MAI ALFARMA SARKIN MUSULMI YACE BA’A GA JINJIRIN WATA A YAU LITININ BA.

Mai Alfarma Sarkin Musulm ya bada sanarwa a NTA ta hannun sakataren sa Prop. Ishaq Olade cewa ba aga jinjirin watan ramadhan ba a saboda haka sai ranar Laraba, ne za ata shi da Azumi. Yan uwa Musulmi ya na da kyau mu yi aikin da wannan sanarwa kar mu yadda rudin da masu mummunar Akidar zagin sahabbai na cewa gobe ne daya ga watan Ramadhan.

1. A mazhabar Hanafiyyah Ibnu Aabidin ya ce cikin Haashiyatu Raddil Muhtar 2/388: ((Ingantacciyar magana ita ce: Harkar tabbatar jinjirin wata abu ne da ake jingina shi zuwa ga Sarkin Musulmi, duk lokacin da ganin wata ya inganta a wurinsa, kuma shaidu suka yawaita to sai ya yi umurni da a yi azumi)). Intaha.
2. A mazhabar Malikiyyah Ibnu Rushd ya ce cikin Al-Muqaddimaatul Mumahhidat 1/251: ((Idan ganin jinjirin wata ya tabbata a wurin Sarkin Musulmi da shaidar adilai biyu to sai ya umurci mutane da yin azumi, da kuma yin idin azumi, kuma ya tilasta wa mutane yin hakan)). Intaha.
3. A mazhabar Hanbaliyyah, ya zo cikin littafin Masaa’ilu Imam Ahmad Bi Riwayati Abdillah 2/610-611: ((Na tambayi babana game da ganin jinjirin wata idan mutum daya ya ba da shaidar ganinsa? Sai ya ce: Sarkin Musulmi sai ya umurci mutane da yin azumi)). Intaha.
***********************************
FATAWAR MALUMAN DA’AWAH:
Sheik Bin Baz ya ce cikin Majmuu’ul Fataawa 15/97: ((Amma su daidaikun mutane Musulmi wajibi ne a kansu su yi azumi ko su sha ruwa a lokacin da shugabanninsu suka ce a yi haka, saboda Hadithin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah: “Azumi shi ne ranar da kuke azumi, Idin karamar salla ranar da kuke Idin karamar salla, Idin Layya ranar da kuke Idin Layya”)). Intaha.
*********************************
Muna fata ‘yan’uwa Musulmi za su daure su rika gina addininsu a kan abin da ya tabbata cikin Shari’ar Musulunci, ba wai a kan ta’assubanci, da son zuciya, da jahilci ba. Muna kuma rokon Allah da Ya nuna mana Ramadan lafiya Ya kuma ba mu ladan da ke cikinsa, Ya kuma tabbatar da dugaduganmu a kan sunnar Annabi cikin dukkan aqiidarmu, da dukkan ibadarmu, da dukkan mu’amalarmu. Ameen.

Allah yasa Mu Dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *