tare da waye ? yace tare da Muhammad [saw] sai sukace dama angayyace shi ne? saiyace ei, nan take aka bude akace madalla da wanan baqo me girma kuma annabi me daraja, Annabi yace sai naga Annabi Adam [as] asama ta 1, sai jibrilu yace dani wannan shine Adam, ka masa sallama, sai na masa, sai yace madalla da Da me daraja, annabi me girma.

Nan take sai muka wuce sama ta 2 nanma aka tambaya mu kamar yadda akayi a sama ta 1 sai kuma ga annabi Isa da annabi Yahya, nanma jibrilu yace wannan Isa ne da yahya ka musu sallama nanma na musu sai sukace madalla da dan-uwa na kwarai annabi me daraja.

Sai muka wuce zuwa sama ta 3 nanma kwatankwacin abunda ya faru a sama 2 ya sake faruwa nan kuma saiga annabi yusuf [as] jibrilu yace wannan shine yusuf kaje ka masa sallama annabi yace saina masa, shima yace madalla da dan-uwa me girma annabi me daraja, annabi yace dana ganshi sai naga an bashi rabin kyau na duniya.

Sai muka wuce zuwa sama ta 4 nanma kwatankwacin abunda ya faru a sama 3 ya faru aka bude sai ga annabi Idris [as] nanma abunda ya faru acen ya sake faruwa.

Sai muka wuce zuwa sama ta 5 saiga annabi Haruna [as] nanma abunda ya faru ya sake faruwa.

Sai muka wuce zuwa sama ta 6, anan kuma sai mukaga annabi Musa, nanma abunda ya faru na gaisuwa ya faru annabi musa ma yace madallah da dan uwa na gari annabi me daraja, annabi yace muna wuce annabi musa sai ya fashe da kuka [akan tambayi annabi musa meya saka kuka ? sai yace yana takaicine annabi matashi yazo abayansa amma al-ummarsa zasu fi nawa yawa [cikin masu shiga aljanna]

Sai muka wuce sama ta 7 saiga annabi Ibrahim nanma abunda ya farui ya faru annabi Ibrahim yace madalla da Da na kwarai annabi na gari, annabi yace saiga annabi ibrahim yana jingine ajikin BAITUL-MA’AMUR [daki ne da yake a sama, kamar ka’abace ta mala’iku inda a kullum suna kai-komo, nanne annabi yace acikin hadisi ingantaccen, akullum mala’iku dubu 70 suna shiga cikin ta suyi ibada insun fita kuma wasune daban zasuzo ba wadancen ba]

Daga nan sai muka wuce zuwa SHAJRATUL-MUNTAHA [bishioyar magaryar qurewa]
annabi yace babu dan adam daya taba wuce wannan bishiya. hatta mala’iku in zasu karbi wahayi daga ubangiji iyakansu nan, nan suke zuwa su karbi wannan sako [wahayi] Da zaka tambayakace to daga wannan bishiya sai me ? sai ace dakai sai Gaibi !, Annabi yace naga ganyen wannan bishiya kai kace kunnuwan giwaye ne.
annabi [saw] yace acikin wani hadisi cewa ubangiji na daya gayyace ni zuwa wannan waje ya bani wasu abubuwa guda 3 wanda be taba baima wani annabi kafin ni ba, biyu daga ciki shine annabi yace ambani;
1-salloli 5 ankuma bani
2-ayoyi 2 nnan na karshen suratul-BaQara
Annabi yaci-gaba dacewa ananne ubangijina ya bani salloli guda 50 a dare da yini, na karbo wannan salloli na taho saida na cimma sama ta 6 inda na tadda annabi musa [AS] sai annabi musa ya tambayeni me aka baka/wajabtawa al-ummarka? sai nace anbani salloli 50 a ranah da yini.

Nan take musa yace dani maza ka koma ka roqi a sage maka don al-ummarka bazasu iya ba, don ni nasha fama da banu isra’ila.

Annabi yace take saina koma na koka wa ubangiji na akan a rage mini, nan take ubangiji ya rage 10.

Na sake zuwa har saida na cimma annabin Allah Musa ya sake tambaya ta, na bashi labarin ubangiji na ya rage 10, namma yace inkoma na sake komawa,
annabi yace saida mukayi haka har saida aka mayar da ita 5, nanma annabi musa yace inkoma arage, don shi an jarrabeshi da banu isra’ila, annabi yace ya musa na nemi ubangiji na ya rage ya rage har saida yanzu kunyar ubangiji na ya kama ni. [don haka ba matsala, zanje ahaka, don bazan iya komawa ba]

Annabi yace alokacin sai me shela yayi shela cewa wannan salloli 5 suna dauke da ladan 50 da aka fara farlantawa. Intahah.

Abu zarril-Gifari yace [a hadisin da imamu muslim ya rawaito] cewa na tambayi annabi [SAW] nace dashi Ya ma’aikin Allah shin kaga ubangijinka?
sai yace dani Haske ne ta yaya zan ganshi? [ma’ana haske ya shiga tsakanina na da shi, banganshi ba, Annabi haske ya gani, amma baiga Allah ba]

imamul-Bukhari da muslim sun rawaito hadisin nana Aisha.
Nana Aisha [ra] take cewa abubuwa guda 3 duk wanda ya baka labari game dasu to wannan yayi wa ubangiji karya;
1- duk wanda yace dakai annabi yaga Allah to wannan yayi wa Allah Qarya,
2- duk wanda yace dakai nnabi ya rage wani abu a addini to wannan yayi wa Allah Qarya
3- duk wanda yace dakai annabi yasan gaibi to wannan yayi wa Allah Qrya.
ta kuma kafa hujja da aya ta 103 suratul an’am [dangane da ganin Allah]
Ga kuma hadisin da yake cikin sahihul bukhari Annabi da kanshi yace wa sahabbai, ku saurara ku sani cikin babu me ganin ubangijinshi anan duniya,
Sheikhul islam yake cewa indai zakayi aikin nemo nassi da yake nuna annabi yaga Allah to bazaka taba samu ba, saidai ma kaga wanda yake nuna annabi be ganshi ba, misali wannan ayada take farkon suratul isra’i ta gwada wasu daga cikin ayoyin Allah aka nuna wa annabi ba Ubangijin da kanshi ba.

Sheikh-Ul islam yace ah! aida ubangijin aka gani da ayan ta nassanta karara
duba Mjmu’u Fatawa vol 6 pag 509
Dan Abbas yace Annabi yace yaga Allah, amma bece da idanunsa ba
sai malamai dukkansu sukayi ijma’i akan cewa to da zuciyarsa yake nufi.

Allah Shine Mafi Sani, Allah yayi Dadin Tsira ga Annabin mu Muhammadu da Alayensa da Sahabbansa da Aminci.

1 COMMENT

 1. Bismilla hirrah ma nirraheem
  Muna rokon allah da sunayensa kyawawa tsalkaka cikakku (99)
  Allah ka sanya albarka ga dukkan kafafen yada labarai na ahalis sunaah da tashoshin gidajen talavision na duniya na ahalis sunnah da malamammu da dalibammu da shuwagabanninmu da mabiyammu da iyayenmu da kakanninmu da ‘ya’yanmu da jikokinmu da manyanmu da kanananmu
  Allah
  Ka hada kan musulmi baki daya akan sunnah ka yafe kurakurammu ka shiryar damu akan hanya madaidaciya
  Allahumma Ameen

LEAVE A REPLY