IDAN JUNINKA ZALUNCI NE INA FIR’AUNA???

Allah ta’ala ya halicci bayi da falalarsa ya bayyana musu daidai daga kuskure, Annabi s.a.w yace ‘ babu wani mutum da Allah zai bashi wani Shugabanci, ya mutu ranar mutuwarsa alhali yayi algus cikin wannan jagoranci face Allah ya haramta aljannah a gareshi.

Alokacin da fir’auna da kasaitarsa da jin ya isa ya dinga azabtar da banu isra’il ya rika kashe mazansu yana barin mata, ya rika rarraba kawunansu zuwa ga kungiya kungiya, ya shimfida zalunci yadda yakeso, a lokaci daya Allah yai masa mummunan kamu, ”Allah taala yace ‘sai muka damqeshi da rundunarsa muka kuma watsasu cikin kogi, kayi dubi zuwaga yadda qarshen azzalumai ya kasance”. na da ikon yin zalunci amma ya haramtawa kansa ya kuma haramtashi ga bayi atsakaninsu domin samar musu da rayuwa mai nagarta. Zalunci tun daga ranar da aka fara yinsa baikai labari ba sai dai yakai me yinsa ga nadama.

Hakanan buktanassar a shekara ta 576 kafin miladiya daya samu iko akan yahudawa ya riqa gallaza musu azaba, daularsa bata wuce hamsin ba ta ruguje.

Haka mutanen makkah yayinda suka riqi siyasar zaluntar musulmai da azabtarsu basuyi qarko ba face an gama dasu an ruguje gumakansu a dan lokaci da bai wuce shekaru takwas ba.

A lokacin da hajjaj bn yusuf yadau salon gallazawa Mutane da kashesu babu gaira babu dalili. kowa yasan yadda qarshensa ya kasance.

Da wannan nake jan hankalin shuwagabanni idan har suna gani cewa
zaluntar talakawa da kashesu shine siyasar da zata tabbatar musu da mulkinsu to sun yi kuskure don kuwa zalunci baya qarko!!!

Shuwagabanni kuji tsoron Allah kuyi adalci ga talakawanku.

Mu kuma talakawa mu sani cewa tafarkin manzo s.a.w shine haquri akan zaluncin shuwagabanni da kuma yi musu adduar Allah ya shiryesu, ba wai Allah ya tsine musu ba, domin idan mun tsine musu, wahar kanmu zata sake dawowa kuma da muni, haramunne daukan makami domin yakarsu ko tsine musu akan Mimbari.

Kuma dukkan wadannan fitintinu da suke faruwa muma sai mun yiwa kanmu garan bawul, mun chanja sannan Allah ya amshi addu’ar mu.

Domin Allah ta’ala yana cewa;

1. “Kuma duk abin da ya same ku na wata masifa, to, game da abin da
hannayen ku suka aikata ne, kuma (Allah) yana yafewar (wadansu
laifukan) masu yawa”. SHURA:30.

2. “Barna ta bayyana a cikin kasa da teku (wato ko’ina), saboda
abin da hannayen mutane suka aikata. Domin Allah ya dandana musu
sashin abin da suka aikata, tsammanin su za su komo (kan hanya).”
Rum:41

3. Kuma da yawa daga cikin al karya akwai wadda tayi tsaurin kai daga
barin umurnin ubangijinta da manzanninsa, sai mu ka yi mata hisabi
(sakamako), hisabi mai tsanani, kuma muka azabtar da ita, azaba abar
kyama”. Dalak:8.

4. “…lallai ne, Allah ba ya canza abinda yake akan Mutane har sai
sun canza abin da yake a rayukan su. kuma idan Allah yayi nufin wata
azaba ga mutane, to, babu mai iya mayar da ita, kuma ba su da wani
majibinci baicin shi (Allah)”. Ra’ad:11.

5. “Kuma wadanda suka kafirta, sashen su majibintan sashe ne, idan ba
ku aikata haka ba (ku musulmi), wata fitina za ta kasance a cikin
kasa, da fasadi babba”. Anfal:73

Daga Qarshe muna addu’a Allah ya dawo da ‘ya’yan mu da wasu suka gudu da su a garin Cibok ta jihar Borno. wayanda suka rasa rayukansu kuma Muna addu’an Allah ya jikansu da raham.

Sannan muna musu bishara da Cewa “Allah taala yace ‘ lalle tare da tsanani akwai.sauki’ sayyiduna umar yace tsanani bai taba rinjayar sauki biyu ba’. Allah ta’ala yace ‘ kasa ta Allah ce yana gadar da ita ga wanda yaso’ yace ‘ mun ributa a cikin Zabuura bayan ambato cewa lalle kasa bayina salihai su zasu gajeta’ Annabi s.aw yace ‘ kuyi hakuri har sai kun iskeni a bakin tabki’ Lalle Allah yana tare da masu hakuri, kuma baya tauye ladan masu hakuri. Allah ya bamu hakuri

Ya Allah mun tuba, ka yafe muna, ka bamu ikon daukar matakin da ya
dace. kuma ya Allah ka kawo muna saukin wadannan musibu, idan kuma Mutuwa tazo muna addu’an Allah yasa mu cika da imani. Amin.

6 COMMENTS

LEAVE A REPLY