IZALA TA JAJANTAWA WADANDA HARIN BOM YA RUTSA DA SU.

ƘUNGIYAR IZALA TA ƘASA TA KAI ZIYARA BABBAN ASIBITIN GWAMNATIN TARAYYA DAKE BIRNIN ABUJA DAN GAIDA WAƊANDA HARIN BOM YA RITSA DA SU A GARIN NYANYA DA YA GABATA.

Shugaban Kungiyar na Ƙasa Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau Shine Wanda ya jagoranci tawagar da ta kai ziyarar gani da ido a asibitin dan jajantawa Majinyatan, a lokacin da yake ganawa dasu, Cikin Su akwai Musulmi da waɗanda ba musulmi ba, yace musu musulunci ba addinin tashin hankali bane, kuma ba addinin ta’addanci bane, addinin Zaman Lafiya ne, yace Annabi Muhammadu Tsira da aminci su tabbata a gare shi ya zauna da waɗanda ba musulmi ba, kuma sunyi kyakkyawar Mu’amala, wanda saboda daɗin zama da shi da Waɗanda ba Musulmi ba sukayi yasa har wasu sun shiga musulunci a dalilin wannan, dan haka muna tayaku addu’an Allah ya baku lafiya, ya kuma kiyaye gaba “Inji shugaban”.

A nasa bayanin, Shugaban Asibitin yayi matuƙar nuna farin cikin sa da wannan ziyara da shine na farko a wurin su, wanda ƙungiya ta addini ta kawo musu ziyara, Yace baza su taɓa mantawa da rana irin wannan ba, anzo an duba marassa lafiya, anyi musu wa’azi, kuma gashi an tallafawa majinyata da kudi ko wannen su dan su samu sauƙin gudanar da jinyar da suke fama da shi, sannan yayi addu’an Allah ya sakawa Shugaba Bala Lau da alkhairi, ya kuma ƙara dankon Zumunci tsakanin juna.

Cikin Tawagar da suka raka shugaba Sun haɗa da Sheikh Dr. Alhassan Sa’id Adam Jos, Sheikh Habibu Yahaya Ƙaura, Malam Mukhtari Bom (National Admin Secretary) Alaramma Ahmad Suleiman, Alaramma Isma’il Maiduguri, Shugaban ƴan agaji na FCT Abuja, Da Sauran Shugabanni/Malamai da ƴan agaji na FCT.

Muna Addu’an Allah ya basu lafiya, ya kiyaye Dukkan wata Musiba anan gaba, Allah ya sakawa Shugaba da sauran ƴan Majalisar sa bisa damuwa da suke da damuwar al’umma. Amin.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY