SON ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM SHINE KOYI DA SHI.

Ya dan uwa ka sani son manzon Allah da son abin da yazo da shi wajibi ne, duk wanda ya kyamaci wani abu da Annabi yazo da shi, to ya kafirta koda yayi aiki da shi. Kuma soyayya kadai bata wadatarwa, dole ne sai ya zamo anfi sonsa fiye da komai, hatta ranka, dama kuma duk wanda yake son abu zai fifita shi kuma zai zabi ya dace da shi.

Mai gaskiya cikin son Annabi shine wanda alamomin hakan zasu bayyana a gare shi ta hanyar biyayya da kwaikwayo da bin umurnin sa da kuma nisantar abin da ya hana, da kuma ladabtuwa da ladubbansa cikin jin dadi da kunci. Domin biyayya da da’a sune soyayya yake haifarwa, kuma ba tare da su ba soyayya bata gaskatuwa.

Kuma son Annabi tsira mai da aminci yana da alamomi da yawa, daga ciki akwai:
-yawan yi masa salati.
-yawan anbatonsa.
-Shaukin (Bege) saduwa da shi.
-Girmama shi da mutunta shi yayin da aka ambace shi.
Sahabban manzon Allah Mai tsira da aminci sun kasance duk sa’adda aka ambaci Annabi sai kaga sun nutsu jikin su ya nuna alama.
Daga cikin alamun akwai kin duk wanda yake kin Annabi SAW, da kuma gaba da duk wanda yake gaba da shi, da nisantar duk wanda ya sabawa sunnarsa ko kuma ya kago wani abu a cikin addini wanda ba shi a cikin addini. Sawa’un cikin yan bidi’ah ko munafukai.

Daga ciki akwai son duk wanda Annabi SAW yake so, kamar iyalan gidansa da matayensa (Ahlul baiti) da sahabbansa na makkah dana Madina (Muhajirun da Ansar) da kuma kin duk wanda yake kinsu. Ko yake gaba da su, da kuma kin mai kinsu.

Daga ciki akwai koyi da halayensa kyawawa, dama kuma shine yafi kowa kyawun halaye, kuma yafi kyauta, musamman ma idan watan ramalana ya kama. Kamar yadda Nana Aisha tace: “Halayensa gaba dayansu Al’Qur’ani ne” ma’ana ya lizamci aikata duk abin da Al’aqur’ani yayi umurni da shi.

SIFOFIN MANZON ALLAH TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI.

Manzon Allah SAW ya kasance yafi kowa jarumta musamman ma idan an fita filin daga. Yafi kowa karamci, kyauta tasa tafi yawa a ramalana, yafi kowa nasiha, yafi kowa hakuri, baya rama abin da akayi masa, amma idan an sabawa Allah to anan yafi kowa zafi, yafi kowa tawali’u, yafi kowa nutsuwa, yafi kowa kunya, kuma yafi kowa kyautatawa iyalansa, yafi kowa jinkai da tausayi. Da sauran su.

Allah ya bamu ikon koyi da shi ta hanyar da ta dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *