MUSULMI ‘DAN UWAN MUSULMI NE.

Manzon Allah saw yace: “MUSULMI dan uwan musulmi ne.Kada ya ha’inceshi kar ya Qaryata shi, kar ya tozarta shi..

Dukkan Musulmi akan Musulmi,Haramun ne (yaci) mutuncinsa,ko ya ta’ba dukiyarsa,ko ya zubar da Jininsa..

Tsoron Allah ANAN YAKE! (YA NUNA QIRJINSA).
Ya ishe Mutum sharri akan kansa, ache gashi ya wulakanta ‘dan uwansa Musulmi”

(Wannan hadisi ne ingantacce. Tirmiziy ya ruwaito shi akan lamba ta 1927)

Da ache dukkan Al’ummar musulmi zamu hadu mu jajirce akan aiki da wannan hadisin ma kadai acikin mu’amalolinmu na yau da kullum, acikin gidajenmu da unguwanninmu da garuruwanmu, da Ma’aikatunmu da Makarantunmu da kasuwanninmu,da bamu samu kanmu acikin rigingimun nan ba.

Allah ya bamu ikon gyarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *